Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC daga hannun Shugaban ƙasa — IPAC
Published: 7th, October 2025 GMT
Ƙungiyar shugabannin jam’iyyun siyasa (IPAC) ta ce lokaci ya yi da za a cire ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) daga hannun Shugaban ƙasa.
Ƙungiyar ta ce kamata ya yi a kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai riƙa yin naɗin shugaban INEC da kwamishinoni da sakatare na hukumar domin tabbatar da gaskiya da cin gashin kai na hukumar.
Shugaban ƙungiyar IPAC, Dakta Yusuf Mamman Ɗantalle, ne ya bayyana haka a wani taro da suka yi da kwamitin Majalisar Wakilai da ke nazarin kundin tsarin mulki a Abuja.
Ya ce tsarin da ake amfani da shi yanzu na bai wa shugaban ƙasa damar zaɓar shugaban INEC na iya rage amincewar jama’a da hukumar.
Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su Tinubu ya umarci NAHCON ta rage kuɗin aikin Hajjin 2026“Don a tabbatar da sahihancin hukumar, dole a cire wannan iko daga hannun shugaban ƙasa. A kafa kwamiti da zai haɗa jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula, Lauyoyi, da wakilan Majalisar Dokoki domin su zaɓi shugaban INEC,” in ji shi.
Ɗantalle ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da adalci da gaskiya a cikin zaɓe, musamman duba da yadda aka yi ta samun ƙorafe-ƙorafe kan yadda zaɓukan baya suka gudana.
Wannan ra’ayi na IPAC ya yi daidai da irin shawarar da tsoffin shugabanni irin su Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan suka taɓa bayarwa, inda suka nemi a inganta tsarin naɗin shugaban hukumar domin ƙara sahihancin zaɓe.
A cewar su, wannan gyara zai taimaka wajen dawo da amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyya, musamman kafin zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.
A yanzu haka wa’adin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, na dab da ƙarewa bayan ya jagoranci zaɓukan 2019 da na 2023. Tuni aka fara raɗe-raɗin wanda zai maye gurbinsa.
Wasu jam’iyyun kuma sun bayar da shawarar cewa jam’iyyun da ke da wakilai a Majalisar Dokoki ta Ƙasa ne kawai za su riƙa bayar da sunayen wanda za a zaɓa domin wannan muƙami.
A nata ɓangaren, Ƙungiyar matasa Musulmi ta Lasa (NMYA) ta nemi majalisa ta duba kudirin doka da ke neman cire ikon shugaba da gwamnonin jihohi wajen naɗin shugabannin INEC da na hukumomin zabe na jihohi (SIECs).
Shugaban ƙungiyar, Injiniya Abdulraham Aliyu, ya ce, “Zaɓe mai gaskiya ba zai tabbata ba muddin shugaba yana da ikon naɗa wanda zai kula da shi.”
Ya ƙara da cewa fasahohin zamani kamar BVAS da IReV da INEC take amfani da su wajen gudanar da zaɓe ba za su yi tasiri ba idan hukumar ba ta zama mai gaskiya ba.
A gefe guda, ƙungiyar CISLAC ta nuna goyon bayanta ga kafa tsarin nadin INEC mai zaman kansa, amma ta ce ba ta goyi bayan rushe hukumomin zaɓe na jihohi ba, saboda hakan zai rage ƙarfin tsarin tarayya.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulki, ya ce, “Gyaran kundin tsarin mulkin da ake yi yanzu dole ne ya haifar da dimokuraɗiyya mai ɗorewa, inda jam’iyyun siyasa za su samu daidaito.”
Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda Sanata Mohammed Tahir Monguno ya wakilta, ya ce zaɓe mai gaskiya da ’yancin ƙananan hukumomi su ne tushen amincewar jama’a da gwamnati.
Ya ƙara da cewa goyon bayan kafa ’yan sanda na jihohi na iya zama hanyar magance matsalar tsaro a ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ikon naɗa Shugaban INEC Shugaban Ƙasa Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa
‘Yan sa’o’i kafin sanarwar da Jam’iyyar ta RN ta yi ne dai, tsohon Firaministansa Edouard Philippe ya ce yana goyon bayan shirya sabon zaben shugaban kasa a gaggauce.
Wannan matsin lamba dai kari ne kan wadda shugaban na Faransa ke fusakanta daga bangaren masu sassaucin ra’ayi, wadanda su kuma bukatarsu ita ce a zabi sabon Firaminista daga cikinsu.
Sai dai a iya cewa akwai ragowar fatan kawo karshen rudanin da siyasar Faransar ta shiga, la’akari da bayanan da suka ce a dazu an shiga tattaunawa tsakanin jagoran jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya Bruno Retailleau da Firaminista Lecournu, kwana guda bayan murabus din da ya yi. Yayin da kuma a gefe guda rahotanni suka ce a gobe Laraba wakilan masu sassaucin ra’ayi na jam’iyyar Socialist za su gana da Firaminista Lecournun mai murabus.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA