Kwamitin gwamnati ya ba da shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13 a Bauchi
Published: 6th, October 2025 GMT
Kwamitin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa domin nazarin buƙatun ƙirƙirar sababbin masarautu da yankunan hakimai da dagattai, ya ba da shawarar ƙirƙirar masarautu 13, da hakimai 2 da dagattai 113 a fadin jihar.
Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton da shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya miƙa wa Gwamna Bala Mohammed a ofishinsa da ke Bauchi.
Da yake miƙa rahoton, Akuyam ya bayyana cewa masarautu 13 da yankunan hakimai biyu da aka bayar da shawarar kafa su su ne suka cancanta daga cikin sama da buƙatu 100 da aka karɓa daga sassan jihar daban-daban.
Kwamitin, an kaddamar da shi ne a ranar 4 ga Yuli 2025, da umarnin ya duba buƙatun al’ummomi, ya tantance dalilan tarihi, al’ada da tsarin mulki, sannan ya bayar da shawarwari da za su taimaka wajen tabbatar da adalci haɗin kai da zaman lafiya a jihar.
Shugaban kwamitin ya bayyana cewa, kwamitin ya karɓi jimillar takardun neman masarautu 196, inda 17 suka nemi ƙirƙirar masarautu, 166 suka nemi hakimai, sauran kuma suka nemi dagattai.
Zargin takardun bogi: Jami’ar Nsukka ba ta taɓa ba ni takardar digiri ba — Minista Tinubu ya fi damuwa da siyasa sama da rayukan ’yan Najeriya — ADCYa ce, “A ƙarshe, kwamitin yana ba da shawarar ƙirƙirar masarautu 13, sarautu 2, da yankuna 111 a faɗin Jihar Bauchi.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sababbin masarautu masarautu 13 da shawarar
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Sandan Jihar Neja Sun Tabbatar Da Masu Sa-kai Kan Sahihiyar Kariya.
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar wa al’ummar jihar a shirye ta ke ta ci gaba da kare mutuncin daidaikun mutane da kungiyoyin da suka sadaukar da kansu domin samar musu da sahihin bayanan sirri da za su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijar.
‘Yan sanda a jihar Neja da ma Nijeriya ƙwararru ne don haka za su ci gaba da aiki da kuma nuna basira da ƙwarewa tare da ƙa’idarta ta sirrin rashin bayyana tushen bayanansu don samun sakamako mafi girma.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman wanda ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, ya bayyana cewa a kwanan baya ya halarci wani taron bita da hedkwatar ‘yan sanda ta shirya kan masu bada bayanai wato Informant domin kara kwarewarsa.
Sai dai Adamu Abdullahi Elleman ya danganta raguwar ayyukan aikata laifuka a Minna babban birnin jihar da sahihan bayanai da aka samu daga jama’a, goyon baya daga babban sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun da gwamnatin jihar Neja a karkashin jagorancin Gwamna Umar Bago, da sarakunan gargajiya da kuma matakin da ya dauka na cewa a mafi yawan lokuta yakan shiga sintiri a Minna, wanda DPO da kwamandojin yankin suka goyi bayansa.
A cewarsa sakamakon wannan yunkurin da aka yi da dama daga cikin miyagu da suka tsunduma cikin ayyukan ‘yan daba, an kama su, an kuma gurfanar da su a gaban kuliya, tare da daure su a matsayin misali ga wasu.
Adamu Abdullahi Elleman ya ci gaba da cewa, ya kuma gargadi Hakimai na yankin da su rika taimaka wa miyagu cewa duk wanda aka kama za a gurfanar da shi a gaban kuliya manta sabo.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, ya kuma yabawa babbar mai shari’a ta jihar, Mai shari’a Halima Ibrahim bisa goyon bayan da ta bayar wajen ganin an samar da shari’a cikin gaggawa, tare da samun hadin kai tsakanin ‘yan sanda da sauran kungiyoyin tsaro baya ga sabon alkawari da jami’an sa da mazaje suke yi na yakar miyagun laifuka da aikata laifuka a duk lungu da sako na jihar.
Adamu Abdullahi Elleman ya kuma kara da cewa a karkashin sa a matsayinsa na sabon kwamishinan ‘yan sanda mai kula da jihar Neja, jin dadin jami’ansa da jami’an rundunarsa shi ne babban abin da ya fi ba da fifiko wajen kara musu kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyuka masu inganci.
INT Aliyu Lawal.