Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin
Published: 16th, April 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 18, da kuma Litinin, 21 ga watan Afrilun 2025 a matsayin ranakun hutun bikin Easter a faɗin ƙasar.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan RiƙoA jawabin da Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida , Dokta Magdalene Ajani ta fitar, Ministan ya nemi mabiya addinin Kirista su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasar addu’o’in zaman lafiya da haɗin kai.
Yayin da yake taya mabiya addinin Kirista murnar wannan lokaci, Mista Tunji yana kuma kira ga al’ummar Nijeriya da su haɗa hannu da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a ƙoƙarin da take yi na inganta rayuwar al’umma ta hanyar ci gaban ƙasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine
Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine.
Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu.
A ranakun da za a tsagaita wutar ne Rasha ke bikin karshen da yakinta da kasar Jamus a shekarun 1941 zuwa 1945, wanda aka fi sani da Yakin Duniya na Biyu a yawancin duniya.
A Rasha ana kiran yakin na Duniya na biyu da sunan Babban Yaƙin Ceton Kasa.
Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji laifi ne — Janar Chibuisi