Aminiya:
2025-11-02@15:25:30 GMT

Firaministan Japan Shigeru Ishiba ya yi murabus

Published: 7th, September 2025 GMT

Firaministan Japan, Shigeru Ishiba, ya sanar da murabus dinsa a matsayin shugaban jam’iyyar Liberal Democratic Party (LDP), watanni kaɗan bayan jam’iyyarsa ta sha mummunan kaye a zaɓen watan Yuli.

Ishiba ya sanar da matakin ne a ranar Lahadi, duk da cewa a baya ya yi ƙoƙarin kaucewa matsin lambar ‘yan jam’iyyarsa da ke neman ya sauka sakamakon rashin nasarar zaɓen, inda ya dage cewa yana son tabbatar da yarjejeniyar haraji da ƙasar ta ƙulla da Amurka ta fara aiki yadda ya kamata.

’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo ’Yan ta’adda sun kashe mutum 63 a Borno

“Tun da Japan ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya, kuma shugaban Amurka ya rattaba hannu a matsayin doka, mun tsallake babban ƙalubale,” in ji shi.

“Lokaci ya yi da zan miƙa wa sabon jini tutar shugabanci,” ya ƙara da cewa.

Duk da murabus ɗinsa daga shugabancin jam’iyyar, Ishiba zai ci gaba da zama Firaminista har zuwa lokacin da za a gudanar da zaɓen cikin gida domin zaɓen sabon shugaban LDP.

Gidan Talabijin na Al-Jazeera ya ruwaito cewa wannan mataki ya ƙara jefa Japan, wacce ita ce ƙasa ta huɗu mafi girman tattalin arziƙi a duniya, cikin ruɗanin siyasa.

Tun bayan hawansa mulki a watan Oktoba da ya gabata, ɗan siyasar mai shekara 68 ya gamu da manyan ƙalubalai da suka yi sanadin kawar da rinjayen ’yan jam’iyyarsa a majalisun biyu na ƙasar.

Rashin nasarar, wanda aka danganta shi da ƙorafin jama’a kan tsadar rayuwa, ya sa gwamnatin Ishiba ta kasa aiwatar da manufofinta yadda ta tsara.

Yayin da ƙasar ke ƙara faɗawa cikin ruɗanin siyasa, manyan ‘yan jam’iyyarsa musamman daga bangaren ’yan ra’ayin mazan jiya sun matsa masa lambar yin murabus, waɗanda suka ɗora masa alhakin rashin nasara a zaɓen majalisar dattawa na Yuli.

Rahotanni sun ce Ministan Aikin Noma na Japan tare da tsohon Firaministan sun gana da shi a daren ranar Asabar domin shawartarsa da ya yi murabus.

A taron manema labarai da ya kira ranar Lahadi, Ishiba ya tabbatar da murabus ɗinsa, tare da bayyana cewa ya fara shirye-shiryen neman wanda zai gaje shi.

Yayin da ƙasar ke ƙara nutsewa cikin rudanin siyasa, manyan ‘yan jam’iyyarsa musamman daga bangaren ’yan ra’ayin mazan jiya sun matsa masa lamba da ya sauka, suna zarginsa da alhakin sakamakon zaben majalisar dattawa na Yuli.

Rahotanni sun ce Ministan Aikin Noma na Japan tare da tsohon Firayim Minista sun gana da shi a ranar Asabar da dare don shawarce shi ya sauka.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan jam iyyarsa

এছাড়াও পড়ুন:

Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka

Wasu lauyoyi biyu a Najeriya sun gargaɗi Gwamnatin Tarayya da ta yi taka-tsantsan wajen yin hulɗa da ƙasar Amurka, inda suka ce maganganun Amurka a kan Najeriya abun ruɗarwa ne 

Babban lauyan nan, Cuf Okoi Obono-Obla, wanda tsohon mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara ne, ya zargi Amurka da son raba kan ’yan Najeriya da sunan kare Kiristoci.

Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 

Ya ce iƙirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya ƙarya ne face nufin tayar da hankali da kawo rikici.

“Najeriya ba ta taɓa zama barazana ga zaman lafiyar duniya ba,” in ji Obono-Obla.

“Idan Amurka, inda ake yawan harbe mutane a coci-coci, ba ta gayyaci sojojin ƙetare su shigo musu ba, to kamata ya yi ta bar Najeriya ta magance nata matsalolin.”

Ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙurin Amurka na yin katsa-landan cikin harkokin Najeriya zai zama take doka da tauye ikon ƙasa.

Shi ma Barista Leonard Anyogo, kuma shugaban ƙungiyar ‘Good Governance Advocacy International’, ya shawarci Najeriya da ta bi hanyoyin diflomasiyya wajen mayar wa Amurka martani ba da faɗa ba.

“Ya kamata mu tattauna, ba mu yi fada ba,” in ji Anyogo.

“Najeriya ta nemi haɗin kai da Amurka a fannin tsaro da diflomasiyya domin kare muradunta.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa
  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Gwamnatin Gombe ta saurari ra’ayoyin jama’a kan kasafin kuɗin 2026