2025-09-18@07:09:09 GMT
إجمالي نتائج البحث: 79

«Maɓoya»:

    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce...
    Ɗan takarar jam’iyyar Labour a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma sabon Olubadan na Ibadan, Rashidi Ladoja, a wani zagayen ganawa da manyan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027. Obi, wanda ke ƙoƙarin ƙara yauƙaƙa zumunci da manyan shugabanni a fadin ƙasar, ya bayyana cewa ziyarar...
    “Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki.  ...
    Firaministan Japan, Shigeru Ishiba, ya sanar da murabus dinsa a matsayin shugaban jam’iyyar Liberal Democratic Party (LDP), watanni kaɗan bayan jam’iyyarsa ta sha mummunan kaye a zaɓen watan Yuli. Ishiba ya sanar da matakin ne a ranar Lahadi, duk da cewa a baya ya yi ƙoƙarin kaucewa matsin lambar ‘yan jam’iyyarsa da ke neman ya...
    Ya kuma nuna damuwa kan rikicin magoya bayan wasu ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na iya tayar da hankali a jihar. Game da tsaro kuwa, Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnati na ɗaukar matakai don shawo kan matsalolin da ke tasowa a wasu sassan jihar. Ya ce sun ƙarfafa haɗin...
    Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027. Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike,...
    Wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan masu fafutikar nan ta “Bring Back Our Goodluck” ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ya tsaya takara a Zaɓen 2027. Ƙungiyar ta ce a Zaɓen 2015 an yaudari ‘yan Najeriya da suka dage wajen ganin bai yi nasara ba a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na...
    An bayyana sakamakon zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Zariya da kewaye, da kuma Mazabar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna. Zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da rahoton tashin hankali ba. Isa Haruna Ihamo na APC ya yi nasara A zaɓen da aka gudanar a Zariya,...
    Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya sha kaye a rumfar zaɓensa yayin zaɓen cike gurbi na mazabar Garki-Babura a Jihar Jigawa ranar Asabar. Ministan ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar Ɓaɓura Ƙofar Arewa Primary School 001, inda sakamakon da aka bayyana, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 112, yayin da PDP ta samu 308 a rumfar zabensa....
    Aƙalla mutum 164,390 ake sa ran za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin Jihar Kaduna a mazaɓar Zariya da kewaye. Sai dai yawancin masu zaɓe ba su fito ba. APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna. Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan...
    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da kama aƙalla ’yan daba 100 da ake zargi da tayar da zaune-tsaye a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bagwai a Jihar Kano. Kwamishinan INEC na Jihar Kano, Abdu Zango, ya shaida wa manema labarai a Bagwai cewa jami’an tsaro...
    Ga hotunan yadda ake gudanar da zaɓen cike gurbi a sassan Najeriya.
    Jami’an tsaro sun kama wani mutum da tsabar kuɗi Naira miliyan 25 da ake zargin kuɗin sayen kuri’a ne a zaɓen cike gurbin da ke gudana a Jihar Kaduna. Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka...
    “Duk da cewa jama’a suna da ‘yancin nuna sha’awarsu kan siyasa, shirye-shiryen amincewa, yunƙurin tattarawa, da tallace-tallace irin na kamfen da nufin tallata ‘yan takara kafin lokacin yaƙin neman zaɓe na hukumance ba a amince da su ba. “INEC tunin ta nusar da wannan batun a lokacin ganawarta da jam’iyyun siyasa, ta kuma gargaɗin dukkanin...
    Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma...
    Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala...
    Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya gargadi ’yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina zagin malaman addini da a yanzu ya zama ruwan dare a ƙasar nan. Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan mummunar ɗabi’a ta cin zarafi malaman addini na iya lalata zamantakewa da tubalin zaman lafiya a tsakanin...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka sake lashe zaɓe a 2027, hakan zai lalata makomar ’yan Najeriya. El-Rufai, ya faɗi haka ne a Jihar Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da jam’iyyar adawa ta ADC, ta shirya. Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka...
    Bayan shekar 22 da kuɓutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuraɗiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kuɗin ƙasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe, maƙudan kuɗin da ake ware wa Hukumar Zaɓe ta...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta...
    Ɗaya daga cikin jigo da suka kafa Jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi zai kayar da duk wani ɗan takara a jihohin Arewacin Najeriya idan ya tsaya takara a PDP. Da yake bayabni a tashar talabijin ta Arise TV a ranar Laraba, Gana ya ce, “Ni...
    Al’ummar Arewacin Najeriya na shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 saboda ƙuncin rayuwa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa da suka mayar da yankin saniyar ware. Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal  ne ya bayyana haka, yana mai cewa gamayyar shugabanni da ’yan siyasar Arewa na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo. Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a...
    Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce adadin mutanen da zazzaɓin lassa ya kashe bana sun kai 151 a fadin kasar. Cikin wata sanarwa da NCDC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, ta ce yawan kisan da cutar zazzaɓin lassa ke yi ya ƙaru daga kashi 17.3 cikin 100...
    Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓarkewa (ATBUTH) da ke Bauchi zai fara gwajin rigakafin cutar zazzabin Lassa. Wannan shiri na da nufin tabbatar da ingancin rigakafin, kuma wani ɓangare ne na babban shiri mai kasashe da yawa mai suna “Background Rates of Adverse Events for Vaccine Evaluation in Africa (BRAVE).” ATBUTH na daga cikin...
    Hadimin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, kan Harkokin Yaɗa Labarai, Temitope Ajayi, ya mayar wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha martani, kan cewa Tinubu bai taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba wajen zama shugaban ƙasa a 2015. Ajayi, ya ce Buhari yana da ƙarfi sosai a Arewa amma hakan bai hana shi faɗuwa...
    Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce ba Shugaban Kasa Bola Tinubu kaɗi ne ya sa Muhammadu Buhari ya ci zabensa a shekarar 2015 ba. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Abuja ranar Laraba, yayin kaddamar da littafin da mai magana da yawun tsohon Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya wallafa...
    Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce duk wani yunƙuri da Shugaba Bola Tinubu, zai yi ba zai hana jam’iyyar APC faɗuwa a zaɓen 2027 ba. Yayin wata hira da aka yi da shi a Jos, a Jihar Filato, Dalung, ya ce ko da Tinubu zai naɗa ɗansa Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), ko...
    Majalisar Dokokin Jihar Filato ta zaɓi Nanloong Daniel a matsayin sabon Kakakin Majalisar, bayan da Gabriel Dewan ya yi murabus. Zaɓen sabon kakakin ya gudana ne a wani zaman gaggawa da majalisar ta gudanar ranar Laraba. David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu Najeriya ta kammala dawo da alhazan da...
    Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane...
    Batun sauya sheka da ke faruwa a cikin tsarin siyasar Nijeriya, Jega ya kira a hana sauya sheka ga wadanda aka zaba a bangaren zantarwa da kuma ‘yan majalisa. Ya kuma yi kira ga jami’an INEC a matakin tarayya, da na jihohi su shirya gudanar da zaben cike gurbi da zarar an samu labari game...
    A yau ne Najeriya ke bikin ranar Dimokuraɗiyya, wanda masana siyasa a ciki da wajen ƙasar ke jinjina kan yadda aka kwashe shekara 26 kan tafarkin mulkin farar hula. Najeriya, ta kasance ƙasa mafi yawan al’umma a Nahiyar Afirka inda ake bikin murnar ranar dimokuraɗiyyar domin tunawa da zaɓen 12 ga watan Yuni wanda ake...
    Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Nijeriya ACF ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da manyan muƙarraban gwamnatinsa da su daina gaggawar shige-da-fice wajen neman tazarce a Zaɓen 2027. ACF ta ce zai fi dacewa gwamnatin Tiinubun ta mayar da hankali wajen ganin ta kyautata rayuwar ’yan Nijeriya maimakon gangamin yaƙin neman a sake zaɓensa a 2027, lamarin...
    A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun...
    Maƙabartar Kuka Bulukiya maƙabarta ce mai daɗaɗɗen tarihi a cikin ƙwaryar birnin Kano, wadda bayanai suka nuna an shafe sama da shekara 500 ana binne mamata a cikinta. Wannan daɗaɗɗiyar maƙabarta tana da matuƙar muhimmanci musamman la’akari da yawan unguwannin da suka kewaye ta da yawan mutanen da aka binne a cikinta da kuma fitattun...
    Hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutane 366 a sakamakon zazzaɓin Lassa da cutar sanƙarau a ƙasar, lamarin da aka bayyana da ƙalubalen kiwon lafiyar ga al’umma sanadin waɗannan cututtuka. Daga ranar 1 ga Janairu zuwa 18 ga Mayu, 2025, NCDC ta tabbatar da ɓullar cutar zazzaɓin Lassa guda...
    Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya amince da wannan batun na takwaransa cikin gaggawa.   “Na tsaya a madadin Sanatoci 109 da ‘yan Majalisar Wakilai 360 don amincewa da wannan matakin na Akpabio,” in ji Abbas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    “Hukumar ta amince da ƙirƙiro sashen AI a ƙarƙashin ɓangaren fasahar sadarwa na hukumar domin cin ribar AI da fasahar da take ɗauke da ita da kuma magance ɓarnar da fasahar ka iya kawowa a lokutan zaɓe” a cewar sanarwar   Wannan matakin da INEC ta ɗauka dai ya biyo bayan tarurruka da dama da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ɗaya daga cikin ginshiƙan tsarin dimokuradiyya shi ne zaɓi – bai wa jama’a dama su zaɓi abin da suke so, ko kuma wanda suke so ya shugabance su. Wannan ne ya sa ɗaya daga cikin muhimman matakai a kafuwar tsarin shi ne zaɓe. Sai dai kuma abin tambaya...
    Babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce, ta soma ɗaukar matakan ɗinke ɓarakar da ta dabaibaye ta a ’yan shekarun nan. Matakin baya-bayan nan shi ne na taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta gudanar. Guguwar raba Masarautar Katsina ta kunno kai Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma Shin ko hakan...
    Tsohon Shugaban APC na ƙasa, Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa ko yau aka yi zaɓe, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai yi nasara. Oshiomhole wanda shi ne mai wakiltar shiyyar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawan Nijeriya ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da gidan talabijin na Channels a safiyar wannan Larabar. DAGA...
    Tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, ya musanta dalilin da tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa dangane da soke zaɓen 1993. Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriyar ya ce dalilin da IBB ya bayar cewa shi ne abin da ya sa ya rushe zaɓen 1993, “ba gaskiya” ba ne. Janar...
    “Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici...
    A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma...
    Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus. Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Merz a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zaɓen zagaye na biyu, bayan ya gaza samun ƙuri’un da yake buƙata a zagayen farko na zaɓen. A zaɓen farko Merz ya samu ƙuri’u 325 na jam’iyyun ƙawance daga majalisar...
    ’Yan siyasar yankin Arewa na ganin dole sai da goyon bayansu ɗan takara zai yi nasara a zaben Shugaban ƙasa. Hakan na zuwa ne bayan tsohon maitaimaka wa shugaban ƙasa a fannin siyasa, Alhaji Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa, nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa. An ɗaure ’yar...
    Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa zaɓen 2027 zai kasance ne kai tsaye tsakanin Shugaba Bola Tinubu da ’yan Najeriya da gwamnatinsa ta jefa su cikin mawuyacin yanayin rayuwa. Shugaban riƙo na PDP, Umar Damagum, ya jaddada cewa zaɓen “Tsakanin Jam’iyyar APC ne da ’yan Najeriya,” yana mai nuni da wahalar da talakawa ke fuskanta a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zazzaɓin cizon sauro, wato maleriya, na cikin cututtuka mafiya shahara da kuma haɗari a Najeriya. Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa Najeriya na da kaso mafi girma na mace-macen da cutar take haifarwa a duniya. Sau da yawa wanda ya kamu da cutar...