Haɗarin tirela ya yi sanadin asarar awaki sama da 100 a Zariya
Published: 1st, August 2025 GMT
A daren Juma’a ne dab da wayewar gari wata motar tirela ɗauke da awaki da kaji wadda ta taso daga Gwauron Dutse a Jihar Kano ta yi haɗari.
Motar tirelar wadda take ɗauke da dakon awaki da kuma kwandunan kaji mai yawa a samanta baya ga mutane da ta ɗauko ta yi haɗarin a kusa da kasuwar Ɗan Magaji saman gadar da ke kan hanyar Zariya zuwa Kaduna.
Awaki kusan sama da 100 suka mutu da kuma kaji kusan ɗari 500 ne aka ƙeyasta sun mutu.
Sai dai ba a sami asarar rai ko ɗaya ba, sai dai akasarin mutanen da suke motar sun sami raunuka cikinsu har da direban motar, kuma an garzaya da su zuwa Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya don samun kulawar likitoci.
Wasu daga cikin matasan da suka kai ɗauki wurin sun kwashe matattun awakin da kajin inda suka watsa cikin wani kududdufi da ake kiwon kifi a kusa da inda motar ta yi hatsarin dan gudun kada wasu bɓata gari su kwashe dan sayarwa al’umma da mushen matattaun dabbobin.
Wani ganau da ke zaune a wurin da hatsarin ya faru ya ce yana zaton kamar barci ne ya kama direban motar.
A cewar ganau ɗin an tafka asarar sosai na dukiya a hatsarin motar sai dai shugabannin mazauna wurin sun sa ido domin ganin cewa ba a kwashi matattaun dabbobin ayi wani wuri da su ba.
An yi ƙokarin tuntuɓar mai magana da yawu hukumar kula da haɗɗura ta ƙasa reshen Zariya tare da tura masa saƙon kar ta kwana domin jin dalilin faruwar lamarin, amma har zuwa lokacin haɗa rahoton bai ɗauki waya ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hatsarin tirela Zaria
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp