Gwamnati ta amince ta bai wa mahajjata kuɗin guzirinsu a hannu
Published: 25th, April 2025 GMT
Gwamnatin Najeriya ta amince kuma ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki.
Hakan ya biyo bayan tsoma bakin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi wanda ya roƙi shugaba Bola Tinubu a madadin maniyyatan ta hannun Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON.
Hukumar NAHCON a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh, ta dage cewa ɓullo da hada-hadar kuɗi ta amfani da kati zai shafi shirin hukumar na gudanar da ayyukan hajjin 2025.
Shugaban ya damu matuƙa da cewa amfani da katin banki na dole da babban Bankin Najeriya CBN ya gabatar don gudanar da aikin hajji zai kawo tarnaƙi ga tsare-tsare da kuma gudanar da aikin Hajjin bana na 2025.
Bayan ganawar Hukumar NAHCON da Mataimakin shugaban ƙasa, Kwamishinan tsare-tsare da ayyukan kuɗi na NAHCON, Aliu Abdulrazaƙ, na cewa hakan zai bai wa mahajjan Najeriya damar kashe kuɗaɗensu da hannunsu yayin ibadar a Saudiyya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.
Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.
“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.
Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.
Gwamnan ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria