Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
Published: 18th, September 2025 GMT
A ƙoƙarinta na ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa.
Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace gunduma ta yankin
A cewarsa, manufar horon ita ce koyar da mahalarta yadda za su samar da kariya yayin al’ada da kansu domin rage kashe kuɗi da kuma kare kansu daga kamuwa da cututtukan mahaifa.
Shi ma shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Shehu Sani Gwadayi, ya bayyana cewa tsafta na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan adam domin inganta rayuwa da ƙarfafa garkuwar jiki.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Muhammad Abdullahi, ya yi wa mahalarta horon bayani kan muhimmancin tsafta yayin al’ada domin gujewa kamuwa da cututtuka.
Shugaban ƙaramar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun Gabas, ya shawarci mahalarta da su mai da hankali ga sashen aikace-aikace na yadda ake sarrafa audugar mata a gida yayin horon.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Kiwon Lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.
Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.
“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.
Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.
Gwamnan ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria