Gwamnatin Kaduna Za Ta Mayarda Yara 200,000 Zuwa Makaranta
Published: 2nd, June 2025 GMT
A wani yunkuri na rage adadin yara da suka daina zuwa makaranta, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da shiri mayarda yara 200,000 zuwa makaranta a cikin shekaru hudu masu zuwa, karkashin shirin Reaching Out-of-School Children (ROOSC).
An bayyana wannan shiri ne a wani taron bita na kwanaki biyu da aka shirya tare da haɗin gwiwar Save the Children.
A cewar, wakilin Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Salisu Baba Lawal shirin zai shafi dukkan ƙananan hukumomi 23 a faɗin jihar.
“Wannan shiri na Gwamnatin Jihar Kaduna ne tare da haɗin gwiwar abokan ci gaba da masu aiwatar da ayyuka,” in ji shi.
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta samo lamunin tallafin kudi domin aiwatar da wannan shiri da nufin maganin matsalar yara da suka bar makaranta a faɗin jihar,” ya ƙara da cewa.
“Zuwo yanzu, an riga an horar da malamai 405, an gina sabbin makarantu 102, sannan ana ci gaba da gyara wasu makarantu 170.
Shirin yana ƙarfafa rajistar yara a makaranta da inganta koyarwa da samar da ingantaccen yanayi na koyo da koyarwa.”
Save the Children International da UNICEF su ne manyan abokan hulɗar wannan shiri, kuma yana samun goyon bayan kai tsaye daga Gwamna Uba Sani.
Save the Children ta raba kayan aiki da horar da malamai a karkashin shirin Reaching Out-of-School Children na Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Ma’aikatar Ilimi.
Shirin ROOSC yana mai da hankali kan ɗorewa, daidaito tsakanin jinsi, da kuma tallafawa marasa galihu, domin tabbatar da damar samun ingantacciyar ilimin firamare ga yara, matasa, da samari a fadin Jihar Kaduna.
Save the Children da UNICEF sun samu wakilci daga gwamnatin jihar ta hannun Ma’aikatar Ilimi don inganta tsarin koyarwa (Save the Children) da kuma ƙarfafa tsarin ilimi gaba ɗaya (UNICEF).
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamnatin Makaranta Mayarda yara Zuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.