Faransa ta jaddada aniyarta na ci gaba da tattaunawar nukiliyar iran
Published: 25th, April 2025 GMT
Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran.
A yayin taron manema labarai na mako-mako a birnin Paris, Christophe Lemoine ya jaddada cewa: “Muna ci gaba da jajircewa wajen warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye muke mu ci gaba da tattaunawa da Tehran.”
Wannan bayanin na zuwa ne bayan da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X cewa, Tehran a shirye ta ke ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai, inda ya bayyana cewa tattaunawar za ta iya bude wata sabuwar hanya.
Araghchi ya bayyana cewa, bayan shawarwarin baya-bayan nan da aka yi a Moscow da Beijing, a shirye yake ya ziyarci Paris, Berlin da London.
Ya kuma ce tun kafin fara tattaunawar da Amurka, Iran na shirye, amma kasashen Turan uku da batun ya shafa ba su nuna sha’awarsu ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ci gaba da tattaunawa nukiliyar Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi: Iran ba za ta tattauna kan batun inganta sinadarin Uranium din ta ba
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Iran ba za ta tattauna ba kan batun inganta sinadarin Uranium din ta a tattaunawar da ta ke da Amurka ba, kuma ba za ta yi watsi da wannan hakki ba a kowe irin dalili.
“A halin yanzu muna fuskantar wani matsayin Amurkawa marasa ma’ana wanda ya saba wa hankali.
Ministan harkokin wajen na Iran ya jaddada cewa Iran ta shiga tattaunawa don tabbatar da hakkokin al’ummar kasar, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba a kan wadannan hakkokin.
“A ra’ayinmu, batun inganta [uranium] kwata-kwata ba abu ne da za a iya sasantawa ba,” in ji shi.
A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata na bayar da amsa karara, kuma a yau jagora ya fayyace matsayinmu, in ji Araghchi yayin da yake magana kan kalaman da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a ranar Talata, inda a cewarsa ba daidai ba ne Amurka ta dage cewa Iran ta daina ayyukanta na inganta makamashin Uranium ta hanyar lumana.
Ayatullah Khamenei ya ce: “hana Iran ta inganta sinadarin Uranium, babban kuskure ne.”
Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da manufofinta, hanyoyinta da kuma aiwatar da su, inji Jagoran inda ya jaddada cewa ba wani mahaluki da zai hana Iran inganta sinadarin urenium din ta.
A cikin ‘yan kwanakin nan, jami’an Amurka sun ce dole ne Iran ta kawo karshen duk wani aikin inganta sinadarin Uranium, batun da jami’an Iran suke ba zai yi wu ba.