Aminiya:
2025-11-18@12:35:08 GMT

’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe

Published: 30th, September 2025 GMT

Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta cafke wasu mutane hudu da ake zargi da aikata laifuka iri-iri a sassa daban-daban na jihar, biyo bayan samamen da aka kai a kan wadanda ake zargi da aikata munanan laifuka.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Dungus Abdulkarim ya fitar, ya ce kamen da aka yi ya nuna yadda rundunar ke jajircewa wajen kare doka da oda a fadin jihar.

An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya

A cewarsa, wannan mataki na daga cikin manyan dabarun tsaro da rundunar ta sanya gaba domin magance laifuka da hana su faruwa gaba daya.

“A cikin makon nan da muke ciki, jami’anmu sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a sassa daban-daban na jihar.

“Wannan na zuwa ne bisa ci gaba da kokarin da rundunar ke yi don tabbatar da zaman lafiya a Yobe,” in ji SP Abdulkarim.

A karamar hukumar Nguru, an kama wasu matasa biyu — Jarma Hussaini Adam mai shekaru 25, da Mohammed Abdusalam mai shekaru 16 — bisa zarginsu da yi wa wani jami’in ‘yan sanda dukan kawo wuka tare da sace bindigarsa.

Lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Satumba, 2025, a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Nguru, inda aka tsinci CPL Amani Ali jina-jina a sume.

Bayan bincike mai zurfi, jami’an tsaro sun yi nasarar kwato bindigar da kuma cafke wadanda ake zargi, yayin da shi kuwa jami’in ke karbar magani a babban asibitin Nguru.

A babban birnin jihar, Damaturu, jami’an ‘A’ Division sun cafke Ibrahim Alhaji Ahmadu, mai shekaru 24, bisa zargin shiga gona da dabbobi, sannan ya yi wa wani manomi barazana da bindiga.

Rahoton da aka kai ofishin ‘yan sanda a kan kari, ya sa aka dauki matakin gaggawa, inda aka kwato bindigar da kuma harsashi daga hannunsa.

Rundunar ta jaddada cewa mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba da kuma yin barazana da ita babban laifi ne da za a hukunta bisa doka.

A can garin Potiskum kuwa, an cafke Dahiru Ali, mai shekaru 19, bisa zarginsa da yi wa wata yarinya ‘yar shekara uku fyade.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a unguwar da suke zaune, kuma ya amsa laifinsa. Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike kafin gurfanar da shi a gaban kotu.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Yobe, CP Emmanuel Ado, ya bayyana takaici da damuwa matuka kan wadannan laifuka, yana mai Allah-wadai da su da kakkausar murya.

Ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar masu laifi, yana mai gargadin masu aikata laifuka da su daina ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

“Muna bukatar hadin kan iyaye da su kara sanya idanun lura a kansu, domin kaucewa fadawa tarkon masu laifi,” in ji Kwamishinan.

A karshe, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa ‘yan sanda bayanai akan lokaci, don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin Jihar Yobe.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Yobe da ake zargi mai shekaru

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi

’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu ’yan bindiga biyar tare da ƙwace tarin makamai a hannunsu a yankin Zuru–Tadurga da ke Jihar Kebbi.

Rundunar ’yan sanda ta musamman da ta kama su, ta bayyana cewa, ’yan bindiga suna cikin waɗanda suka kai hare-hare a kan al’ummomin Zuru a kwanakin baya.

Ta ƙara da cewa dukkansu ’yan asalin kauyen Birnin Tudu ne da ke cikin ƙananan hukumomin Bukkuyum da Gummi a Jihar Zamfara.

Kakakin ’yan sanda a jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce makaman da aka ƙwato daga hannun ’yan bindigar sun haɗa bindigogi AK-47 guda 7 a wata ƙaramar gida guda 1 da harbi-ruga guda uku.

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara Da amincewar hukumomi nake tattaunawa da ’yan bindiga — Sheikh Gumi

Sauran sun haɗa da kurtun albarusan AK-47 guda 3  da harsashi 89 da kuma tsabar kuɗi Naira miliyan 2.6

Ya ƙara da cewa an miƙa waɗanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Birnin Kebbi domin ci gaba da bincike da kuma gano sauran abokan aikinsu.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kebbi, Bello M. Sani, ya yaba da jarumta da jajircewar jami’an rundunar tare da ƙarfafa su da kada su yi ƙasa a gwiwa har sai an kawar da matsalar ’yan bindiga da garkuwa da mutane daga jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanzu-yanzu: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP
  • Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshe 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda
  • ’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi
  • Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
  • APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe
  • PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu
  • Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso