’Yan Najeriya da tauraronsu ya haska a Ballon d’Or
Published: 26th, September 2025 GMT
A ranar Litinin aka gudanar da bikin bayar da kyautar Ballon d’Or a Birnin Paris, inda ake karrama fitattun ’yan ƙwallon duniya.
A bana, Ousmane Dembele na Ƙasar Faransa da PSG ne, ya lashe kyautar maza, yayin da Aitana Bonmati ta Spaniya ta lashe ta mata karo na uku a jere.
An gano yarinya da aka sayar ₦3.7m a Ondo Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan
Abin farin ciki ga Najeriya shi ne, mai tsaron ragar Super Falcons, Chiamaka Nnadozie, ta zo ta huɗu a jerin mata, wanda shi ne matsayi mafi girma da wata ’yar Najeriya ta taɓa samu.
Ga jerin ’yan Najeriya da suka taɓa shiga cikin jerin waɗanda suka fafata neman kyautar Ballon d’Or:
Finidi George — 1995Ya taka leda a Ajax inda ya taimaka wajen lashe gasar Champions League. Ya zo na 21 a duniya.
Nwankwo Kanu — 1996 da 1999Ya taimaka wa Najeriya ta lashe Olympics a Atlanta 1996, sannan ya taka rawa a Inter Milan da Arsenal. Ya zo na 11 a 1996 da na 23 a 1999.
Victor Ikpeba — 1997“Prince of Monaco” ya taimaka wa Monaco wajen lashe gasar Ligue 1. Ya zo na 32.
Asisat Oshoala — 2022 da 2023Ita ce mace ta farko daga Najeriya da ta shiga jerin neman kyautar Ballon d’Or. Ta zo na 16 a 2022, sannan ta zo na 20 a 2023.
Victor Osimhen — 2023Ya jagoranci Napoli wajen lashe gasar Serie A bayan shekara 33. Ya zo na 8, sannan ya lashe gwarzon ɗan ƙwallon Afirka.
Ademola Lookman — 2024Tauraronsa ya haska Atalanta, inda ya taimaka mata wajen lashe gasar Europa League, ya kuma zura ƙwallaye a Gasar Afirka. Ya zo na 14.
Chiamaka Nnadozie — 2025Ta zo na 4 a cikin masu tsaron raga mata, abin alfahari ga Najeriya. Ta kuma lashe gasar Kofin Afirka sau biyu (2018 da 2024).
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Ƙwallo Najeriya wajen lashe gasar
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya
Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya.
Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA