Gwamnatin Tarayya Za Ta Bada Tallafin Naira 75, 000 Ga Marasa Kafi A Jigawa
Published: 8th, February 2025 GMT
Shirin Inganta rayuwar al’umma na jihar Jigawa ya raba katinan cire kudi na ATM a kananan hukumomi 10 daga cikin 27 domin al’umma su sami tallafin naira dubu saba’in da biyar biyar na gwamnatin Tarayya.
Shugaban shirin na jihar, Malam Mustapha Umar Babura ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.
Yayi bayanin cewar, ana rabon katinan karbar kudin ne ga wadanda za su sami tallafin inganta rayuwa na naira dubu sabain da biyar.
A cewarsa, duk da korafe korafen da ake samu wajen rabon katinan, aikin na cigaba da gudana yadda ya kamata.
Mustapha Umar Babura ya ce ana ta kokarin warware duk matsalolin da ma’aikatan suke cin karo da su wajen rabon katinan ga al’umma.
Yana mai cewar, a zancen ma da ake yi yanzu, ana nan ana tsare-tsare na sake dawo da shirin ciyar da dalibai a makarantu.
Babura, ya ce duk mai korafi zai iya gabatar da shi ga jami’an shirin da ake da su a kananan hukumomin jihar 27 domin inganta ayyukan shirin.
Shugaban shirin inganta rayuwar al’umma na jihar Jigawa ya kara da cewar an bullo da shirin ne domin inganta rayuwar masu karamin karfi a jihar.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na zamani na kimanin Naira Miliyan 250 ga cibiyoyin horas da sana’o’in hannu biyu da ke Kofar Mata da Gwale, domin yaƙi da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a tsakanin matasa, ta hanyar samar da aikin yi.
Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofarmata, ya ce an amince da tallafin ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf don bunƙasa tsare-tsaren ƙarfafa matasa a jihar.
Ya bayyana cewa an samar da injinan sarrafa fata guda 26 domin cibiyoyin wadanda al’ummar yankunan suka kafa, amma ba su da isassun kayayyakin aiki.
Ya ce Gwamna Yusuf ne ya gina Cibiyar Horaswar ta Gwale kasancewar nan ce mazabarsa, yayin da Dakta Yakubu Adam ya taka rawa wajen gina ta Kofar-Mata.
Ya ce cibiyoyin za su samar da daruruwan ayyukan yi tare da rage matsalolin zaman kashe-wando da ta’addanci a tsakanin matasa.
A nasa jawabin, Ali Musa Kofar-Mata na ƙungiyar IKMA ya gode wa gwamnati bisa wannan gudummawar da ya kira mai sauya rayuwa.
Ya ce cibiyar ta fara ɗaukar matasa maza da mata, kuma horon zai ɗauki watanni uku kafin a shiga sabon zagaye.
Abdullahi Jalaluddeen