2025-08-10@12:32:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1483
«Babachir Lawal»:
dimokuradiyya ta hanyar ba da umarni ga manyan wadanda ya nada na arewa su halarci taron. “Wannan aiki daya na sadaukarwar da shugaban kasa ya yi don tattaunawa da mutane Yana ishara da cewa, ba wai isa ce kadai a kan iya siyasa ba har ma da isa matuka wajen mutunta ka’idojin dimokuradiyya....
Ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya soki hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, kan wallafa sakon alhinin mutuwar ɗan wasan Falasɗinawa da ya rasu ba tare da ba da cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa ba. A ranar Alhamis aka kashe Suleiman al-Obeid, wanda aka fi sani da Pelen Falasɗinawa – a...
Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon saukar agajin da aka kai a zirin Gaza ya kai Falasdinawa 23 tare da jikkata wasu 124 Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon saukar da agaji ta hanyar jiragen sama tun bayan fara yakin kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan zirin Gaza ya...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa a wannan Lahadin domin tattauna ƙudirin Isra’ila na ƙwace iko da Zirin Gaza. Wannan shirin, wanda Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da shi a ranar Juma’a, ya jawo suka daga ƙasashen duniya. Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a...
Jaridar Tehran Times, ta nakalto cewa, Iran da Amurka a shirye suke su fara wata sabuwar tattaunawa. Majiyoyin sun ce tattaunawar za ta kasance ba kai tsaye ba, sanann kuma ana sa ran cewa kasar Norway ce za ta kasance mai shiga tsakanin bangarorin biyu. Jaridar ta kasar Iran ta yi nuni da cewa “Tehran...
Dubban mazauna birnin Tel Aviv ne suka taru a tsakiyar birnin a daren jiya Asabar, domin neman kawo karshen yakin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da shirin kara kai hare-hare da kuma mamaye birnin Gaza. Masu zanga-zangar dai na dauke da allula da kuma hotunan wadanda ake tsare da...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar. Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya yabawa yan jarida musamman a khidimar da suka gabatar a yakin kwanaki 12. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a lokacinda ya kai ziyarar ganin ido a cibiyar hukumar gidajen radiyo da talabijin na JMI a nan birnin Tehran....
Yansanda a kasar Burtaniya ta kama mutane fiye da 200 wadanda suka fito zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin London. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai a birnin London na cewa mutane kimani 600-700 ne suka fito suka kuma tsaya a wani wuri kusa da majalisar dokokin kasar wanda...
Yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna damuwa game da yadda majalisar dattawa ta 10 ke gudanar da harkokin majalisa, suna cewa ‘yan majalisar sun gaza bayar da muhimman ayyukan da aka ɗora musu na binciken ɓangaren zartarwa don kare ‘yan Nijeriya. Ana zargin majalisa dattawa ta 10 da ƙin tilasta wa gwamnatin tarayya wurin magance tarin...
Gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da sulhuntawa da kasashen Armedia da Azarbaijan a fadar white House, amma ta yi gargadin shishigin kasashen waje a yankin Caucasus, da ke makobtaka da Iran. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta ta nakalto wani bayani wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a yau Asabar na...
Falasdinwa 11 suka rasa rayukansu a yau Asabar a Gaza saboda yunwa, wanda ya kawo adadin wadanda yunwa ta kasashe a Gaza tun lokacinda HKI ta hana shigowar abinci yankin zuwa 212. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar ma’aikatar kiwon lafiya na Gaza na fadar haka, sannan masana sun bayyana cewa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani. Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Shirin gwamnatin mamayar Isra’ila shi ne shirin share al’umma Falasdinu daga kan doron kasa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Shirye-shiryen da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take yi na mamaye yankin Zirin Gaza da kuma tilastawa al’ummar yankin gudun hijira wani karin shaida ne...
Fitattun matsayi na kasashen Larabawa da kungiyoyi sun yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da matakin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Kasashe da kungiyoyin Larabawa sun yi Allah wadai da matakin da majalisar ministocin gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka mai hatsari na sake mamaye yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kusan...
Rinsola Babajide, Ajibola Abiodun. ‘Yan Wasan Tsakiya Ibrahim Ayinde, Asisat Oshoala, Chinwendu Ihezuo, Christy Ucheibe, Onyi Echegini, ‘Yan Wasan Gaba Chioma Okafor, Toni Payne, Rasheedat Ajibade, Florence Ijamilusi, Esther Okoronkwo Ifeoma Onumonu, Hakazalika a wani taron liyafa da shugaba Tinubu ya karɓa, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayar da lambar...
A gobe Lahadi ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani zaman gaggawa kan halin da ake ciki a zirin Gaza, kamar yadda wakilin Al-Mayadeen a birnin New York ya bayyana. Wannan shawarar ta zo ne bayan amincewar majalisar ministocin Isra’ila da shirin firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya hada...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince ta bada sama da naira miliyan 156 domin sayen tikitin jirgi na mayar da daliban jihar masu karatun likita har su 184 da suka kammala hutun su a gida zuwa makaranta a kasar Cyprus. Shugaban Hukumar Bada Tallafin Karatu ta Jihar, Alhaji Saidu Magaji, ya bayyana hakan ga manema labarai...
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki...
Ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Aragchi ya rubutawa babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC Hussain Ibrahim Taha, da kuma tokwarorinsa na kasashen Saudiya da Turkiya, Faisal bin Farhan da kuma Hakan Fidan wasiku dangane da bukatar kasashen kungiyar su gudanar da taron gaggawa kan abinda ke faruwa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke...
Kudirin gyaran dokar fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa. Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji...
Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza. Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da...
Falasdinawa masu yawa ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin ‘yan sahayoniyya suka kai kan tantuna da gidaje da ‘yan gudun hijira a Gaza Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu masu yawa da sanyin safiyar yau Alhamis a wasu munanan hare-hare da jiragen yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana bukatar samar da wata sabuwar hanyar yin mu’amala da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, inda ya bayyana cewa, ba a kayyade lokacin shiga wasu shawarwari da Amurka ba, ya kuma tabo batun muhimmancin dangantakar dake tsakanin Iran da kasashen Rasha, Sin...
Ofishin jakadancin kasar Sin a Birtaniya, ya yi tir da kausasan kalamai kan rahotannin dake cewa tsohon firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ziyarci yankin Taiwan na Sin da kiran da ya yi wa kasashen yamma su kulla huldar tattalin arziki da yankin. Wani kakakin ofishin jakadancin ya bayyana a jiya cewa, suna adawa matuka da...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da kyautar fuloti da kuɗi naira miliyan biyar ga kowane ɗaya daga cikin iyalan tawagar ’yan wasan nan na Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a watan Yuni. Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya tabbatar da...
Fararen hula 14 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai El Fasher na Sudan Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Sudan ta sanar da cewa: kungiyar Rapid Support Forces ta kasar Sudan ta Dakarun kai daukin gaggawa ta kashe akalla fararen...
Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan. Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira wani zama na gaggawa a jiya Talata, domin tattauna mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza, inda ya mayar da hankali musamman kan fursunonin Isra’ila da ke hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinu. A tsakiyar zaman dai batutuwa biyu ne suka dauki hankali: daya daga kasashen yammacin turai...
Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala...
Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko. A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na...
Dakarun sojin Nijeriya sun hallaka aƙalla ’yan ta’adda 17 na ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a wasu hare-haren kwantan bauna da suka kai a jihohin Borno da Adamawa a tsakanin ranakun 23 ga Yuli zuwa 2 ga Agustan 2025. Kyaftin Reuben Kovangiya, Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, ne ya bayyana hakan...
Wasu zauna gari banza sun burma wa wani jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) wuka har lahira a Kasuwar Shuwarin da ke ci Karamar Hukumar Kyawa a Jihar Jigawa. Kakakin Hukumar NSCDC reshen Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani, ya bayyana cewa an kai wa jami’in hari ne a lokacin da yake bakin aiki a ranar...
Hukumar Yaki da Hamada da Sauyin Yanayi ta Kasa ta kammala shirye-shiryen dasa itatuwan dabino miliyan hamsin (50,000,000) a jihohi goma sha ɗaya 11 da ke fama da fari a Najeriya. Daraktan Hukumar, Alhaji Salihu Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin dasa itatuwan dabinon da aka gudanar a Dutse, babban birnin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin ‘yan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin yahudawan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa. A lokacin da yake halartar taron manema labarai da kakakin...
Mashawarcin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Za su koma shawarwari da Amurka ne yayin da suke dauke da makamai a hannu Mai baiwa ministan harkokin wajen Iran shawara Sa’ed Khatibzadeh, ya jaddada cewa: Iran ba za ta sake amincewa da Amurka kan duk wata tattaunawa da za ta iya yi ba, yana mai...
Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin...
Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe. Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa...
Shugaban kasar Lebanon Josepth Aoun ya yi alkawalin adalci ga iyalan wadanda fashewar tashar jiragen ruwa na Beirut ya sha bayan shekaru 5 da aukuwar hakan. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau litinin. Ya ce har yanzun ba wanda aka kama ko ake tuhuma da haddasa...
Rahotanni daga Gaza na cewa sojojin Isra’ila sun sake buɗe wuta kan Falasɗinawa da ke cikin tsananin buƙatar agaji a kusa da inda ake rabon kayan tallafi a cibiyoyi biyu, a jiya Lahadi. Asibitoci a Gaza sun ce aƙalla Falasdinawa 27 aka kashe. Rahotanni na cewa sojojin sun buɗe wa mutane wuta bayan isa gab...
Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi. An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano. Kano tana da gidan...
Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi. An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano. Kano tana da gidan...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada kudirin ta na kare al’umma daga ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasa ta yi hasashen samu a wasu kananan hukumomin jihar a daminar bana. Mataimakin Shugaban kwamitin fasaha kan magance ambaliya, kuma mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ambaliya da kuma sauyin yanayi, Alhaji...
Rahotonni sun bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila ta ki bari an gano kashi 88% na irin laifukan da ta aikata a yakin Gaza ba Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta bayyana cewa: Hukumomin mamayar Isra’ila sun boye kusan kashi 88% na binciken laifukan yaki ko cin zarafin da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata...
A kokarin da Gwamnatin Jihar Jigawa ke yi na kara habbaka harkokin noma, shirin ACRESAL yace sami amincewar gwamnatin na siyo injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana guda 3,000 domin tallafawa manoma. Shugaban Shirin na Jihar, Malam Yahaya Kafin Gana ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. Yana mai cewar, samar da...
Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban. Kazalika, ya...
Sojojin HKI sun kashe falasdinawa 62 daga safiyar jiya Asabar zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Lahadi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa mafi yawan wadanda aka kashen masu neman abainci ne, a cibiyoyin karban abincin wadanda HKI da Amurka suka kafa. Kafafen yada labarai daga asbitocin Gaza sun bayyana...
Magana ta gaskiya matsala daya ce zuwa biyu ko uku, na farko akwai laifin iyaye, na biyu akwai laifin samari da suke zuwa su yi auren, na uku kuma akwai laifin amaryar wacce ita ce take zaman auren. Bari na fara da maganar farko, dalilin da ya sa na ce laifin iyaye ne shi ne;...