Burkina Faso: Masu Ikirarin Jihadi Sun Kashe Fararen Hula 50 A Cikin Watanni Hudu
Published: 15th, September 2025 GMT
Hukumar kare hakkin bil’adama ta “Human Right Watch” ta fitar da wani rahoto da a cikin ta bayyana cewa; kungiyar nan mai ikirarin jihadi a kasar Burkina Faso, ( Jama’at Nusratul-Islam wal Muslimin) da kuma kungiyar Daular Musulunci a cikin yankin Sahara, sun kashe fararen hula 50 daga watan Mayu zuwa yanzu.
Rahoton ya ci gaba da yin bayanin cewa, a cikin Ogusta kungiyoyin na masu riya cewa suna yin jihadi sun kashe mutane 40 a cikin garuruwan Djibo da Youba.
Rahoton ya kuma ce; a watan Yuli kuwa kungiyar IS ta kai wa fararen hula hari da suke kan hanyar kai kayan agaji zuwa garin Gorom-Gorom da aka killace da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9.
Kungiyar kare hakkin bil’adama din ta ce, wadannan irin hare-haren sun sabawa dokokin kasa da kasa na jin kai, kuma suna a matsayin laifukan yaki.
Kungiyar kare hakkin bil’adaman ta “Human Right Watch” ta mika sakamakon binciken da ta gabatar ga hukumomin tsaro da na shari’a na kasar ta Burkina Faso. Sai dai har yanzu babu wani martani da ta samu.
Shekaru 3 kenan da kasar ta Burkan Faso take a karkashin mulkin soja da su ka sha alwashin kawo karshen masu tayar da kayar baya da sunan jihadi.
Tun daga 2016 ne kungiyoyin dake dauke da makamai suke kai hare-hare a sassa mabanbanta na kasar ta Burkina Faso da sunan jihadi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha September 15, 2025 Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China September 15, 2025 Fizishkiyan: Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI September 15, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci Daga Yanzu
A wani rahoto da miami herald ya wallafa a jiya jumaa ya nuna cewa kasar Amurka na shirin kaiwa kasar Venuzuwela hare hare, yayin da Donald trump shugaban kasar Amurka yake musantawa cewa babu wani shiri na daukar matakin soji a kasar ta latin Amurka.
Yace gwamnatin trump ta yanke shawarar kai hari kan wasu wuraren soji a kasar, a kowanne lokaci.
Yace duk da yakin da washington ke yi kan miyagun kwayoyoi gwamnatinsa ba ta la’akari da kai hare-haren sojin kan venuzuwela yana nuna a akwai karo da juna a kalamansa na makon da ya gabata
Da manema labarai suka tambayeshi ko hare-haren da Amurka takai a yan kwanakin nan kan jiragen ruwa a yankin karebiya da aka ce suna fataucin miyagun kwayoyi na iya sanyawa akai hare hare kan venuzuwela trumpa ya amsa da cewa A’a.
A yan makwannin nan da suka gabata Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kai hari kan wuraren da suke da alaka da miyagun kwayoyi acikin venuzuwela yana mai cewa kasar za ta zama it ace ta gaba da za su daukai mataki a kanta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci