UCL: Real Madrid ta murƙushe Man City da ci 3
Published: 20th, February 2025 GMT
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta sake doke Manchester City da ci 3 da 1 a filin wasa na Bernabeu.
Madrid ta karɓi baƙuncin Man City a wasan zagaye na biyu na gasar Zakarun Turai, bayan doke ta a gida da ci 3 da 2.
Gobara ta ƙone gidaje, dabobbi da kayan abinci a Kano Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan TsaroKylian Mbappe ne ya zama tauraro a wannan wasan, inda ya jefa wa Manchester City ƙwallaye uku rigis a raga.
Ɗan wasan gaban na Real Madrid, ya fara jefa ƙwallo ta farko a minti na 4 da fara wasa, sannan ya jefa ƙwallo ta biyu a minti na 33.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne, Mbappe ya sake jefa ƙwallo ta uku a ragar Manchester City a minti 61.
A minti na 92 ɗan wasan Manchester City, Nico Gonzalez, ya warware mata ƙwallo ɗaya.
A haka wasan ya ƙare, amma Jude Bellingham ya samu katin gargaɗi, wanda hakan ke nufin ba zai buga wa Madrid wasanta na gaba a gasar ba.
Idan aka raba jadawalin ƙungiyoyin da za su kara da juna, Real Madrid za ta iya haɗuwa da Bayer Leverkusen ko Atletico Madrid.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gasar Zakarun Turai
এছাড়াও পড়ুন:
Lamine Yamal Ya Buga Wasa 100 A Barcelona
Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville.
Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin.
Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp