Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, ya kaddamar da wasu sabbin motocin alfarma masu kujeru 18 guda 50, domin inganta ayyukan zirga-zirgar jama’a na jihar.

 

Da yake jawabi a wajen kaddamar da bikin a Gusau, babban birnin jihar, Gwamna Lawal ya bayyana ci gaban a matsayin wani sabon babi a tarihin sufuri na Zamfara.

 

 

A cewar Gwamnan, motocin bas din suna da kayan kariya na zamani da na jin dadi, wadanda suka hada da na’urorin sanyaya waje da sauran kayyakin jin dadin matafiya.

 

Dokta Lawal ya bayyana cewa, da gangan aka samu jinkirin tura motocin bas din bayan isowarsu, inda ya ce gwamnati ta fara samar da tsare-tsare na sa ido da kuma bin diddigi don tabbatar da dorewar da kuma hana almundahana da ke dabaibaye ayyukan da aka yi a baya.

 

Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa, ma’aikatan kamfanin sufurin jihar da suka hada da direbobi, kanikanci, jami’an bayar da tikiti, da ma’aikatan gudanarwa sun sami horo mai zurfi da ya shafi fasaha, da’a, da hidimar kwastomomi.

Tun da farko, Shugaban Kwamitin cika shekaru biyu na Gwamna kuma Shugaban Ma’aikata, Mukhtar Luggaga, ya sanar da cewa, motocin bas din za su fara aiki gadan-gadan.

 

Lugga ya bayyana ci gaban a matsayin rabon dimokuradiyya ga al’ummar Zamfara.

 

A nasa bangaren, Manajan daraktan hukumar sufurin na jihar Zamfara, Ukashatu Abdullahi, ya yabawa gwamna Lawal bisa jajircewarsa na inganta harkar sufuri ta hanyar samar da motocin bas na zamani.

 

Bikin kaddamarwar ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a harkar sufuri, shugabannin gargajiya, jami’an gwamnati, da sauran manyan baki.

 

 

 

COV/AMINU DALHATU.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu

Iyayen ɗalibai ’yan mata 25 ’yan bindiga sace ɗakunan kwanansu a Jihar Kebbi sun bayyana irin tashin hankali da suka shiga bayan abin da ya faru.

“Ita kaɗai gare ni,” in ji Malam Muhammad Maga, mahaifin Nafisa, wadda ita kadai ya haifa, kuma take cikin ɗaliban da ’yan bindiga suka sace a makarantar.

Malam Muhammad wanda idanunsa ke cike da ƙwalla ya ce, “Roƙona Allah Ya sa a dawo min da ita lafiya, ita kaɗai gare ni. Ina roƙon Gwamna Idris ya taimaka a dawo mana da su.  Mun san ƙoƙarin da yake yi a fannin tsaro a tsawon shekara biyu da ya yi a kan mulki.”

Shi ma Malam Aliyu Yakubu, ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban da aka sace, ya ce, “’Yata na cikin ɗaliban da aka sace daga ɗakin kwanansu a safiyar Litinin, gaskiya ni da sauran iyaye muna cikin tashin hankali.

Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno

“Babban abin da nake tsoro shi ne kada abin ya zama irin na Makarantar ’Yan Mata ta Gwamantin Tarayya ta Birnin Yauri, inda yaran da aka sace suka shafe sama da shekara biyu a hannun ’yan bindiga

Muna rokon Gwamnatin Jihar Kebbi da Gwamnatin Tarayya su yi duk mai yiwuwa su ceto mana ’ya’yan mu”

Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar Litinin ne ’yan bindiga suka yi ta harbe-harbe a iska sa’annan suka kutsa cikin Makarantar sakandaren ’Yan Matan Gwamnati ta Musamman (GGCSS) da ke garin Maga a Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, suka yi abin gaba da ɗalibai 25.

’Yan bindigar sun ci karensu babu babbaka, ba tare da wani ƙalubale ba, in banda Mataimakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin hana su tafiya da ɗaliban, amma suka harba shi har lahira, suka yi abin gaba da yaran.

Makarantar GGCSS Maga ta kasance a rufe na kimanin shekaru biyar saboda tsaron irin garin GGSS Birnin Tauri a zamanin gwamnatin da ta gabata ta Abubakar Atiku Bagusu, sai ’yan shekarun baya aka buɗe ta, inda aka girke jami’an tsaro.

Wani mahaifi da ’yarsa A’isha take cikin ɗaliban da aka sace, ya ce, wani mazaunin garin ne ya fara sanar da shi cewa A’isha tana cikin yaran da aka sace,  “Amma ban gaskata ba, sai da na zo makarantar na iske iyaye na ta koke-koke. Roƙona ga gwamnati shi ne ta taimaka ta ceto maka ’ya’yanmu.”

Kawai Altine, wanda shi ma ’yan bindiga sun sace ’yarsam ya ce, “Na miƙa komai ga Allah, kuma na yi imanin cewa Allah Zai dawo mana da ita nan ba da jimawa ba. Roƙona kawo shi ne gwamnati da jami’an tsaro kada su yi ƙasa a gwiwa, wajen bi sawu domin gano yaran namu.”

Wani shugaban al’umma a yankin, Malam Rabi’u Abubakar, ya ce harin ya girgiz al’ummar yankin, musamman iyayen ɗalibai.

Ya ce, “Muna da dalilin yin baƙin ciki, saboda sun tafi mana da ’ya’ya, kuma suka kashe mana Malam Yakubu Makuku, saboda ya nemi kada su ɗauki yaran. Haƙiƙa wannan babban rashi ne.”

Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi, Abdullahi Idris Zuru, ya shaida wa Aminiya cewa an turo ƙarin jami’an tsaro daga Abuja zuwa jihar domin su taimaka a aikin da ake yi na nema da kuma ceto ɗaliban.

Tun da farko Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da harin, tare da sanar da cewa tuni jami’an tsaro da mafarauta suka fara aikin ceto ɗaliban.

Aminiya ta ruwaito cewa Gwamna Jihar Kebbi, wanda labarin harin ya sa shi gaggawar yanke ziyarar aiki da ya kai Abuja, ya yi wata ganawa da iyayen ɗaliban, inda ya ba su tabbacin yin duk mai yiwuwa tare da jami’an tsaro domin kuɓutar da yaran.

Karo na biyu ke nan da ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar kwana ta ’yan a Jihar Kebbi suka yi garkuwa da gomman dalibai — na farko shi ne a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamantin Tarayya da ke Birnin Yauri.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji
  • GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
  • Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana
  • Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
  • ’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara
  • Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16
  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
  • Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP
  • PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu