Aminiya:
2025-11-18@15:21:53 GMT

Matan Sojojin da aka tsare a Maiduguri sun nemi a yi wa mazajensu afuwa

Published: 2nd, October 2025 GMT

Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa.

Matan da yawansu ya haura 30 tare da wasu yara ’yan ƙasa da shekara biyu da suka haɗa da ‘yan uwa da abokan arziki sun ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da ke Maiduguri a ranar Laraba don miƙa wannan koke na su.

HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku

Mai magana da yawun, su Madam Rose Emmanuel David a lokacin da take zantawa da manema labarai ta ce, an tsare wasu mazajensu ta hanyar aikata ƙananan laifuffuka sama da shekara guda.

Rose ta jaddada cewa hakan ya jefa su cikin halin wahala matuƙa musamman wajen shawo kan matsalolin iyali, saboda hakan ya tilasta musu yin sana’o’in da ba su dace da su ba domin ɗaukar nauyin kuɗin makaranta da ciyar da ‘ya’yansu.

Sun yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya da hukumomin soji sun shafe shekaru suna yin afuwa ga ’yan Boko Haram, ’yan fashi da sauran masu aikata muggan laifuka.

“Don haka ya zama wajibi su bayyana ra’ayinsu, ta hanyar roƙo a madadin mazajensu da ke tsare a ofishin ’yan sandan Soja (MP) da ke Maiduguri ko su ma sa samu ‘yancinsu da kuma haɗuwa da mu iyalansu.”

“Muna nan a madadin mazajenmu da aka tsare sojojin Nijeriya a ofishin ’yan sandan Soja na runduna ta 7 da ke Maiduguri don miƙa kokenmu.”

“Muna cikin tawali’u da neman jin ƙai da gafara, kasancewar da yawa an tsare su tsawon watanni da shekaru kan laifuka dabam-daban, tun daga lokacin sun amince da kura-kuransu, sun yi tunani sosai, kuma yanzu suna neman dama ta biyu don yi wa ƙasarsu hidima.

“Muna cikin girmamawa muna kira ga mai girma shugaban ƙasa, kuma babban kwamandan sojojin ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya yi musu afuwar shugaban ƙasa.”

“Muna kuma kira ga majalisun dokoki na ƙasa, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da dukkan ’yan Nijeriya da su goyi bayan wannan roƙo na mu don ganin an sako mana mazajenmu, wadda ya kamata a tuna cewa, an yi afuwa ga tubabbun ‘yan tada ƙayar baya da ‘yan bindiga da suka taɓa tayar da fituntuni a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP

এছাড়াও পড়ুন:

Iran : kasantuwar sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ce ga zaman lafiyar duniya  

Iran ta yi gargadin cewa tsanantar ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean da Latin Amurka na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, kuma ta yi kira da a girmama hurumi da cikakken yancin Venezuela.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya ce barazanar Amurka na amfani da karfi kan zababiyar gwamnatin Venezuela ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Ya kuma bayyana cewa irin wadannan ayyuka tamkar keta ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, musamman haramta amfani da karfi.

A daya bangaren kuma, M. Baghai ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ke kai wa jiragen kamun kifi na Venezuela a matsayin misalai na kisan gilla ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma yi kira ga Washington da ta daina keta ikon kasar Venezuela a karkashin hujjar yaki da miyagun kwayoyi, sannan ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da Sakatare Janar António Guterres da su sauke nauyin da ke kansu na hana duk wani karin tashin hankali.

Amurka ta kai hare-hare akalla sau 20 kan kananen jiragen ruwa da take zargi da hannu a safarar miyagun kwayoyi a yankin Caribbean da Pacific, Wadannan sukayi sanadiyyar mutuwar mutane 80.

Tun daga watan Agusta, Amurka ta tura jiragen ruwa a yankin ciki har da katafaren jirin nan na sojojin ruwan ta mafi girma a duniya USS Gerald R. Ford da jiragen yaki samfarin F35 da dubban sojoji zuwa yankin Caribbean, bisa fakewa da yaki da kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi na Latin Amurka.

Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya yi watsi da zargin hannu a safarar miyagun kwayoyi, yana mai jaddada cewa Washington tana amfani da batun don ci gaba da shirinta na “canjin gwamnati” da kuma kwace arzikin mai na Venezuela.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025  Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin  Da Kotu  Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025  An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba November 15, 2025 Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi
  • MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi
  • Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira
  • Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon
  • Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.  
  • Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang
  • Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya
  • Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa
  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
  • Iran : kasantuwar sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ce ga zaman lafiyar duniya