HausaTv:
2025-11-03@17:56:04 GMT

Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza

Published: 3rd, November 2025 GMT

Turkiyye na karbar bakuncin wani taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi kan halin da ake ciki a Gaza.

Wannan taron ya zo ne bayan makonni uku da fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

A cewar Turkiyya, manufar taron ita ce taimakawa wajen mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sake tabbatar da rawar da take takawa a wannan batu.

Ƙasashen musulmin dake halartar taron na yau Litini a Istanbul su ne wadanda Donald Trump ya aminta dasu don tabbatar da nasarar shirin zaman lafiya na Gaza.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyye Hakan Fidan, wanda ke karbar bakuncin takwarorinsa, ya gabatar da wannan taron a matsayin hanyar yin nazari kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, samar da matakai na gaba, da kuma daidaita su kafin tattaunawa da kasashen Yamma.

Haka kuma hanya ce ga wadannan kasashen da suka fi yawan al’ummar Musulmi su nuna jajircewarsu wajen kiyaye yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ya bayyana tsagaita wuta a matsayin mafi rauni idan aka yi la’akari da kalubalen da mataki na biyu na shirin ke fuskanta.

Mataki na biyu na shirin na Trump ya tanadi kwance damarar makamai na kungiyar Hamas, samar da rundunar sulhu, da sauransu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza November 3, 2025 Girgizar kasa ta yi ajalin gomman mutane a Afghanistan November 3, 2025 Najeriya : tun kafin kalamman Trump muka dauki matakai November 3, 2025 Sudan : Mutane 1,500 sun rasa matsugunansu sakamakon tashin hankali November 3, 2025 UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza November 3, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Zargin Da Amurka Tayi Mata Kan Batun Motocin Agaji A Gaza November 3, 2025 El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai November 3, 2025 Iran Ta Karbi Sako Kan Batun Komawa Teburin Tattaunawa Ba Kai Tsaye Ba November 3, 2025 Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan: Mayakan RSF Sun Kashe Mata 300 Da Yi Wa 25 Fyade A El Fasher November 3, 2025 Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yarjejeniyar tsagaita wuta

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza

Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya musanta zargin da y ace karce ce ” da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta yi cewa Hamas ta sace wata babbar mota dauke da kayan agaji.

“Mun tabbatar da cewa wannan zargin karya ne, kuma wani bangare ne na manufar kafofin watsa labarai da nufin bata sunan rundunar ‘yan sandan Falasdinu, wadanda ke aikinsu na kasa da na jin kai na neman taimako da kare ayarin motocin agaji,” in ji Ismail Al-Thawabta, darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza.

Yakara da cewa ba a fayyace ainihin rana, lokaci, da wurin da lamarin ya faru ba, Al-Thawabta ya bayyana bidiyon a matsayin “yunkuri bayyananne na yada bayanai marasa tushe.”

Sanarwar ta karyata ikirarin CENTCOM cewa “kusan kasashe 40 da kungiyoyin kasa da kasa suna aiki a Gaza,” yana mai jaddada cewa ainihin adadin kungiyoyin da ke ba da agajin jin kai bai wuce 22 ba, “yawancinsu suna fama da cikas da kuntatawa saboda matakan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sanya.”

Haka kuma ta soki shiru da CENTCOM ta yi game da laifuka da cin zarafi da Isra’ila ke yi a kullum tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.

“Shirun da rundunar sojin Amurka ta yi a gaban wadannan laifukan na yau da kullum, yayin da take aiki don yada labaran da ba su da tushe game da rundunar ‘yan sandan Falasdinu, ya nuna cikakken son kai ga mamayar Isra’ila da kuma rashin sahihancinta a matsayin wacce ya kamata ta kasance mai shiga tsakani,” in ji sanarwar.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza
  • UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza
  • El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta