Aminiya:
2025-09-19@08:44:52 GMT

’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa 

Published: 25th, April 2025 GMT

’Yan bindiga sun kashe wani sabon ango, sun kuma yi wani gaba da amaryasa bayan kwanaki 11 da ɗaura aurensu a wata unguwa a Jihar Nasarawa.

Ganau sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kai hari gidan sabbin ma’auratan ne da misalin ƙarfe karfe 11:00 na dare ranar Laraba, inda suka harbe angon har lahira, sannan suka tafi da matar zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Name(required) Email(required) Website Message

Submit

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Akaleku, da ke Ƙaramar Hukumar Obi ta Jihar Nasarawa, a kan hanyar Lafia zuwa Makurɗi.

Ma’auratan, Mista da Misisi Alu Anzaku, an ɗaura aurensu ne a ranar 12 ga Afrilu, 2025.

An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aure

Majiyoyi masu kusanci da iyalan ma’auratan sun ce da alama suna cikin lokacin amarci lokacin da wannan mummunan lamari ya faru, wanda ya katse sabuwar rayuwarsu tare.

Har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, ’yan uwa da abokan arziki sun ci gaba da nuna matukar damuwa, saboda har yanzu ba a samu wani labari game da inda amaryar da aka sace take ba, ko kuma halin da take ciki.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ba amsa kiran waya da sakonnin tambayoyin da wakilimmu ya aika mata game da lamarin ba har zuwa lokacin da aka kammala rubuta wannan labarin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Amarya Ma aurata

এছাড়াও পড়ুন:

Kotun Sojin Nijeriya Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Soja Da Ya Kashe Ɗan Adaidaita

Kotun ta kuma samu Musa da mallakar harsashi na musamman har guda 34 mai nauyin (7.62mm) ba bisa ƙa’ida ba.

 

Ga laifin kisan kai, sashe na 220 na kundin laifuffuka da kuma hukuncin da ke karkashin sashe na 221, Musa an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. A laifi na biyu na mallakar harsasai ba bisa ka’ida ba, sashe na 8 (1) na dokar bindigogi, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari. Bugu da ƙari, an kore shi daga aikin sojan Nijeriya acikin ƙasƙanci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotun Sojin Nijeriya Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Soja Da Ya Kashe Ɗan Adaidaita
  • Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar
  • Yadda jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa yayin tsere wa harin ’yan bindiga a Neja
  • ’Yansanda Sun Kama Mutane 9 Kan Yin Ƙaryar Sace Su A Jihar Neja
  • ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m
  • Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas
  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu