An yaudari ’yan Nijeriya da suka hana Jonathan lashe Zaɓen 2015 — Ƙungiya
Published: 25th, August 2025 GMT
Wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan masu fafutikar nan ta “Bring Back Our Goodluck” ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ya tsaya takara a Zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta ce a Zaɓen 2015 an yaudari ‘yan Najeriya da suka dage wajen ganin bai yi nasara ba a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu, lamarin da yanzu kowa yake nadama saboda an jefa ƙasar cikin tsanani da tsadar rayuwa da rashin tsaro.
A yayin wani taro na Arewa maso Yamma da aka gudanar ranar Lahadi a Kano, madugun ƙungiyar na ƙasa, Dokra Grema Kyari, ya bayyana cewa lokaci ya yi da Jonathan zai dawo ya “ceci Najeriya daga matsin tattalin arziƙi da rashin zaman lafiya.”
Ya zargi jam’iyyar APC da shugabanninta a wancan lokaci, ciki har da marigayi Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu, da yi wa al’ummar Najeriya alƙawura na bogi.
Ƙungiyar ta jero dalilai huɗu da ta ce sun wajabta dawowar Jonathan da suka haɗa da samar da zaman lafiya, inganta tattalin arziƙi, shugabanci na haɗin kai da kuma kima a idon duniya.
Kyari ya yi nuni da cewa a zamanin Jonathan buhun shinkafa kilo 50 bai wuce N7,800 ba, amma yanzu yana kaiwa N80,000–N100,000.
Ya kuma ce manufofin gwamnatinsa kamar YouWin!, SURE-P da shirin bunƙasa noma sun amfani matasa da mata.
Ƙungiyar ta roƙi manyan ‘yan adawa kamar Atiku Abubakar, Rabi’u Musa Kwankwaso, Peter Obi da su haɗa kai su mara wa Jonathan baya a 2027, tana mai cewa “Zaɓen 2027 aikin ceto ne.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zaɓen 2015 Zaɓen 2027
এছাড়াও পড়ুন:
Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp