Leadership News Hausa:
2025-11-18@14:04:51 GMT

Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano

Published: 3rd, October 2025 GMT

Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano

Wasan Kalankuwa A Nijeriya, 1977

A gwamnatance a wannan kasa, an fara shirya manyan bukukuwan nuna fasahohinmu da aladunmu na-dauri, cikin Shekarar 1977 a Legas. Wanda aka fara gudanar da taron, daga 15 ga Watan Janairu, zuwa 12 ga Watan Farairun Shekarar 1977. A farkon lamari, an niyyaci ci gaba da shirya bikin na baje-kolin al’ada ne a duk Shekara, da niyyar samar da hadin-kai a tsakanin jama’ar Kasa bakidaya.

Da farko an kira bikin ne da FESTAC ’77, daga baya aka koma kiransa da NAFEST (National Festibal of Arts and Culture).

Saboda muhimmancin irin wadannan bukukuwa, lokacin da aka fara shirya shi a wannan kasa, an sami mahalarta taron ne daga mabanbantan kasashe har kimanin hamsin da biyar (55). Ba ya ga yunkurin samun hadin-kai a tsakanin al’umar wannan kasa, an kara fadada kudirin taron har zuwa ga daukacin sassan duniya. Inda aka nuna cewa, duk wani mutum bakar-fata dake zaune a wannan nahiya tamu ta Afurka, da sauran kasashen Duniya, shi ma wannan taron nuna fasahohin mutane bakaen fata da al’adunsu nasa ne, a matsayinsa na guda daga jinsin bakar fata. Irin wannan wasan Kalankuwa na farko, zai iya tunawa mutumin wannan kasa, yawan kiraye-kirayen da marigayi Dr Yusuf Maitama Sule Danmasanin Kano ke yi cewa, lokaci ya yi da ya dace jama’ar Afurka su tashi su lalubo irin tsarin Dimukradiyyar da ta dace da mutanensu bakaken-fata, tare da rabuwa da irin dimukradiyyar kasashen Turai da Amurka.

 

Makasudin Shirya Wannan Biki A Kano, KANFEST, 2025

Da mutum zai tsaya ya dubi irin dalilan da masu shirya wannan taro a Kano suka gabatar, lalle zai kai ga fahimtar yiwuwar ciyar da al’uma gaba, da yunkurin raya al’ada ke samarwa. Daga bayanan da ke fitowa daga waccan ma’aikata mai jibi da tarihi da al’adu ta Kano, “History and Culture Bureau”, sun fadi cewa, wannan biki da a turance aka kira shi da “First Kano Festibal of Arts and Culture (KANFEST, 2025), an shirya shi ne bisa wasu manyan makasudai da kuma wasu manufofi da ake son cimmawa. Da farko, wannan hukuma, ta ayyana cewa, ta shirya wannan babban biki ne, don nuna kyawawan al’adu hada da fasahohin da Bahaushen Kano ke da shi, ko a ce ya gada kaka da kakanni. Kuma za a nunawa daukacin al’umar Duniya wannan biki, babu ragin-daka.

Bugu da kari, akwai wasu wasannin nishadi iri daban-daban masu kayatarwa da za a nuna su ga mahalarta taron, da ma waninsu. Wasannin Bahaushe, irin su wasannin Wanzamai, wasan wuta na Makera, wasan shan kankana na Manoma. Sannan, akwai baje-kolin basira daga gwanayen mabanbantan masu sana’o’in Malam Bahaushe, wadanda suma za su zalakarsu a ranakun bikin a Kano. Sana’o’in Majema, Masaka, Marina, Dukawa, da ma tsagin wasanni masu kayatarwa, suma za a nuna su ga mahalarta taron. Wasan “Yan-baka, wasan langa, wasan bago, “yar-carafke, gada, lugude, tafa-tafa, “yar gala-gala, kokawa, dambe, Malam na bakin kogi…da sauransu, duka za a nuna su daya bayan daya.

Tamkar irin yadda aka fara shirya wannan taro a matakin kasa bakidaya a Shekarar 1977, ita ma wannan hukuma da ta shirya taron a Kano, na da kudirin ci gaba da shirya bikin a duk Shekara, tamkar irin yadda manyan kasashen Duniya da suka ci gaba a yau suke shiryawa. Ba ya ga wasannin kwaikwayo na nishadi da ilmantarwa da za a nuna a ranakun bikin, suma kananan yara ba a bar su a baya ba, suma za su zo, tare da baje-kolin irin baiwar da Allah Yai musu. Jama’ar kowace karamar hukuma a Kano, za su halarci wannan biki da ake kokarin gudanarwa. Sannan, kowane 6angare na kananan hukumomin, za su zo tare da nuna irin baiwa, hazaka da fasahohin da suka yi shuhura akai, a ranakun bikin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: shirya wannan wannan kasa wannan biki

এছাড়াও পড়ুন:

A Zamanantar Da Tsarin Karatu A Makarantun Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci – ECOWAS

“A shekaru goma da suka gabata, ayyukan ta`addanci da tashe-tashen hankula daga masu tsattsauran ra`ayi ya haifar da mummunan koma bayan tattalin arziki da na zamantakewar alummomin dake shiyyar, halin da daliban irin wadannan makarantu suke ciki yana bukatar kulawar gaggawa daga kungiyar ta ECOWAS, abin takaici irin wadannan makarantun allo suna daukar dalibai masu yawan gaske kuma akasari kananan yara daga shiyyar, to amma kuma ba a bai wa makarantun da daliban kulawar da ta kamata, wannan ta sanya kungiyoyin `yan ta`adda ke samun kofar kusantar su domin kwadaita musu shiga cikin kungiyoyin.”

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe November 16, 2025 Labarai NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji November 16, 2025 Nazari Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna? November 16, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing
  • NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar
  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  • Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
  • An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing
  • Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30
  • A Zamanantar Da Tsarin Karatu A Makarantun Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci – ECOWAS
  • An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka
  • Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso
  • Sanusi ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso