Sharhin Bayan Labarai: Shin Kissan Mutanen Gaza Gaba Daya
Published: 25th, April 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan ‘wani makircin da kasar faransa ta kullawa falasdinawa a gaza’ don su amfana da kwararrunsu’ wanda ni tahir amin zan karanta.
///… Shugaba kungiyar kare hakkin bil’adama masi suna [the Euro-Mediterranean Human Rights Monitor] ta fallasa wani shiri tsakanin gwamnatin kasar faransa da HKI na fitar da kwararru da kuma masana falasdinawa da suka rage a Gaza, zuwa wajen yankin, kafin HKI ta fa wani gagarumin kissan kiyashi a yankin kashe falasdinawa da suka rage a yankin.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Ramy Abdu shugaban kungiyar na fadar haka, ta kuma kara da cewa, offishin jakadancin kasar Faransa da ke birnin Qudus da aka mamaye, yana aiki tare da HKI don zakulo masana da kwararru a fannonin ilmi daban daban da ke tsare a cikin zirin gaza, zuwa wajen yankin saboda amfani da su don amfanin kansu.
Rahoton ya kara da cewa, wadanda zasu fitar daga yankin na Gaza, sun hada da dukkan masu digiri na uku wato PHD, likitoci, inginiyoyi, masanan tarihi da kuma wadanda suke da korewa a abubuwan al-adu da kayakin tarihi .
Kamfanin dillancin labaran Parstoday a kara da cewa wannan shi ne wannan gagarumin aiki mikirce ne tsakanin Faransa da sojojin HKI na korar Falasdinawa daga Zirin gaza. Wannan shirin, inji Ramy Abdu ya sabawa dokokin kasa da kasa, kuma kasar faransa ta fada cikin wannan laifin wanda ake iya gurfanar da kasar da ta aikata haka a gaban kuliya.
Abdu ta kara da cewa abinda HKI ta kasa samu tare da amfani da makami tana son ta yi amfani da kungiyoyin kare hakkin bil’adama don cimma wanna manufar.
Kafar yada labarai da kasar Burtaniya mai suna ‘Middle East Eye’ HKI ta fara wani shiri na musamman, mai matakai 5 don tabbatar da ba wani bafalasdine da ya rage a Gaza, wanda kuma zai bata damar kafa kasar “yahudawa zalla’ a kan kasar Falasdinu.
Yahudawan sun sha nanata manufarsu ta ganin dukkan falasdinawa sun fice daga Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan tun bayan an fara yakin 7 ga watan Octpba shekara ta 2023.
Jaridar ta kara da cewa gwamnatin HKI ta fara aiwatar da wannan shirin, yana da matakai 5, kuma sun hada da, saka Falasdinawan cikin yunwa, rage yawan falasdinawa a gazar ta hanyar kashe su matukar iyawarsu, da lalata tsarin kiwon lafiya, ta yadda dan karamin cuta zata kashesu, maida gaza wurin da ba wanda zai ita rayuwa cikinsa, sannan daga karshe anfani da dokokin kasa da kasa na maida gaza bangare na HKI bayan sun kammala kashe sauran falasdinawa a yankin.
Wannan ya nuna cewa zasu kashe falasdinawa kimani miliyon 2 a cikin karamin. Don haka a wannan tsarin suna ganin a mataki na 5 sun kammala kashe dukkan falasdinawa a gaza.
Jaridar ta kammala da cewa idan wannan shirin bai yi aiki ba suna da wani tsari wanda zai kasu ga shafe dukkan Falasdinawa a gaza. A cikin watan Jenerun wannan shekara ne shugaban kasar Amurka Donal trump ya bayyana wannan ra’ayin. Sai dai wannan ba ra’ayinsa na karan kansa ba, ra’ayi ne na yahudawan na samar da kasar yahudawa zalla tun asali.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: falasdinawa a gaza a kara da cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa adadin waɗanda talauci ya yi wa katutu a Nijeriya zai ƙaru zuwa kaso 3.6 cikin ɗari a 2027.
Wannan dai na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar game da tattalin arziki da kuma yanayin tsadar rayuwa a Nijeriya.
Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura a Sifaniya da Portugal Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin MusulmiBankin Duniya ya fitar da rahoton ne bayan ganawa tsakanin wakilansa da na Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF kamar yadda RFI ya ruwaito.
Rahoton ya ce dogaro da Nijeriya ta yi gaba ɗaya kan man fetur na ɗaya daga cikin dalilin da zai sa haɓakar tattalin arzikinta ya ci gaba da tafiyar hawainiya.
Bankin Duniyar ya ce har yanzu mahukuntan Nijeriya ba su ɗauko hanyar fitar da ingantattun tsare-tsaren tattalin arziki da za su taimaki talakawan ƙasar ba.
A cewarsa, abin takaici ne yadda talakawan ƙasashe masu tarin albarkatu ke fama da talauci saboda rashin mayar da hankali daga shugabanni.
Bankin ya ce duk da ci gaban da Nijeriya ta samu a sauran fannonin da ba na man fetur ba musamman a bara, amma duk da haka babu alamar samun ci gaba a ɓangaren tattalin arzikin talakawan ƙasar ta yammacin Afirka.
Rahoton ya jaddada cewa har yanzu yankin ƙasashen Sahel ne ke kan gaba a talauci a duniya gaba ɗaya, yayin da yankin ke da kaso 80 adadin mutane miliyan 695 na mutanen da ke fama da baƙin talauci.