’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya
Published: 15th, April 2025 GMT
’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi.
Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya.
Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje.
Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin a fito da ita, shi ya sa ingancin ya samu matsala.
Duk da samun koma baya: Najeriya ce kasa mafi arzikin danyen mai a Afirka —OPEC Matashi ya yi yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a KanoDon haka ya shawarci masu saya da su shanya ta a rana kuma su wanke ta sosai sa’annan su dan turara ta domin dawo da ingancinta.
A gefe guda kuma wadanda da suka amfana da wani rukuni na daban na shinkafar gwamnatin sun yaba da ingancinta ta fuskar dandano da kuma yanayi.
Kawo yanzu dai hukumomi ba su ce uffan game da korafin da jama’a ke yi kan wannan lamari ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati
এছাড়াও পড়ুন:
ASUU Ta Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Albashin Watan Yuni
Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta.
ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya.
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun.
Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba.
“Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen mutanen da ke da alhakin sakin kuɗin ne,” in ji Piwuna.
Ya ƙara da cewa sauyi tsarin biyan albashi daga IPPIS zuwa GIFMIS ya ƙara jefa malamai cikin wahala.
ASUU ta ce duk wata Jami’a da ba a biya malamanta albashin Yuni kafin 7 ga Yuli ba, to, ya kamata su fara yajin aiki nan take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp