HausaTv:
2025-09-17@21:51:43 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a)

Published: 31st, August 2025 GMT

137- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi.

Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka fara yakin gama gari tsakanin sojojin Imam Ali (a) da kuma na Mu’awiya dan Abu sufyan. Bayan yaki mara nauyi na wani lokaci mai tsawo.. Mun ji yadda ya raba tutocin ga kwamandojin rundunarsa.

Sannan munji yadda a wani lokaci wasu sojojin mu’awiya sukan tunkari Imam Ali (a) suna son kashe shi, kai tsaye amma shi da kansa yake kashe su, sannan munji yadda yayansa Imam Alhassan da Alhussain (a) da kuma Muhammadul Hanafiyya suke tare da shi suna kare shi.

Sannan an yi wani lokacin da sojojinsa suka tarwatse a gabansa, sai Malik dan Ashtar ya ji tsoron kada a kashe shi, sai yayi sauri ya zo masa, sai da ya karaso, y ace masa ya je ya kira wadanda suka gudu, ya fada masu kan cewa mutuwar da suke gudunta, zata riskesu ko da basu mutu a yau ba.

Malik ya je ya isar da sakon Imam (a) ya kuma sake tattarasu, ya basu tada kumajinsu suka sake farwa sojojin makiya . har sai da suka dangana da haimar Mu’awiya dan Abusufyan. Har kuma ya fara shirye-shiryen gudu.

Sannan daga karshen a lokacinda kawukan mutanen da dama suka fadi a siffin, kasa ta jike da jinin mutane muminai da azzalumai. Sai Ammar dan Yasir All..ya yardadashi, ya fada cikin tunani, inda ya tuna da Alkawalin shahada wanda manzon All..(s) yayi masa, kan cewa, Ya Ammar wata kungiya a zzaluma zata kashe ka, a wani hadisin ya kara da cewa, Ammar yana kiransu zuwa Aljanna, su kuma suna kiransa ga wuta.

Sai ya ga cewa shekarunsa sun kusan 90 a duniya, don haka ya fara tunanin cewa, me yake jira, yana son haduwa da wadanda suka rikashi da Imani, yana shaukin haduwa da Ubangijinsa. Sannan ya lura da tutocin da ke siffin ya ga cewa sun yi kama da tutocin manzon All..(s) a badar da Uhud da Hunanin. Sannan a dayan bangaren kuma tutocinsu sun yi kama da mushrikai da kuma Ahzaba.

Sai Amma ya tabbatar da cewa irin wannan ranar ce manzon All..(s) yayi masa Alkawali zai yi shahada.

Sai yana cewa zan yi shahada ina yakar makiyan All…da manzonsa (s), sannan gaban waliyin All..Wsiyyin manzonsa (s) a bayansa.. Ya tuna da iyayensa Yasir da Sumayya, da yadda mushrikai suka azabtar da su, suka sha azaba har suka yi shahada.

Sannan ya tuna da cewa yana tsohonsa, yadda khalifa na uku ya yayi shi, har ya kusan ya kashe shi. Ya sha dukkan wannan azabtarwa saboda ikidarsa. Daga nan sai ya fara shaukin shahada a wannan yakin. Sai fara munajati da Ubangijinsa yana cewa

(Ya uabangiji ka san cewa ni, da na san yardarka shi ne an sanya kaifin takobi na a kirgina har ya bulla ta baya na da na yi haka, da na san cewa yardarka tana cikin in jefa kaina cikin wannan kogin (furat) in mutu) da na yi hakan, da na san yardarka tana cikin in jefa kaina daga kan dutse in kashe kaina da na yi haka, (Ya Ubangiji) ni ban san wani aiki na samun yardarka, wanda yafi yakar wadannan azzalumai ba. Da kuma na san akwai wani aiki wanda ya fi wannan da na yi)).

 Sannan yaji wajen Amirul muminin (a) hawayensa na kwarara kan kumatunsa, a lokacinda Imam Ali (a) ya ganshi sai ya tashi ya rungumeshi sannan ya kebe da shi,  Sai Ammar ya juya wajen Imam (a), y ace masa: Ya dan’uwan manzon All..(s) shin kayi mani zini in shiga yaki ne.? Sai Imam (a) ya ji tsoron kalamansa, saboda shi yana  kamar hannun damarsa ne da yake tashi da shi, sannan daya daga cikin kwamandojinsa ne a cikin sojojinsa.

Sai tunani ya sake dawo masa, sai ya yunkura zai tashi ya shiga yaki, sai kuma ya dawo yacewa Imam (a) shi ka yi mani izini a shiga yaki.

Sai Imam (a) yace: Ka saurari All..ya jikanka. Ya nanata neman izni wajen Imam (a) yana jinkita shi, sai yace, ina shaukin haduwa da Ubangijina, ina kuma son hadawa da yan uwa na wadanda suka rikani cikin Imani.

Daga karshe Imam (a) ya ga dole ne y aba shi amsa, kuma ya rabuda shi Kenan. Sai ya tashi ya rungumeshi, yana cewa: (Ya Aba-yakzann, All..ya saka maka, da alkhairi kan abinda kayi mani kuma kaiwa annabinka, ka kasnace dan uwa na gaskiya, da kuma aboki na gaskiya,) Sai ya fara kuka sannan ammar ya fara kuka da kukansa.

Sai yana cewa ya shugaban Mumiminai, ban bi k aba sai bisa basira, ni naji manzon All..(s) yana fada a ranar Hunain: Ya Ammar, fitina zata kasance a bayana na, Idan haka ya faru to ka kasance to bi Aliyu da tawagarsa, don lalle yana kan gaskiya kuma gaskiya na tare da shi, kuma zai yaki masu karya al-kawali da azzalumai a bayana, All..ya saka maka Ya Amirul muminina da mafi kyawun sakamako,. Hakika na isar, na sadar kuma nayi nasiha.

Sannan Ammar ya shiga fagen fama, muhajirun da Ansar suna binsa. Har suka shiga karkashin tutar Hashim dan Utbatu al-Mirhal. Ya ci gaba da yaki, yana farinciki yana kuma jiran wanda zai kashe shi.

An ji shi yana fada (Aljanna tana karkashin madaukaka, a zan hadu masoya Muhammad (s) da jama’arsa,.). Ana cikin wannan halin sai ga Abulghadiya ya zo ya kasheshi.

Hakika Amma ya yaki kuraishawa sun Mushrikai sannan ya yakesu suna fitinannu, Abulghadiya wanda ya kashe Ammar yana daga cikin wadanda suka yi bai’atul Ridwan a hudaibiyya, ya kasancewa idan zai shiga wajen Mu’awiya bayan yakin sai yace ‘Wanda ya kashe  Ammar yana kofa (yana sallama)” wato yana al-fakhari da hakan.

An ruwaito manzon All..(s) yana cewa: Da ace dukkan mutane a doron kasa sun taru sun kashe Ammar da sun shiga wuta).

Don haka a lokacinda labarin kissan Ammar ya watsu cikin musulmi gaba daya, sai muhajirun da Ansar da sauran mutane suna kuka suna ta saurin zuwa makwancinsa.

Amirul muminina (a) yana daga cikin wadanda suka zo suka tsaya a kan gawarsa, jike da jininsa, yana kukan rabuwa da Ammar. An ruwaitoshi yana cewa:

{Idan wani daga cikin musulmi, bai yi bakincikin kashe Ammar ba, bakin ciki bai shiga cikin zuciyarsa ba, da kuwa baya kan shiriya.

All..ya jikan Ammar ranar da ya musulunta, Kuma All…ya jikan Ammar ranar da aka kashe shi, kuma All..ya jikan Ammar a ranar da za\a tasheshi da ransa. Hakika ni na ga Amma a lokacinda ba za’a ambaci sahabban manzon All..(a) 4 face shi ne na hudun, ko 5 sai shi ne na 5 din.

Babu wani daga cikin sahabban Muhammad (s) da ke shakkar, cewa Aljanna ta wajaba ga Ammar ba a wuri ba daya ko biyu biyu ba, jin dadi ya tabbata ga Ammar}   

Sai Imamul Hassan (a) ya tsaya kusa da gawar ammar ® yana ambaton hadisan da ya ji kakansa manzon All..(a) ya fada dangane da Ammar dan yasir, : Lalle manzon All…(s) ya fadawa sahabbansa ku gina mani (Arisha) ko khaima, kamar khaimar musa, sannan ya ci gaba da karban tubali daga mutanensa, yana cewa: Ya Ubangiji! babu alkhairi sai Alkhairin Lahira, ka gafartawa, Ansar da muhajirun , sannan ya ci gaba da karban tubali daga Ammar yana cewa: Kaitunka ya dan Sumayya, rundunar azzalumai zasu kasashe ka.

A wani hadisin y ace: Kakana ya fada: Lalle Aljanna tana shaukin mutane 3, Aliyu da Ammar da Salman.

A lokacinda labarin mutuwar Amma ya yadu, mutanen sham sun rikici, saboda hadisin da suka ji wajen Amru dan Ass kan cewa, azzalumar kungiya ce zata kashe Ammar, sun fahinci cewa sune azzalumar kungiyar. Amma Amru dan Assi tare da wayonsa na shaitana, ya fada masu cewa , Ai Aliyu(a) wanda ya fito da shi , shi ya kashe shi, da haka kuma jahilan mutanen sham suka amince da wannan wayon. Wanda ko yaro karami zai fahinci cewa ba haka yake ba. .

Masu sauraro a na zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alakum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 136 August 31, 2025 Iran Ta Sami Nasarar A Kan Amurka A Gasar Volleyball Na Kasa Da Kasa August 31, 2025 Rasha Tace: Masu Son Yaki A Turai Suna Zangon Kasa Ga Kokarin Trump Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine August 31, 2025 AU Da WHO Zasu Hada Kai Don Yakar Cutar Kolera  A Nahiyar Afirka August 31, 2025 Almashat: Yemen Za Ta Dauki Fansar Jinin Shahidanta A Kan Sahyuniyawa August 31, 2025 Iran ta yi Allawadai da kisan jami’an gwamnatin Yemen da Isra’ila ta yi August 31, 2025 Yemen: Firayi Ministan da wasu ministoci sun yi shahada a wani harin Isra’ila August 31, 2025 Argentina: Lauyoyi sun bukaci a cafke Netanyahu a kan laifukan yaki August 31, 2025 Sudan: Hamedti ya yi rantsuwar shugabantar gwamnati mai kishiyantar gwamnatin kasar August 31, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Ba Za Su Kyale A Lalata Alakar Iran Da Armeniya Ba August 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: masu sauraro wadanda suka kashe Ammar

এছাড়াও পড়ুন:

Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 

“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.

 

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.

 

Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki