Zaɓen Jigawa: Ministan Tsaro ya faɗi a rumfar zaɓensa
Published: 17th, August 2025 GMT
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya sha kaye a rumfar zaɓensa yayin zaɓen cike gurbi na mazabar Garki-Babura a Jihar Jigawa ranar Asabar.
Ministan ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar Ɓaɓura Ƙofar Arewa Primary School 001, inda sakamakon da aka bayyana, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 112, yayin da PDP ta samu 308 a rumfar zabensa.
Zaɓen cike gurbin na Babura-Garki ya fara ne da tsauraran matakan tsaro a fadin mazabar. Jami’an tsaro suka kasance a rumfunan zaɓe da wuraren da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya.
A daidai ƙarfe 8:30 na safe, jami’an Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) sun isa rumfar Garki-Kofar Fada (003) inda suka fara shirye-shiryen zaɓe. Mr Ibrahim Shehu, jami’in zaɓe a rumfar, ya shaida wa manema labarai cewa zaɓen ya gudana lafiya ba tare da wata matsala ta tsaro ko fasaha ba.
Sarkin Zuru ya rasu yana da shekara 81 APC ta lashe zaɓen cike gurbi na Ghari/Tsanyawa a KanoA rumfar Primary Yamma (005), Ministar Ƙasa ta Ilimi, Hajiya Suwaiba Ahmad, ta yaba da yadda zaɓen ke gudana cikin kwanciyar hankali. Ta kuma bukaci al’umma su fito su kada ƙuri’a domin jam’iyyar APC. Hajiya Suwaiba ta bayyana kwarin gwiwa cewa APC za ta yi nasara a ƙarshe.
Sai dai, a wasu sassan mazabar, an ga mazauna suna ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, inda aka ga kasuwanci na gudana. Zaɓen ya samu fitowar jama’a mai yawa a yawancin rumfunan zaɓe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jigawa Ministan tsaro Zaɓe Zaɓen Cike Gurbi
এছাড়াও পড়ুন:
APC ya lashe zaɓen cike gurbi a Zariya
An bayyana sakamakon zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Zariya da kewaye, da kuma Mazabar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna.
Zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da rahoton tashin hankali ba.
Isa Haruna Ihamo na APC ya yi nasaraA zaɓen da aka gudanar a Zariya, Isa Haruna Ihamo na jam’iyyar APC ne ya samu nasara da ƙuri’u 26,613.
Nuhu Sada Abdullahi na jam’iyyar SDP ya zo na biyu da ƙuri’u 5,721, yayin da Mahmud Abdullahi Wappa na PDP ya samu ƙuri’u 5,331.
Tun watan Ramadan muke cikin duhu — Al’ummar Jauro Jatau NNPP ta lashe zaɓen Bagwai/Shanono a KanoFarfesa Balarabe Abdullahi, wanda ya bayyana sakamakon zaɓen, ya tabbatar da cewa Isa Haruna Ihamo ya cika dukkan sharuddan da ake buƙata don lashe zaɓen.
APC ta ƙara yin nasara a Mazaɓar BasawaA Mazaɓar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Farfesa Nasiru Rabi’u ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen da ƙuri’u 10,926, sai PDP ke biye da ƙuri’u 5,499.
Zaɓe cikin kwanciyar hankaliRahotanni sun tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin lumana ba tare da wata hayaniya ko rikici ba, lamarin da ya kara tabbatar da sahihancin sakamakon.