Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ’yan jarida su daina kawo rahoton ayyukan ’yan ta’adda
Published: 17th, April 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta nemi kafafen watsa labarai da su daina kawo rahoton ayyukan ‘yan ta’addan da ke tada hankali a jihohin Filato, Borno, Zamfara, Binuwai, da sauransu.
Aminiya ta rawaito cewa jihohin na fama da tashe-tashen hankula musamman a baya-bayan nan in da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan ya sanya wasu ‘yan Nijeriyar da suka haɗa da sarakuna, ‘yan siyasa, ƙungiyoyin cikin gida da na waje tuhumar gwamnati kan aikinta na kare ‘yan ƙasa.
Sai dai gwamnatin ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Mohammed Idris, ta ce yaɗa labaran ayyukan ’yan ta’addan da ’yan jarida ke yi ne ke ƙara kawo barazana ga tsaron ƙasar.
Ministan ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar soji da ke Abuja a yayin a wani taron masu ruwa da tsaki a harkokin kafafen yaɗa labarai.
Ministan wanda babban daraktan kafar Muryar Nijeriya, Jibril Ndace ya wakilta, ya ce gwamnatinsu na ƙoƙari wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, ta hanyar samar wa jami’an tsaro kayan aiki, horo, da tattara bayanan sirri.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Ministan Yada Labarai Tsaro Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci: Nan Ba Da Jimawa Ba, ‘Yan Ta’adda Za Su Ɗanɗana Kuɗarsu – COAS
Ya kara da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin Nijeriya suna aiki tukuru domin ganin an ga sauye-sauye a yaki da ta’addanci da ake yi, a fili kuma a bayyane.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp