2025-09-18@00:57:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 68
«Dokokin Gyaran Haraji»:
Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara...
A cikin shekaru uku da kafuwarta, gidauniyar Misilli, ta mayar da yara 150 makarantar boko a Jihar Gombe, ciki har da mata 88 da maza 62, tare da ɗaukar nauyin kuɗaɗen karatunsu. Wannan mataki ya taimaka wajen rage nauyin iyaye marasa hali, inda suka samu ’yancin zaɓar makarantun da ke kusa da su. Ambaliya: NEDC...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Iyaye na ci gaba da kokawa kan yadda ilimi ke ƙara tsada yayin komawan ’ya’yansu makaranta a sabuwar shekarar karatu. Makarantu na ƙara ɓullo da sabbin hanyoyin karɓar kuɗi daga hannun yara da sunan koyarwa. NAJERIYA A YAU: Yadda ake gudanar da bukukuwar Sallar Gani yayin Mauludi DAGA...
Kasashe takwas, ciki har da Pakistan, Morocco, Syriya, Libya, Jordan, Lebanon da kuma Masar, sun himmatu wajen bayar da fifikon kula da cutar kansa ta yara, ta hanyar kula da ka’idojin kasa, ta hanyar yin gwajin cutar da a kan lokaci, samar da ingantattun magunguna da kuma samar da kudade don bai wa iyali kariya....
Kun tuna jita-jitar ake yaɗawa game wai arzikin sa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma Mutane da yawa sun gaskata. A matsayin sa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantan sa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa...
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa...
Farashin Man Fetur Ya Fadi Kadan Sabuda Fatan Kyarar Bututun DRUZHBAC Na Kasar Rasha Farashin man fetur ya tashi a kasuwannin duniya bayan da ana saran za’a kammala gyaran bututun kwararar man fetur na kasar Rasha watu DRUZHBA wanda yake kai man fetur zuwa kasashen turai ta kasashen Slovakia da kuma Hungary. Kamfanin dillancin labaran...

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya. A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian na Shirin wata kai wata muhimmiyar ziyara a kasashen Armeniya da Belarus. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, mai baiwa shugaban kasar shawara Mahdi Sanaei, ya ce Pezeshkian zai bar Tehran zuwa Yerevan a ranar Litinin din nan, sannan ya wuce Minsk. Ya kara...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun...
Tawagar Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta kai ziyarar ta’aziyya ga sabon Sarkin Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a fadarsa. Ziyarar ta biyo bayan rasuwar marigayi Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello, wanda aka yi ta murna da shi a bisa kyakkyawan jagoranci da kuma gudunmawar ci gaban masarautu da jihar Zamfara....
Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi samun ɓullar cutar kwalara a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka. Darektan Hukumar UNICEF mai kula da yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, Gilles Fagninou ne ya bayyana hakan tare da cewar annobar kwalara ta zama...
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala gyaran makarantu fiye da 1,200 a kananan hukumomi 44 na jihar a wani yunkuri na farfado da harkar ilimi. Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana hakan yayin taron bitar yini guda kan kara kaimi a tsarin duba ingancin karatu, da aka gudanar a...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano. Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: “Ina alfahari da zuwanku wannan zama...
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta ce ta kama wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin sace yara da yin garkuwa da su sannan ta kashe su. Rundunar ta ce wadannan kananan yara biyu mata ne ‘yan shekara bakwai, lamarin da ya jawo tarzoma da kona coci. Kakakin Rundunar, CSP Mohammed...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ce an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abubuwa na daban da kuma ba su damar shakuwa da ’yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da...
Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya. A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai...
Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure da a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin...
Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa Fursunoni 58 suna rubuta Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa NECO ta shekarar 2025. Wannan ci gaba ya samu ne bayan biyan kudin rajista da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Kofar-Nasarawa, ne...
Wani malamin addinin musulunci a jihar Zamfara, Sheikh Mohammed Tukur Sani Jangebe, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara da su gaggauta gudanar da kananan gyare-gyare daga mahadar Maru –Mayanchi – Maradun, da ke kan hanyar zuwa wani yanki na karamar hukumar Talata Mafara. Ya ce mummunan yanayin hanyar yana ci...
Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) a jihar Kano ta ce ta samu rahoton laifuka 351 na take hakkin yara daga cikin jimillar kararraki 446 da ta samu daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025. Kodinetan NHRC na jihar Kano Alhaji Shehu Abdullahi ne ya bayyana haka a Kano. Ya bayyana cewa daga...
Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum shida hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 120, bisa samun su da laifin satar yara da kuma sayar da su. Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Mercy Paul, Ebere Ogbono, Emmanuel Igwe, Loise Duru, Monica Oracha, da Chinelo Ifedigwe. PDP...
Ya nanata cewa nasarar da aka samu ya zuwa yanzu ta samo asali ne sakamakon kyawawan tsare-tsare, ingantaccen jagoranci, da kuma kula da albarkatu. Gwamnan ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar idan aka kwatanta da abin da ya gada a shekarar 2023. A cewar sa, inganta...
Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa wani mai suna Olukoye Olalekan hukuncin daurin shekaru 76 a kukuku saboda yada hotunan tsiraicin yara kanana da kuma aikata damfara. Alkalin kotun, Mai Shari’a Alexander Owoeye, ne ya yanke hukuncin ranar Alhamis, bayan ya samu mutumin da aikata laifukan da aka zarge shi da su....
Don girmama ziyarar shugaban ƙasa, gwamnatin jihar ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu domin bai wa mazauna yankunan damar halarta taron da kuma bin diddigin abubuwan da suka shafi ziyarar. Wannan ita ce ziyarar farko da Tinubu ya kai Jihar Benuwe tun bayan da rikicin ya ƙara tsananta. Jama’a da dama na kallon wannan...
Jimillar fursunoni: 80,879 Adadin cibiyoyin gyaran hali: 256 Kashi na rijista da aka kammala: 74% Umar ya jaddada cewa sauran fursunonin da ba a yi wa rijistar ba za a cigaba da yi musu, kuma an kafa duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da nasarar kammala aikin cikin sauki. Hukumar ta bayyana wannan aikin...
Attajirin nan na duniya dan asalin kasar Amurka, Bill Gates, ya ce a shekara 25 da gidauniyarsa ta yi da kafuwa, ya kashe Dalar Amurka biliyan 100, kwatankwacin Naira tiriliyan 161 wajen inganta kiwon lafiya a nahiyar Afirka. Attajirin ya bayyana hakan ne a Legas yayin wani taro da gidauniyarsa ta Gates Foundation ta shirya...
A wani yunkuri na rage adadin yara da suka daina zuwa makaranta, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da shiri mayarda yara 200,000 zuwa makaranta a cikin shekaru hudu masu zuwa, karkashin shirin Reaching Out-of-School Children (ROOSC). An bayyana wannan shiri ne a wani taron bita na kwanaki biyu da aka shirya tare da...
Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban...
Babbar jami’a a hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Shen Haiping, ta ce a shekarun baya bayan nan koshin lafiyar yaran kasar Sin na kara inganta. Jami’ar wadda ta bayyana hakan ga wani taron manema labarai a yau, ta ce a shekarar 2024, alkaluman mace-macen jarirai a kasar ya ragu zuwa jariri hudu cikin duk...
Kasar Faransa ta ce daga ranar daya ga watan Yuli mai zuwa ta haramta shan sigari a wuraren taruwar jama’a. Kasar ta ce wuraren da haramcin ya shafa sun hada da makarantu da tashoshin mota ko na jirgi, wuraren shakatawa, wuraren wasanni ko kasuwanni saboda kada yara kanana su gani. Yadda ambaliyar Neja ta ci...
Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman mafaka ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 30, ciki har da yara da dama, a cewar jami’an kiwon lafiya da na fararen hula. Da sanyin safiyar yau litinin ne sojojin gwamnatin...
Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa. Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa. ‘Yan mata suna cikin hadari,...
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga hukumomin gwamnati da shugabannin makarantu da su ba da fifiko wajen kula da duk wasu gine-ginen makarantu da aka gyara domin kiyaye abubuwan da kuma tabbatar da ci gaban fannin ilimi. Gwamna Dauda Lawal ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da sabuwar makarantar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta cafke wasu maza biyu bisa zargin yi wa ƙananan yara mata fyaɗe a lokuta daban-daban a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sun kama wani mutum mai shekara 47, da zargin yi wa ‘yar matarsa mai shekara biyu fyaɗe...
Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba. Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu. ...
Ya ƙara da cewa Ganduje mutum ne da kullum yana cikin yi wa ma’aikatansa fara’a. Ya ce masu yaɗa bidiyon na ƙoƙarin tada rikici ne domin dalilan siyasa. “Wannan ba zai rage farin jinin Ganduje ba,” in ji shi. “Ya yi wa Jihar Kano aiki tuƙuru, yanzu kuma yana yi wa ƙasa. ‘Yan adawa ba...
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa: Gaza na gaf da afkawa cikin babbar masifa saboda zaluncin ‘yan mamayar Isra’ila A yayin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da killace Zirin Gaza sama da watanni biyu, abubuwan da ke faruwa a kowace rana, abubuwa ne da suke yadda bala’i ke shafar kowane gida, kowane...
Ilimi na da muhimmanci wajen gina al’umma, amma ga daliban Makarantar Firamare ta Bare a karamar Hukumar billiri, Jihar Gombe, wannan lamari ya zama kamar mafarki mai wahalar tabbatuwa. Duk da ikirarin da Gwamnatin Jihar Gombe ke yi na cewa, tana fifita ilimi ta hanyar manyan ayyuka kamar gine-ginen makarantu masu hawa biyu a kowace...
Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin...
Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa kimani yara 3,500 suka rasa rayukansu a kokarin ketara tekun Medeteranina a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Spunic na kasar Rasha ya nakalto hukumar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar dangane da hakan. Labarin ya kara...
Ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta bayyana ayyana dokar ta-ɓaci a harkar ilimi, kuma ta kashe biliyoyin Naira wajen gyara da sabunta makarantun kwana, inda ta ce “nan ba da jimawa ba za a sake buɗe su don yara mata su ci gaba da samun ilimi.” Ta kuma ƙara da cewa wasu daga cikin makarantun...
Wasu kafofin yada labarai a duniya na ganin cewa, idan gwamnatin Amurka ta ci gaba da saka shingayen haraji, to sauran kasashe za su maye gurbinta a bangaren samar da hidimomi. Abin da gwamnatin ta yi biris da shi yayin da take kididdigar harajin da za ta kakabawa sauran sassa, har yanzu wannan bangare na...
Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motocin kamfanin sufurin Borno Express na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane 18 kowacce. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Litinin, bayan wani fashewa mai ƙarfi a harabar garejin....
An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP). Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito,...
Wani sabon rahoto da hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar a Nijeriya, na ishara da cewa mutum miliyan 11 ne a fadin jihohi shida na Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Nijeriya ke fuskantar matsalar karancin abinci a shekarar 2025. Kazalika, rahoton ya danganta matsalar da rashin tsaro da ake ci...
Sai dai, tabbas za a karya tsarin, ganin yadda ba a samun adalci a ciki. Mun san kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka warware dabaibayin hana ci gaba da kasashen yamma suka daura musu, inda ta raya tattalin arzikinta, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin duniya ta fuskar samar da...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba a kan kananan yara. “Ba mu da wani bayani a tarihin wannan zamani dangane da ke bukatar tallafin lafiyar kwakwalwa kamar yaran Gaza,” in ji mai magana...
Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan. Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis. Sanƙarau...