An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano
Published: 16th, August 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna.
Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan NajeriyaYa bayyana cewa an yi wannan kamen ne domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen.
Ya ce suna ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka tabbatar na da laifi za a gurfanar da shi a kotu.
Kiyawa, ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda.
A gefe guda kuma, ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ra lamunci tashin hankali ko rikicin siyasa a Kano ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan daba Zaɓen Cike Gurbi zaɓen cike gurbi
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya.
Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar.
Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-BissauJama’ar yankin ne suka kira rundunar cewar fasinjojin wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai launin baƙi sun jefar da wata jaka, sannan suka tsere.
Da jami’an rundunar suka isa, sun tarar da jakar da aka jefar.
Bayan gudanar da bincike, sun gano harsasai 210 na ɗangon 7.56mm.
DPO ɗin yankin ya sanar da sauran jami’an rundunar da ke kan hanyar Funtuwa domin dakatar da motar amma ba a ga motar ba.
Ana zargin direban da fasinjojin motar sun lura da jami’an tsaron da ke kan hanyar, wanda hakan ya sa suka zubar da jakar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yi kira ga jama’a da ci gaba da bai wa rundunar sahihan bayanai.
Ya jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da sintiri da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.
Ya kuma gargaɗi masu aikata laifi da su guji duk wani yunƙurin tayar da zaune-tsaye, inda ya ce duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani.