Zaɓen cike gurbi: An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a Zariya
Published: 16th, August 2025 GMT
Aƙalla mutum 164,390 ake sa ran za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin Jihar Kaduna a mazaɓar Zariya da kewaye.
Sai dai yawancin masu zaɓe ba su fito ba.
APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a KanoWakilinmu ya zagaya rumfunan zaɓe, inda ya gane wa idonsa yadda aikin zaɓen ke tafiya a hankali saboda matsalar na’urar tantancewa.
Malam Halliru Hamza, ya ce shi ma bai samu damar kaɗa ƙuri’a ba saboda na’urar taƙi ta tantance shi.
Ya ƙara da cewa mutane da dama ba su fito ba saboda yadda siyasa ke tafiya ba tare da ci gaba ba, sai tsadar rayuwa da rashin tsaro.
A gefe guda kuma, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna, Alhaji Ahmed Maiyaki, ya musanta zargin ‘yan adawa na cewa jam’iyyar APC ta shirya tafka maguɗi.
Ya ce hakan kawai alamar tsoro ne.
Kwamishinan ya ce APC ta yi aiki tuƙuru wajen neman goyon bayan jama’a, inda Gwamna Uba Sani da Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Abbas Tajudeen, suka jagoranci kamfen a wurare daban-daban ciki har da Zariya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zaɓen Cike Gurbi Zariya zaɓen cike gurbi
এছাড়াও পড়ুন:
An Taƙaita Zirga-Zirga A Ƙananan Hukumomi 4 Kafin Zaben Cike Gurbi A Kano
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp