‘Yansandan Jihar Filato Zasu Koya Darasi Ga Masu Daukar Hukunci Ba Tare Da Bincike Ba
Published: 3rd, October 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Filato, ta sha alwashin ba da misali da masu yanke hukunci da kansu ba tare da barin doka ta yi aikin ta ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, CP Emmanuel Adesina ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Jos yayin da suka kama wasu manyan mutane tara (9) da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane da wasu laifuka daban-daban.
Ku tuna cewa a wasu lokutan a cikin watan Agustan wannan shekara ta 2025, an kashe jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a karamar hukumar Bassa sakamakon aikata irin wannan danyen aiki.
An bayyana cewa dan sandan ya tafi bakin aiki ne, inda ya zakulo wanda ake zargi da gudu sannan ya kama mai laifin, sai ya fara ihun barawo…. barawo….sai ga jama’a sun kashe jami’in har lahira ba tare da basu damar bayyana kansa ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato, CP, wadda ya yi kakkausar suka ga irin wannan aikin, ya ce sun kama mutane da dama da ake zargi da aikata laifin.
Ya kuma bayyana dalilin da ya sa aka kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a wurare daban-daban a fadin jihar.
Ya kuma bukaci ‘yan jihar Filato da su kasance masu taka-tsan-tsan tare da baiwa jami’an tsaro sahihin bayanai masu inganci da za su bankado masu mugun nufi da jihar Filato da Najeriya baki daya.
DORCAS GWANI JOS.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: da ake zargi da jihar Filato
এছাড়াও পড়ুন:
PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu
Jam’iyyar PDP ta kori Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose da tsohon sakataren jam’iyyar na ƙasa, Samuel Anyanwu.
PDP ta yanke wannan hukunci ne a babban taron jam’iyyar da ake gudanarwa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Gwamnati, UNICEF da ’yan jarida sun haɗa don yaƙar cututtukan da aka manta da su a Gombe Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — KwankwasoTsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na yankin Kudu, Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, sannan Samaila Burga, shugaban PDP na Jihar Bauchi, ya mara masa baya.
A baya, tsagin jam’iyyar da ke goyon bayan Wike sun kai ƙara kotu don a hana gudanar da taron.
Amma PDP ta samu hukuncin da ya ba ta damar ci gaba da taron daga Kotun Ƙoli ta Jihar Oyo.
Kwana biyu kafin taron, Mao Ohuabunwa, Shugaban Majalisar Amintattu (BoT) na ɓangaren Wike, ya ce duk wanda ya tafi Ibadan don taron hutu ya je yi, domin doka ba za ta aminta da shi ba.
A cewarsa, Anyanwu ya riga ya fitar da sanarwar ɗage taron.
Ohuabunwa ya ce: “Mun zauna a matsayin kwamitin zartarwa na ƙasa na PDP, muka duba abubuwan da muka yi. Mun yadda da bin hukuncin kotu game da taron Ibadan. Don haka ba mu da hannu a taron.
“Ibadan wurin jama’a ne, mutane na iya zuwa don kowane abu amma ba don babban taro ba. Duk wanda ya tafi can da sunan taro ya ɗauki hakan a matsayin shaƙatawa kawai.
“Ba za mu amince da take haƙƙin kundin tsarin mulki da wasu mutanen ke yi da sunan babban taro ba.”
Muƙaddashin shugaban tsagin, Abdulrahman Muhammad, shi ma ya kira wakilansu da su guji zuwa taron.
Ya ce tsagin nasu zai ci gaba da haɗa kan mambobi a jihohi 36 da Abuja domin ƙarfafa jam’iyyar.
Muhammad ya ce: “Muna kiran dukkanin wakilai su guji zuwa taron Ibadan.”
A nasa jawabin, Wike ya gode wa mambobin jam’iyyar saboda yadda suke tsayawa wajen kare jam’iyyar a yankunansu.
Ya ce su a ɓangarensu za su ci gaba da bin doka kuma ba za su bari a tsoratar da su ba.
Wike, ya kuma ce ba zai taɓa yaudarar waɗanda ke goyon bayan kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.
Ya ce: “Ina farin ciki da yadda kuke nuna damuwa game da jam’iyyar a yankunanku. Zan ci gaba da goyon bayanku, ba zan yaudare ku ba.”