HausaTv:
2025-10-13@15:47:23 GMT

Magajin Garin Landan Ya Yi Dirar Mikiya Kan Shugaban Kasar Amurka Donald Trump

Published: 26th, September 2025 GMT

Magajin garin Landan ya caccaki shugaban Amurka Trump, yana mai cewa shi mai nuna wariyar al’umma ce tare da kyamar musulmi

Magajin garin Landan Sadiq Khan ya bayyana shugaban Amurka Donald Trump a matsayin “mai nuna wariyar al’umma kuma mai kyamar musulmi,” bayan da Trump ya zarge shi da neman aiwatar da shari’ar Musulunci a babban birnin Birtaniya.

Khan ya shaida wa tashar Sky News cewa: “Yana ganin Trump a matsayin mai nuna wariyar al’umma, mai dabi’ar bunsuro, mai son zuciya, kuma mai kyamar musulmi.”

Ya yi nuni da cewa, Landan ce ta farko a cikin alamomi da dama, kamar zuba hannun jari na kasashen waje, ya kuma jaddada cewa “yana matukar alfahari da cewa Landan ce birni mafi girma a duniya.”

A jawabin da ya yi a taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, Trump ya ce: “Ya kalli Landan, inda take da magajin gari da bai dace ba, ya canza ta, ya canza ta da yawa,” ya kara da cewa: “Yanzu kuma yana son aiwatar da shari’ar Musulunci a cikinta.”

Khan wanda musulmi ne ya rike mukamin magajin garin Landan tun shekara ta 2016. A waccan shekarar, ya caccaki dan takarar shugaban kasa na lokacin Trump kan kudirinsa na hana ‘yan kasashen da mafi rinjaye musulmi shiga Amurka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Yemen Sun Kai Wani Gagarumin Hari Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila September 26, 2025 Iran ta yi Allah wadai da yunkurin E3 na neman sake dawo mata da takunkumi September 26, 2025 Maduro jaddada hadin kai tsakanin al’ummomin Venezuela da Colombia September 26, 2025 UNRWA: Halin da ake ciki a Gaza ya yi muni matuka September 26, 2025 Sojojin Yaman: Mun kai hari kan sojojin mamaya a Jaffa September 26, 2025 Iran Ta Yi Tir Da ‘Hannun Diblomasiyya’ Na Trump Bayan Farmata Da Yaki September 25, 2025 Pezeshiyan: Babu Amfanin Tattaunawa Idan An Maida Takunkuman Tattalin Arziki A Kan Iran September 25, 2025 Iran Ta Nuna Bayanan Sirri Na Cibiyoyin Nukiliyar HKI September 25, 2025 Kasashen Duniya Suna Yin Gargadin Cewa HKI Za Ta Kai Wa Jiragen Ruwan Ceto Na “Sumdu” Hari September 25, 2025   September 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine

Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da ta danganta da na karya da Amurka ke yi wa kasar cewa ta na da hannu a yakin da ake yi a Ukraine, tana mai daukar wadannan zarge-zarge a matsayin wani makirci na siyasa da nuna kiyayya.

A cewar ma’aikatar harkokin wajen Cuba, hukumomi “ba su da wani takamaiman bayani kan ‘yan kasar Cuba” da suka shiga ko kuma suke shiga cikin rikicin “da kansu” a cikin “dakarun sojan bangarorin biyu da ke rikici da juna” tsakanin Rasha da Ukraine.

Tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, kotunan kasar Cuba sun saurari kararrakin laifuka tara da suka shafi ayyukan sojan haya, inda suka yanke wa wadanda ake tuhuma 26 hukuncin zaman gidan yari tsakanin shekaru 5 zuwa 14.

Cuba ta kuma fayyace cewa duk wani daukar aiki na ‘yan kasar Cuba don shiga yakin kasashen waje, kungiyoyin waje ne ke aiwatar da su, wanda bai da alaka da gwamnatin Cuba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter  A Kasar Habasha October 12, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta October 12, 2025 An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan October 12, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa October 12, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Yunkurin Balair Na Yiyuwar Shiga Gwamnatin Gaza. October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh
  • Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk
  • ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar
  • Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine
  • Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh
  • China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100%
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta
  • Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa
  • Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya
  • Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta