2025-10-16@14:59:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 360

«Gwamna Inuwa Yahaya»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka rattaba hannu tsakanin kasashen biyu a shekara ta 1979. Tashar talabijin ta NAN ta nakalto Eliyahu Dekel, tsohon shugaban hukumar leken asirin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma masani kan al’amuran Masar na cewa: Masar na cikin gaggawar shirin tunkarar rikicin soji, yana mai cewa “yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu a shekarar 1979 ta kasance cikin yanayi na rugujewa tun lokacin da...
    Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da tsohon Sojan sama (Air Vice Marshal) Ibrahim Umaru a matsayin sabon Kwamishinan tsaro na cikin gida a yayin taron majalisar zartarwa na 28 a fadar gwamnati. Tsohon hafsan Sojan saman, wanda ya yi ritaya, ya kasance Daraktan-Janar na sashin aiyuka na musamman a fadar gwamnatin jihar Kano kafin naɗin nasa. Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci Gwamnan Yusuf ya buƙaci sabon kwamishinan ya yi aiki da gaskiya, mutunci da himma wajen kare rayuka da dukiya a jihar, yana mai jaddada mahimmancin haɗin gwuiwa tsakanin hukumomin...
    Fira ministan gwamnatin rikon kwaryar Libiya ya bayyana cewa: Babu wata cibiyar tsaro a Libya sai dai cibiyoyi na yau da kullum da suka hada da sojoji da ‘yan sanda Abdul Hamid Dbeibah, shugaban gwamnatin rikon kwaryar gwamnatin hadin kan kasa, ya ce: “Babu wani wuri a kasar Libya, sai dai cibiyoyi na yau da kullum, ciki har da sojoji da ‘yan sanda,” Dbeibah, ya fadi haka ne biyo bayan al’amuran tsaro da suka faru a babban birnin kasar, Tripoli, a ranar litinin bayan kisan Abdul Ghani al-Kikli, wanda aka fi sani da “Ghaniwa,” kwamandan kungiyar da ake kira “Stability Support Apparatus”. Bayanin na Dbeibah ya zo ne a yayin wani taron tsaro da aka gudanar a makon da ya...
    Jiragen na sojojin HKI sun kai hari ne dai a yau Lahadi a kan hanyar da ta raba tsakanin garin Beit-Yahun da Bent-Jubail dake kudancin kasar. A garin Kafar-kalla ma wani jirgin saman marar matuki ya jefa bama-bamai masu sauti a kusa da wani gida da dama an rushe shi. Harin na sojojin HKI yana cikin ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon da take yi wanda ya wuce 2000 tun daga tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Nuwamba na 2024.  Bugu da kari HKI ta girke sojojinta a cikin wasu wurare 5 dake kan iyaka,wanda shi ma keta karjejeniya ce. Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hizbullah ta sha yin kira ga gwamnatin kasar da ta yi duk abinda...
    A lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki a watan Mayun 2023, ya ci karo da tsarin kiwon lafiya da ya tabarbare saboda rashin kulawa. Ya ce, “Gwamnatinmu, ƙarƙashin ginshiƙan shirye-shiryen ceto, nan da nan ta fara tantance abubuwan da asibitoci ke buƙata, inda sakamakon ya zama abin tsoro kuma ya nuna akwai jan-aiki. “Alal misali, a jihar da ke da mutane kusan miliyan 6 tare da tarin ƙalubale, na’urar duban ɗan tayi ɗaya ce kawai a cikin dukkan cibiyoyin da gwamnati ta mallaka, kuma shi ma duk faci ne a jikinsa da salataf ko’ina! Nan take na ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya don dawo da ababen more rayuwa, samar...
    Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriryar musulunci ta Iran ta sanar da cewa, saboda yadda Amurka take bai wa ‘yan sahayoniya cikakken goyon baya ne, ya sa su cigaba da aikata laifuka na kisan kiyashi akan mutanen Gaza. Bayanin da ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta fitar, ya zo ne  saboda tunawa da zagayowar lokacin da aka kori Falasdina aka kirkiri HKI, wanda ake kira da “Nakba” ta bayyana cewa; Falasdinawa ne suke da hakkin ayyana makomarsu,kuma nauyi ne na doka da halin kwarai akan kasashen duniya su takawa HKI birki akan kisan kiyashin da take yi a Gaza. Bayanin ya sake jaddada kira da gabatar da masu hannu a kisan kiyashin al’ummar Gaza a gaban kotu domin su fuskanci sakamakon laifukan...
    “Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne.   “Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.”   Taron ya samu halartar Ministar Harkokin Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa; da Ministan Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi.   Sanata Umahi, wanda aka ruwaito ba daidai ba cewa yana daga cikin ministocin da za su gabatar da nasarorin Gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu a wani taro a London, ya goyi bayan furucin Idris, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Jam’iyyar NNPP wadda Dakta Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu ƙarfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya. Shigowarsa ta farfaɗo da jam’iyyar, inda ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2023 ta hanyar lashe kujerar gwamna da wasu kujerun majalisa. Sai dai rikicin cikin gida da na shugabanci sun dabaibaye jam’iyyar, wanda hakan ya haddasa ficewar wasu manyan ’ya’yanta zuwa APC, lamarin da ke haifar da tambaya kan makomar NNPP a Kano. Shin NNPP za ta kai labari a Kano, musamman bayan ficewar wasu jiga-jiganta? NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta shirya wata zanga-zanga da Falasdinawa ke jaddada cewa: babu halacci ga ‘yan mamaya kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da gwagwarmaya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da halacci ko kuma wani ikon mallakar wani yanki na Falasdinu da ta mamaye, kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da kare kansu ta hanyar gudanar da gwagwarmaya har sai sun kwato dukkanin Falastinu tare da kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci kai wacce Qudus zata kasance a matsayin babban birninta. A yayin bikin cika shekaru 77 da kafuwar Nakba, -boren Falasdinawa na farko- kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewa: “Ba za a yi wani sabon...
    Kashi na biyu na maniyyata 415 daga jihar Kwara sun tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.   Da yake jawabi ga maniyyatan jihar kafin tafiyarsu, Amirul-Hajj na Jiha, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya- Alebiosu ya shawarce su da su kasance jakadu nagari na jihar yayin da suke kasar Saudiyya.   Oba Yahaya- Alebiosu ya ce gwamnatin jihar ta samar da matakai daban-daban don tabbatar da annashuwa da kare lafiyar alhazai a tafiyar da suke yi a kasa mai tsarki.   Mai baiwa gwamnan jihar Kwara shawara ta musamman kan harkokin addini, Alhaji Ibrahim Dan-Maigoro ya jagoranci tawagar maniyyata guda 415 zuwa kasar Saudiyya.   An dauke Mahajjatan ne a jirgin Max Airline daga filin...
    Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.   Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan 1.5 aka bayar da rahoton, sun samu maki kasa da 200 daga cikin mafi girman maki 400, lamarin da ya haifar da damuwa a bangaren ilimi na kasar.   UTME ta wannan shekara, ta gamu da koma baya sosai, wanda ya haifar da damuwa tsakanin ɗalibai, iyaye, da malamai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Shugaban Asibitin ido dake Gaza, Dr. Abdussalam Sabah, ya sanar da cewa, adadin Falasdinawan da su ka rasa ganinsu sanadiyyar yaki sun kai 1500. Dr. Abdussalam ya kuma yi gargadin cewa da akwai wasu Falasdinawa da sun kai 4000 da suke fuskantar barazanar rasa idanunsu saboda rashin kayan aiki a asibiti da kuma magani. Likitan na asibitin idanun Gaza, ya kara da cewa; Rashin kayan aiki a asibitin domin yin tiyatar ido, yana yin barazanar tsayuwar aikin asibitin baki daya. Dr. Abdussalam ya kara da cewa; A halin yanzu almakashi 3 kadai ake da shi a asibitin, irin wanda ake amfani da shi domin yin tiyatar ido. Da dama daga cikin masu lalurar idanun sun same ta ne sanadiyyar fashewar...
    Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar. Alkali Emeka Nwite ya ɗage shari’ar bayan ya saurari hujjojin daga ɓangaren masu gabatar da ƙara da na masu kare Yahaya Bello. An Karrama Shugaban Qausain TV, Kanar Sani Bello Da Lambar Yabo Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Lawal Yahaya Gumau Ya Rasu Yana Da Shekara 57 Wani shaidar hukumar EFCC, Nicholas Ojehomon, wanda ya faɗi a kotun cewa ba a tura kuɗin karatar ƴaƴan gidan Yahaya...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin  da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon  watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni  akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda yake faruwa a tsakiyar duniyar musulunci,kuma dukkanin duniya tana Kallon abinda yake faruwa. Shugaban na kungiyar Ansarullah ya kuma ce, a baya, ba a Kallon laifuka irin wadannan kai tsaye ta talbijin amma a yanzu ana Kallon ta akwatin talabijin. Shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya kuma yi gargadin cewa da akwai sakamakon da zai biyo bayan wadannan manyan laifuka,yana mai kara da cewa. Alummar musulmi,...
    Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasim, ya bayyana cewa mutanen kasar Lebanon zasu ci gaba da gwagwarmaya da HKI wacce ta ke mamaye da wasu kasashen larabawan yankin har zuwa nasara. Tashar talabijibn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheik Kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo a taron da aka fara gudanarwa a yau a makarantar Darushafia dake birnin Qom. Taron na Qom yana Magana dangane da “Makarantun Hauza a Qum, Juyin juya halin musulunci a Iran da kuma Gwagwarmaya’. Sheik Kasim ya kara da cewa mutanen kasar Lebanon sun fara gwagwarmaya ne bayan gwamnatin HKI ta mamaye kasarsu, sannan bayan sun sami jagoranci da tunanin Imam Khumaini (q)...
    Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, shekaru 80 da suka gabata, al’ummomin kasar Sin da na kasar Rasha sun bayar da gudummawa mai tarihi da ba za a taba mantawa da ita ba wajen samun nasarar yaki da zaluncin danniya a duniya, tare da kulla kakkarfar alaka da ba za a iya kassarawa ba ta hanyar sadaukar da jini, wadda ta kafa tubulin raya dangantakar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al’umma. Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar “gwagwarmaya” da rikici ko sabani da gwamnati. NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda za a yi gwagwarmaya ba tare da an taka doka ba. Domin Sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al’umma. Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar “gwagwarmaya” da rikici ko sabani da gwamnati. NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda za a yi gwagwarmaya ba tare da an taka doka ba. Domin Sauke shirin, latsa nan
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta. ////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata, sannan take barazanar zata farwa kasar da yaki saboda shirin na makamashin nukliya, sabbin rahotanni sun bayyana cewa iran tana gaba a fitar da kayaki kasuwanci zuwa kasar China sannan ita ce ta 9 a duniya wajen samar da kwan kaji da sauran tsuntsaye. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa, yawan danyen man fetur wanda kasar Iran take sayarwa kasar China...
    ’Yan bindiga sun kashe wata mata da suka sace tare da mijinta Yakubu Dada watanni bakwai da suka gabata a yankin Kontagora da ke Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa ’yan ta’addan sun halaka matar mai suna Lami bayan karɓar Naira miliyan 10 kuɗin fansa. ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano Kwankwaso: Abba ya mayar wa Baffa Bichi martani Kazalika, ’yan bindigar sun kuma nemi ƙarin Naira miliyan 20 da baburan Bajaj huɗu, tare da yin barazanar kashe mijinta muddin aka gaza kai musu abubuwan da suka buƙata. Aminiya ta ruwaito cewa, tun a ranar 31 ga watan Oktoba na 2024 ne Yakubu Dada da mai ɗakinsa suka faɗa tarkon masu garkuwa yayin da suke kan hanyar zuwa Kontagora....
    Yau Litinin ne kotun kasa da kasa ta ICJ za ta yanke hukunci kan karar da Sudan ta shigar kan Hadaddiyar Daular Larabawa. Khartoum ta kai karar UAE a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, inda ta zarge ta da hannu wajen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit, sakamakon zarginta da goyon bayan dakarun (RSF) da suka shafe shekaru biyu suna yaki da sojojin Sudan. Khartoum na zarginsu da kasancewa masu goyan bayan kisan kare dangi” da ake ci gaba da yi wa al’ummar Massalit na Darfur, saboda zarginsu da goyon bayan dakarun gaggawa na Janar Hemedti (RSF). Khartoum na fatan alkalan kotun su umurci Hadaddiyar Daular Larabawa da ta daina goyon bayan kungiyar RSF,...
    An kamala gudanar da zabe a yankin jabal Lebanon na kasar Lebanon a safiyar yau Lahadi har an kuma an fara irge. Tashar talabijin ta Almanar ta kasar ta bayyana cewa an bude rumfunan zabe tun karfe 7 na safe, kuma an kamala zaben da yamma. Sannan ma’aikatar cikin gida da kuma kananan hukumomi ta bayyana cewa mutanen da suka fito don kana kuri’insu ya kai kimani kashi 45.% da yan kai. Yankin Jabal Lobnon dais hi ne yanki mafi yawan mutane a kasar kuma yanki ne wanda hizbullah take da masu goyon baya da dama. Matsalolin daya dayan daya, wadanda suka hada da rashin kudade da rashin gwamnati ya hana a gudanar da zabubbuka kananan hukumomin wanda yakamata a...
    “Siyasar da na sani ba ita ce abin da ke faruwa a yau ba. Siyasar da na sani ita ce gwagwarmayar muradun jama’a don tabbatar da cewa suna da kyakkyawar rayuwa a duk fannoni kamar ilimi, ruwa, kiwon lafiya, da sauransu. “Na kasance a siyasa tsawon shekaru 48 da suka gabata,” in ji shi. Ya bayyana yanayin siyasa a matsayin wanda ke cike da rudani da son kai, yana mai jaddada cewa ‘yan siyasa da talakawa sun rikice. “Saboda wannan, akwai rudani ga masu nema da kuma wadanda ake nema. Masu neman suna makancewa, ba su da imani ko tausayi. Manufarsu kawai ita ce tabbatar da matsayi a gare su. A halin yanzu, talakawa sun tsunduma ciki yunwa, talauci, da...
    Ministan harkokin jin kai da rage radadin talauci na UNOCHA, Farfesa Nentawe Goshwe, ya sanar da yunkurin hukumar na ficewa daga Nijeriya. Ya shaida hakan ne a yayin taron kara wa juna sani kan tsarin da za a dauka a Nijeriya, wanda aka gudanar a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a Abuja. A cikin wata wasika da aka yada a shafin intanet na hukumar a ranar 11 ga Afrilu, shugaban hukumar ta UNOCHA, Tom Fletcher ya ba da sanarwar yanke ayyuka sakamakon karancin kudade na kusan dala miliyan 60 a shekarar 2025. Hukumar ta ce za ta rage ayyukanta a Nijeriya, Kamaru, Kolombiya, Eritriya, Iraki, Libya, Pakistan, Turkiyya da Zimbabwe,...
    Wata ƙungiyar matasa mai suna “North-East Coalition Against Terrorism” ta yi maraba da Major General Abdulsalam Abubakar, sabon kwamandan yakin Operation HADIN KAI (OPHK), inda ta bayyana cewa tana fatan zaman lafiya ya dawo yankin. A cikin wata sanarwa da Ismail Mustapha da Sakatare Danlami Bukar suka rattaba hannu, ƙungiyar ta ce Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin babban Hafsan Soja Janar Chris Musa za su ci gaba da matsa lamba kan mayakan. Ta kuma yi kira ga al’ummar yankin su ba sabon kwamandan goyon baya. Boko Haram Sun Kashe Masu Kamun Kifi 18 A Borno Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato  Ƙungiyar ta gargadi matasa su ƙi tayin shiga ƙungiyoyin da ba...
    Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna.   Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan cuta, amma asalin kudaden sun zarta haka, musamman idan Maleriyar ta yi kamari, za a iya kashe ninki uku ko sama da haka na wannan kudi.   Yayin da duniya ke yin wannan biki na ranar Maleriya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nanata cewa, cutar na ci gaba da zama barazana, musamman a yankuna masu fama da zafi, duk da cewa; cuta ce da...
    Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta kawo tabbaci da kuma kyakkyawar makoma ga duniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja. Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke Jihar Kaduna. Hanyar na ci gaba da ganin ƙaruwar kwararan motoci a sakamakon ingancinta da kuma karancin matsalar tsaro, idan a ka kamanta ta da babban titi Abuja zuwa Kaduna. Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027 An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Adadin motoci da ke bin titin ya kara dagawa a bayabayan nan a dalilin...
    A Kaduna, an kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wani da ya ce ya koma jihar ne domin kafa sabuwar ƙungiya bayan an kama abokan aikinsa a Kwara. Haka kuma, an kama wasu biyu da ke ɗauke da bindigogi. ‘Yansanda sun gano makamai da dama, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 da AK-49, da kuma wasu makamai da aka ƙera a gida. Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na yaƙar garkuwa da mutane da safarar makamai a faɗin ƙasar. Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu da zarar an kammala binciken. Ya kuma yaba da goyon...
    A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana. An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida. DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno PSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba. Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan.   A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama.   Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013...
    “Gwamnati ta amince da hada hannu da shugabannin al’umma na cikin gida domin tabbatar da tsaro.   “Muna gode muku kan abin da kuke yi. Amma muna bukatar Sarakuna su yi magana da mutanenmu kan kokarin da dukkanmu muke yi don kare al’ummominmu daga masu kutse.”   Gwamnan ya yi kira da a inganta hadin gwiwa a tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.   Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Bologi II, wanda shi ne Etsu Patigi, ya yaba wa gwamnan bisa hada gwiwa da su domin tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron. Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore. Har’ila yau ana gudanar da bincike a...
    Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan  kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata,  jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National  ”  bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
    Fira ministan Indiya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kokari da zage dantse wajen taimakawa a fagen inganta zaman lafiyar yanki da na duniya baki daya Fira ministan Indiya Narendra Modi ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, yana mai cewa: Gwamnatin Indiya tana goyon bayan kokarin Iran na karfafa zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya, yana mai jaddada bukatar warware takaddama ta hanyar diflomasiyya, ciki har da na Iran da Amurka. Har ila yau fira ministan na Indiya ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da abin da ya faru a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke lardin Hormozgan a kudancin kasar Iran,...
    ’Yan kasuwar kayan abinci sun bayyana yadda suke tafka asara  bayan sun saye wasu kaya sun ajiye suna jiran samun tuna mai tsoka idan kayan sun yi tashin gwauron zabo. A shekarar bara, ’yan kasuwa, musamman masu hadahadar kayan abinci da na amfanin gona a Nijeriya, kakarsu ta yanke saƙa, saboda tashin gwauron zabon da kayan a ƙasar. Galibin waɗannan amfanin gona na kasuwanci ana fitar da su zuwa ƙasashen a duniya. Hukumar Bunƙasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC) ta sanar a watan Agusta na shekarar ta 2024, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci-gaba a fannin fitar da kayayyaki da ba na man fetur ba a watanni shidan farkon shekarar, inda ta samu kuɗin shiga kimanin dala biliyan 2.7....
    “Rashin samar da daidaito a hada-ahadar kasuwanci, ya kasance abinda ya sanya Hukumar ta NPA ke cazar kudaden gudanar da aiki da yawa,” Inji Dantsoho.   Dantsoho wanda Janar Manaja na sashen hudda da jama’a da gudanar da tsare-tsare na Hukumar NPA Miista Seyi Iyawe Akinyemi ya wakilce shi a wajen taron, ya ce, NPA ta bai wa kamfanini biyar Lasisi a jihar Legas, bisa kokarin da take yi, na bunkasa fitar da kaya zuwa waje ta hanyar amfani da Tashoshin ta.   Sai dai, ya sanar da cewa, Hukumar na duba yuwuwar samar da rangwamen cazar kudaden, musamman domin ta kara inganta ayyukanta.   Ya yi nuni da cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa waje ne da ke taimaka wa wajen...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi kashedin kan illar ci gaba da killace Gaza da kuma hare-haren ta’addancin ‘yan mamaya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da rashin hukunta ‘yan sahayoniyya kan kisan gillar da suke yi a zirin Gaza da Gabar yammacin kogin Jordan, da kuma mamayar wasu yankunan kasar Labanon da Siriya yana da matukar barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan ci gaba da ayyukan wuce gona da iri da na ta’addancin yahudawan sahayoniyya a Gaza da Lebanon.
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a cikin yankunan Siriya, a cikin abin da gwamnatin Isra’ila ta kira “yankin da ke da kariya,” wanda ya hada da mamaye wasu sassan garuruwan Quneitra da Dara’a. Majiyoyin cikin gida a garin Nawa da ke cikin karkarar Dara’a na cewa, mahukuntan kasar Siriya na ci gaba da daukan matakan matsin lamba, ta hanyar shugabannin kabilu da kwamandojin ma’aikatar tsaro a Dara’a, na tilastawa bangarorin da...
    Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda.   A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22  a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba.   A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar.   Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda.  ...
    Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti.   “An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan sun gama jinya,” in ji sanarwar.   Rundunar ‘yansandan ta ce Baba-Beru, mazaunin Kofar Mazugal a karamar hukumar Dala, na cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo kafin faruwar lamarin.   Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, ya yabawa bajintar jami’an da suka dakile yunkurin ‘yan fashin tare da jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.  ...
    Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akif al-Masri, kwamishinan hukumar koli ta al’amuran da suka shafi Falasdiwa a Gaza, ya ce: “Matsalar yunwa tana barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutanen Gaza,  yana mai cewa: Mafi yawan gidaje kusan babu kayan abinci, kuma iyalai ba za su iya samun abincinsu na yau da kullum ba.” Al-Masry ya tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun ketare dukkan iyakokin kasa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga tarin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu sabbin matsalolin na ƙara kunno kai. Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar hare-haren da ake zargin na ƙungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, da kuma sabbin kashe-kashe a sassan jihohin Filato da Binuwai, sai kuma ga wata sabuwar ƙungiya da ake zargin ta ’yan ta’adda ce mai suna Mahmuda ta ɓulla a Jihar Kwara. To ko mene ne ya haddasa wannan koma-baya ta fuskar tsaro? Shin a ganinku, me ya sa matsalar tsaro “ta gagari gwamnatin” Najeriya? NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi DAGA LARABA:...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City dake buga babbar gasar Firimiya ta kasar Ingila ta koma gasar yan dagaji ta Championship bayan da tayi rashin nasara a guda a wasanta da Liverpool. Leicester wadda ta lashe gasar Firimiya a shekarar 2016 ta samu maki 18 kacal a wasanni 33 da ta buga, ta zura kwallaye 27 yayinda aka zura mata kwallaye 73 a ragarta, Leicester ta koma gasar Championship duk da cewar akwai sauran wasanni 5 da su ka rage ba a buga ba a gasar Firimiya ta bana. Yaushe Liverpool Za Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila? Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Kocin Leicester Ruud Van Nistelrooy ya karbi ragamar horarwar...
     Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka hada da kwamandojin ‘yan tawaye a shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher. Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: A ranar Alhamis ne sojojin kasar Sudan tare da hadin da tallafin dakarun hadin gwiwa na kungiyoyin fafutuka, da hukumar leken asiri ta kasar da ‘yan sanda, suka dakile wani mummunan hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support...
    Shugaban ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin cewa, ako da yaushe, kofar Hukumar ta NPA, bode take domin hadaka wacce ta zarce ta gudanar da baje koli. Dakta Dantsoho ya kara da cewa, an samar da tsarin na EPT domin a tabbatar da cewa, ana fitar da kaya zuwa waje, ta hanyar yin amfani da na’urar zamani. “Wannan na zai taimaka matuka wajen kaucewa samun jinkiri da kuma mai-maita aiki da Hukumar ta saba fuskanta a baya,” A cewar Dantsoho. Kazalika, Dantsoho ya bayyana cewa, domin a samu sauki wajen kai kaya a tsakanin masu kananan da matsakaitan sana’oi, musamman duba da cewa, tsarin na EPT, zai taimaka matuka ga guraren da ake adana kaya a...
    Waɗanda suka take wa Ministan sawu a tafiyar su ne jagororin hukumomin yaɗa labarai da wayar da kai da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa. Ya yi zama daban-daban tare da ƙwararru inda suka tattauna kan yadda za a inganta ƙwarewa da kuma kayan aiki na zamani na kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya.   Ya ce: “Ina sanar da ku waɗannan abubuwan ne domin jaddada ƙudirin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an samu cigaba mai ɗorewa a fannin watsa labarai a ƙasar nan.   “Wannan ne ma ya sanya muke gudanar da irin wannan taron bita na ministoci, da kuma shirin ƙaddamar da Taron Tattaunawa da Jama’a a sassan ƙasar nan nan gaba kaɗan.” Idris ya kuma...
    Wani mutum mai suna Muhammad Ma’aba daga ƙauyen Fujeregi da ke Ƙaramar hukumar Gbako a Jihar Neja, ya mutu a hannun tsohon mijin matar da yake shirin aura. Rahotanni sun bayyana cewa, wata Ƙungiya ƙarƙashin jagorancin tsohon mijin matar mai suna Alhaji Yikangi, daga ƙauyen Yikangi Chikan ne suka kai wa Ma’aba hari a tsakanin garin Saganuwa da Fujeregi. PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, tsohon mijin ya saki matar mai suna Fatima Suleiman sau uku, amma ya dage cewa ba za ta ƙara aure ba — ko da ta samu sabon mai neman aurenta....
    A ranar Lahadi Liverpool ta sake matsa ƙaimi a gasar Firimiya bayan ta doke abokiyar karawarta West Ham United ci 2-1 a filin wasa na Anfield dake birnin Liverpool, yayin da Mohamed Salah ya kafa tarihin cin ƙwallaye a kakar wasa ta bana, sakamakon ya sa Liverpool ta samu tazarar maki 13 tsakaninta da Arsenal dake matsayi na biyu a kan teburin gasar. Yayinda yake saura wasanni shida a kammala gasar, Liverpool na buƙatar maki 3 kacal domin lashe gasar a karo na biyu tun bayan da aka sauya wa gasar suna da fasali, West Ham na matsayi na 17 da maki 35 akan teburin gasar. Ba Zan Ci Gaba Da Zama A Liverpool Ba -Salah Salah Ya Ƙulla...
    Rahotanni da suke fitowa daga Nigeria sun ce, a kalla mutane 7 su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama su ka jikkata sanadiyyar fashewar wasu abubuwa masu karfi akan hanyar Damboa-Zuwa Maiduguri. Rahotannin sun ce abubuwan su fashe ne dai a lokacin da wasu ayarin motoci da suke wucewa ta hanyar tare da rakiyar sojoji a jiya Asabar da hakan ya haddasa asarar rayuka da kuma jikka. Hanyar Damboa zuwa Maiduguri tana zuwa kananan hukumomi da dama a kudancin Jahar ta Borno, a lokaci daya kuma yanki ne da ya yi kaurin suna a matsayin matsugunin ‘yan Bokoharam. An dade da rufe hanyar saboda matsalar tsaro, amma gwamnatin Babagana zulum ta sake bude ta, da kuma dawo da...
    Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar wadanda ta ke tunanin za su tsaneta kasancewarta jarumar fim sun zamo masoyanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun da safiyar yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka. Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa  Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran. A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi, ministan harkokin wajen Iran ya yaba da matsayar Oman akan batutuwa da dama su ka shafi wannan yankin na yammacin Asiya.  Daga cikin masu yi wa ministan harkokin wajen na Iran rakiya da akwai  mataimakinsa a fagen dokokin kasa da kasa...
    Sojojin HKI suna ci gaba da yin kiyashi a sassa mabanbata na Gaza, da a bayan nan su ka yi wa mutane 30 kisan kiyashi a unguwar Shuja’iyya dake birnin Gaza.  Majiyar asibitin Falasdinawa ta ambaci cewa; Harin da sojojin HKI su ka kai da manyan bindigogi sun yi sanadiyyar shahadar mutane 17 a unguwar ta Shuja’iyya.Dama tun da safiyar Laraba wasu Falasdinawan 50 sun yi shahada a wannan unguwa ta Shuja’iyya dake cikin birnin Gaza. Wasu majiyoyin Falasdinawa sun ambaci cewa: Sojojin mamayar sun kai wasu hare-haren da manyan bindigogi a kusa da masallacin; UMMU HaBIBAH, da kuma kasuwar sayar da kekune a yankin Qaizan a kudancin Khan-Yunus. A gefe daya,majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa; Da akwai Falasdinawa miliyan...
    Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani  kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja. Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan. Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke ɗauke da fasinjoji da kuma buhunan shinkafa kimanin 200 daga ƙauyen Bugge na Jihar Kogi a zuwa ƙauyen Sokun na Jihar Neja a ranar Laraba da dare. Wani mazaunin yankin, Baba Alhassan, ya shaida wa wakilinmu cewa, ba a kai ga tantance ainihin yawan fasinjojin da ke cikin kwalwkwalen a lokacin da lamarin ya faru ba, amma an yi asarar duk buhunan shinkafar a hastarin....
    Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fidda jadawalin kudaden fito ga dukkan kayakin da suke shigowa Amurka daga wadannan kasashen, daga ciki har da kasashen Turai da kuma kasar Chaina, ya zuwa yanzu dai kasar china ta maida martani da kashi 34% na kayakin Amurka da suke shigowa kasar China, sannan Amurka ta kara maida martani ga kasha 104 kan kayakin kasar china masu shigowa Amurka, sannan kasashen turai da dama...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa JMI ba zata taba jada baya a kan shirinta na makamashin Nukliya ba, kuma yayi allawadai da duka wani shiri na kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Hare-hare. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron raya ranar Nukliya ta karo karo na 19 a wanda aka gudanar a nan Tehran. Shugaban ya kara da cewa, Iran bata neman yaki da kowa, amma zata maida martani kan duk wata takala daga HKI ko Amurka. Ya ce Iran ba zata amince wani ya hana mutanen kasar amfani da fasahar da All..ya hore masu ba. Ya kuma kara jaddada cewa JMI bata neman mallakar makaman Nukliya. A rana irin ta yau ce...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yi tir da gwamnatin Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, saboda dirar mikiyan da ta yi kan Falasdinawa a yankin wadanda suke zanga-zangar beman HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da ta yi a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Litinin ce, Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, suka rufe shagudansu da harkokin kasuwancinsu da kuma ofisoshinsu don neman HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da suke yiwa yan uwansu kuma yan kasarsu a Gaza. Amma kamar yadda jami’an tsaron HKI ta hanasu zanga zanga a wasu wurare, jami’an tsaron gwamnatin Falasdinawa a yankin ma, karkashun...
    Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas. Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu. Hundeyin ya ce makwabta ne suka kwarmata wa Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke yankin Okokomaiki, bayan mutumin ya kashe ’yar tasa ya kuma binne ta a cikin harabar gidansu. Jami’in ya ce ““Bayan samun rahoto jami’anmu suka ce suka gano kabarin, suka tono gawar aka gudanar da bincike,” shi kuma yana hannun hukuma yana amsa tambayoyi. Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga Algeria...
    Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wasu ƙauyuka na Ƙaramar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato. Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Ruwi, Manguna, Daffo, Josho da Hurti. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana waɗannan hare-hare a matsayin rashin hankali da tausayi. Ya ce an kashe mutane da dama ciki har da mata da yara, yayin da wasu da dama suka jikkata. Ya ƙara da cewa irin waɗannan hare-hare na barazana ga zaman lafiya da haɗin kan yankin Arewa. A wata sanarwa da kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, ya...
    Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu nay au zai yi magana kan cewa “Amurka ba zata taba zama mai sulhuntawa tsakanin HKI da Falasdinawa ba” wanda ni tahir amin zan karanta. A dai dai lokacinda rikicin gaza ya zama matsalar ta duniya a halin yanzu, da dama daga cikin masana suna ganin gwamnatin Amurka wacce ta kasance mai goyon bayan HKI na asali ba zata kuma zama mai shiga tsakanin don kawo karshen rikicinta da falasdinawa ba. Dangane da wannan shafin yanar gizo mai suna “Alkhanadik’ ya rubuta wani sharhi dangane da yakin na gaza a jiya Asabar yana cewa, a dai dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka ta kasance bangare babba a cikin haddasa matsaloli ga al-ummar Falasdinu na...
    Yayin ziyararsa kasar Sin kwanan nan, babban mashawarcin gwammatin wucin-gadi ta kasar Bangladesh, Muhammad Yunus, ya tattauna da wakiliyar CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, inda a cewarsa, a matsayin kasa ta farko a kudancin nahiyar Asiya, wadda ta rattaba hannu tare da kasar Sin kan takardar bayanin hadin-gwiwa game da raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, Bangladesh na matukar bukatar shawarar nan, ganin yadda aikin raya shawarar ke da muhimmanci sosai. Muhammad Yunus ya ce, Bangladesh na matukar bukatar cudanyar sassa daban-daban. Hanyoyin mota na taka rawar gani wajen jigilar hajoji, don haka kasar na bukatar kara shimfida hanyoyin mota. Hanyoyi su ne tamkar manyan jijiyoyin tattalin arzikin kasa, shi ya sa ya...
    Tsohon Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano kuma tsohon Mashawarci na Musamman ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, CP Muhammad Wakili (ritaya), ya jaddada cewa dole ne ’yan sanda su yi amfani da ikon da suke da shi cikin gaskiya da adalci, don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Da yake jawabi a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Gombe, a matsayin wani ɓangare na bikin makon ’yan sanda, CP Wakili ya ce ba zai yiwu jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba tare da goyon bayan al’umma ba. An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu zuwa Kudu Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52 Ya buƙaci jami’an...
    Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su. Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar. Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su.   Ya kara da cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a kara musu kudin fansa, amma hakan ba ta yi wu ba.   Wata majiya mai tushe ta sojoji ta kuma tabbatar da sakin Tsiga. Majiyoyi na kusa da dangin sun ce yana cikin koshin lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma. Dawowarta ta zo ne a daidai lokacin da ake cike da rikicin siyasa, domin tun da farko gwamnatin jihar Kogi da rundunar ‘yansandan jihar ta kafa dokar hana tarukan jama’a, saboda dalilan tsaro. Sannan kuma, shugaban karamar hukumar Okehi, Hon. Amoka Eneji, ya kuma sanya dokar hana fita a karamar hukumar a wani yunkuri na dakatar da shirin dawowar Natasha gida a yayin bukukuwan Sallah tare da...
    Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan.   Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara.   Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.   Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumin Ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka haɗa da ƙara ƙaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da al’umma da kuma falala masu yawa da ba su misaltuwa. Wani sauyi da watan azumin watan Ramadana ke zuwa da shi shi ne canjin yanayin cimar al’umma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma buɗe-baki. Bayan kwanaki 29 zuwa talatin na samun waɗannan canji, ta waɗanne hanyoyi ne al’umma za su koma cimaka kamar yadda suka saba gabanin watan Ramadana NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah...
    Asbitin ‘Mount Sinai’ (Dotsen Sinaa’ a kasar Amurka ta salami wata likita daga aiki, bayan da aika da wani rubutu da hoto a shafukan yanar gizo tana, wanda Asbitin tana cewa ai Musanta hare-haren ranar 7th ga watan Octoba ne’. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa Dr Leila Abbasi,diyar shekara 46 a duniya, ta aika sako cikin shafinta na yanar gizo inda take goyon bayan kungiyoyin Hamas da Hizbullah na kasar Lebanon sannan tana allawadai da kuma aibata HKI kan kissan yara da take yi a Gaza.   Gwamnatin kasar Amurka dai tana ganin kanta a matsayin kasa wacce take gaba wajen kare hakkin fadin albarkacin baki, amma idan al-amarin ya shafi HKI sai ta nuna...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan  na Ramadan. Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa  shugabanni jagorancin  don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma. Namadi ya kuma yi addu’ar samun  zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa. ...
    Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare. Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman na biyu, ya jaddada muhimmancin hadin kai wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a lokacin da ya gabatar da sakon Sallar a fadarsa da ke Kauru. Alhaji Zakari Ya’u Usman ya kuma yi gargadi game da masu ba da labari da ke taimaka wa masu laifi tare da karfafa gwiwar mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi. Dangane da...
    Har ila yau, masu bincike sun gano wasu tsoffin dabarun hana koguna da madatsun ruwa ambaliya da yadda aka tsaga manyan hanyoyin ruwa da aka yi amfani da su shekaru 5,000 da suka gabata, a wani tsohon yanki na Zhejiang ta hanyar amfani da kayan binciken muhalli. Binciken ya fayyace wayewar kai na tsara birane da kula da koguna da hanyoyin ruwa irin na Liangzhu a tsohon zamani. Babu shakka, amfani da wayewar kan magabata a zamaninmu na yanzu yana daga cikin sirrin nasarorin da Sinawa ke samu ta fuskar wayewar kai da bunkasa ci gaban kimiyya da fasaha da kere-kere da kirkire-kirkire. Ina fatan kasashenmu na Afirka su dau hannu domin jifar tsuntsu biyu da dutse daya, tabbatar da...
     Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya yi murabus daga mukaminsa. An tabbatar da murabus din nasa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar. Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din a hukumance, inda ya nuna jin dadinsa da irin gudunmawar da Janar din sojan ya bayar a lokacin da yake gudanar da aikinsa. Rasha Da Ukraine Sun Amince Da Tsagaita Wuta A Tekun Black Sea Kasuwar Kayayyakin Masarufi Ta Sin Za Ta Ci Gaba Da Nuna Yanayin Bunkasa Bisa Daidaito A Bana LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Manjo janar Idris (mai ritaya) shi ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ce bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan al’amura. Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shi ne na farashin kayayyakin masarufi. A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka. NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Ƙasa Kiranye DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna Shirin Daga Laraba na wannan makon zai tattauna ne kan farashin kayayyakin masarufi gabanin bikin sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
    Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; An kai hari nau’i biyu, da ya hada amfani da motar take mutane da kuma bude wuta daga bindiga. Harin da aka kai a kusa da yankin “Yukna’am Iliyat” dake gabashin garin Haifa, ya yi sanadiyyar halakar wani dan share wuri zauna da kuma jikkata wani guda daya. ‘Yan sandan HKI sun ambaci cewa, wanda ya kai harin ya isa wurin ne a cikin motarsa, inda ya sami ‘yan share wuri zauna da yawa a tashar mota, ya kuma bude wuta akan masu wucewa da hakan ya yi sanadiyyar jikkata wasu da dama. Ma’aikatan Agaji kuwa sun amabci cewa baya ga halaka da kuma jikkatar ‘yan share wuri zauna, an harbe mahari. Tashar...
    Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo a wasan da Portugal ta doke abokiyar karawarta ƙasar Denmark a daren ranar Lahadi, ƙwallon ita ce ta 929 da tsohon ɗan wasan na Manchester United ya jefa a tarihinsa na ƙwallon ƙafa, duk da cewar ya ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da Portugal ta tsallake rijiya da baya, hakan ya sa ta kai wasan dab da na kusa da na karshe a gasar ta Nations League. An tashi wasan ne da ci 3-3 jimilla bayan mintuna 90, amma Francisco Trincao ya sake zura kwallo a minti na 10 na ƙarin lokaci bayan da mai tsaron ragar Denmark Kasper Schmeichel ya ture wata ƙwallon da Goncalo Ramos ya buga....
    Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta. Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta...
    Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD a Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa a kasa Switzerland Chen Xu ya yi jawabi a gun taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 58 kan batun kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, inda ya yi bayani game da tunanin Sin kan kare hakkin dan Adam da kin amincewa da siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam. Chen Xu ya yi nuni da cewa, ana bukatar bin ra’ayin bangarori daban daban da tunanin kare hakkin dan Adam da yin hadin gwiwa mai amfani don sa kaimi ga raya sha’anin kare hakkin dan Adam. Wasu kasashe sun yi amfani da dalilin kare hakkin dan Adam wajen tsoma...
    A wata hira da tashar talabijin din, manzon musamman na Amurka a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff ya rubuta a shafinsa na; X cewa; Sakon da Trump ya aike wa  Tehran ba ta nufin yin barazana. Manzon na Amurka ya riya cewa;wasikar ta kunshi cewa; Ni shugaban kasa ne mai son zaman lafiya , abinda  nake son bayyanawa kenan, don haka babu bukatar a yi magar yaki. Wajibi ne mu zauna mu tattauna.” Wittkoff ya kuma ce; Da akwai hanyoyi na bayan fage da ake tatatunawa da Iran. Har ila yau ya kara da cewa; Abinda Trump yake so shi ne warware sabanin da ake da shi. Shafin watsa labaru na Axos ya bayyana cewa; Waskiyar da Trump din...
    Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa. Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake. Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma...
    Gwamnatin HKI ta bayyana damuwarta da jibge sojojin da gwamnatin kasar masar take yi a yankin Sinaa kusa da kan iyakar kasar da HKI. Tun bayan da gwamnatin HKI ta gama lalata makaman gwamnatin kasar Siriya bayan ta taimaka ta kawo dan Daesh kan kujerar shugabancin kasar ta Siriya, kuma ta bayyana cewa yankunan da ta mamaye a kasar Siriya sun zama HKI ne har abada.take nuna damuwa da kasar Masar. Banda haka mun ga yadda sabon shugaban kasar ta Siriya  Julani ya yi shiri da bakinsa a kan mamayar da HKI takewa kasar Siriya da kuma yadda ta kai hare-hare fiye da dubu guda kan kasar tana lalata makamanta, ko wa ya fahinci cewa, siriya ta gama yawo,. Kuma...
    Sama da shekaru 80 kenan da kafa VOA wadda ke yada shirye-shiyenta cikin harsuna 40. Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki daya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun hada da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da bangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Daga ciki har da hukumar US Agency for Global Media wadda gidan rediyon Muryar Amurka wato VOA ke karkashinta da Radio Free Europe da Asia da Radio Marti wadda ke yaɗa labarai da Sifaniyanci a Cuba. Haka kuma tuni Trump din ya soma daukar wasu matakai wadanda suka...
    ’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya.  Farashin kayan abincin ya karye ne a lokacin da wasu ’yan kasuwar suka riga suka saye amfanin gona suka boye tun a lokacin kaka, da nufin rubanya kudinsu idan farashinsa ya yi tashin gwauron zabo daga musamman a lokaci irin wannan na azumin watan Ramadan, da wasu bayin Allah suke saya don raba wa mabukata. ’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a Katsina ’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu Kudin hatsi irin su shinkafa da...
    Da yake jaddada cewa ya kamata mutane su fahimci cewa a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, ba wai shi kadai ke wakiltar mazabarsa da jam’iyyarsa ba, har ma da yankin da ba a taba rike wannan mukami ba tsawon shekaru 46 da suka gabata.Shugaban majalisar ya bukaci wadanda ke sukar sa da su yi shiru da bakinsu. Akpabio ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa ba wai kansa kadai yake wakiltar ba, al’ummar yankin Neja Delta gaba daya ba yake wakilta. A yayin da yake jawabi a kan batun samar da kujerun zama da ya shafi Natasha Akpoti-Oduaghan, wanda ya kai ga zargin cin zarafi, Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa mutane suna ihu ne kawai ba tare da fahimtar ka’idojin...
    A jawabinsa na godiya a wurin taron, dan majalisar dokokin ya bayyana godiya ga al’ummar Funtuwa, ya ce zai ci gaba da kawo ayyukan alheri tare da abubuwan jin dadin more rayuwar ga al’ummar mazabunsa na Funtuwa da kewayenta gaba daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.   Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.   A cewar Gidan-Goga, Ministan ya zabi bayar da kudi ne maimakon kayan abinci, saboda tuni wasu ‘yan siyasa a jihar suka raba wa magoya bayansu hatsi.   Ya kuma jaddada cewa tallafin kudi zai baiwa magoya bayan jam’iyyar APC damar siyan wasu muhimman abubuwan da ake bukata a cikin watan Ramadan.   “A wannan karon,...
    Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace. Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa. “Amma da suka hango...
    Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da tallafin kayan abinci ga magidanta dubu 30 a fadin jihar. A yayin da yake kaddamar da tallafin tare da bayar da jari ga masu kananan sana’oi a gidansa a ranar Litinin, ya bayyana cewar tallafin wani mataki ne na saukakawa mabukata halin kunci a watan Ramadan mai girma. Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Alhinin Rasuwar Fitaccen Masanin Aikin Jarida, Kabir Ɗangogo Tambuwal wanda ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a majalisar dattawa, ya bukaci wadanda za su rarraba kayan abincin da su gudanar da gaskiya da adalci wajen tabbatar da tallafin ya kai hannun wadanda suka cancanta a mazabu 244...
    Adelaja ya jaddada mahimmancin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi, duba da irin kaifin basira da masu fasa-kwari ke amfani da wasu a ‘yan kwanakin nan wurin cimma muradunsu.   “Masu fasa kwauri na ci gaba da bunkasa a ayyukansu, kuma don tunkararsu yadda ya kamata, dole ne mu hada kai ta hanyar bayar da bayanan sirri don cimma nasarar ayyukanmu,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Kuma wasu sun yi amannar cewa, hakan ne ya sa manufar babban yankin kasar Sin a kan Taiwan ta zama mai tsaurin gaske. Da take mayar da jawabi game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa da ya gudana yau 10 ga wata cewa, wannan shi ne daidaitaccen matsayin...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin...
    Shugaban Amurka Donald Trump, ya katse tallafin da yake baiwa jami’ar Columbia saboda zanga-zangar goyan bayan Falasdinu. Trump ya ce an katse tallafin na dala miliyan 400 ga jami’ar, daya daga cikin manyan a kasar, bisa zarginta da gazawa wajen fuskantar ayyukan kyamar Yahudawa a harabarta, wanda ke nufin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Ana kallon wannan a matsayin alwashin da Donald Trump, ya sha a lokacin yakin neman zabe inda sha yin tir da yadda wasu jami’o’i ke nuna gazawa wajen fuskantar zanga zangar goyan bayan Falasdinu. Masana da dama na ganin matakin a matsayin misali na siyasantar da manyan makarantu da kuma tsoma bakin gwamnati. Shugaban kungiyar jami’o’in Amurka ya bayyana cewa matakin na gwamnatin Trump “ya haifar da...
    A cikin abubuwan da aka tattauna a taron, a cikin kananan hukumomi 774, Jihar Delta ce kadai mai kananan hukumomi 25, suka mika bayanan asusunsu domin biyansu kai tsaye. “Kawo yanzu kananan hukumomin Jihar Delta ne kawai suka bayar da bayanan asusunsu. “Duk da haka, ana ci gaba da tuntubar babban lauyan gwamnatin tarayya game da yadda ake gabatar da asusun.” Da take maida jawabi kan kalubalen, Madein ta ce an tsara tsarin da za a aiwatar, amma kalubalen farko shi ne na tantance shugabannin kananan hukumomin da tsarin mulki ya zaba. Ta bayyana cewa wannan matakin ya kasance mara tabbas. “Bugu da kari, ga wadanda ke da zababben shugabanci, akwai alaman tambaya cewa wasu hanyoyin za a bi don...
    Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a yau Juma’a yahudawa 800 sun kutsa cikin iyakar Lebanon, zuwa kabarin wani malamin yahudawa Rabbi Ashi. Sun kuwa isa wurin ne a karkashin rakiyar sojojin mamaya. Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce, kabarin malamin yahudawan dai yana a cikin iyakar Lebanon ne dake kallon matsugunin ‘yan share wuri zauna ta Mir Gliot. A cikin makwanni kadan da su ka gabata dai yahudawan ‘yan share wuri zauna sun rika ketaro iyaka daga Falasdinu dake karkashin mamaya zuwa Lebanon, sai dai na yau Juma’a ne mafi girman adadin yahudawan da suka ketara iyaka. Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga sojojin Lebanon ko gwamnati akan abinda ya faru. Amma a jiya...
    An kashe mutane fiye da 70 a fafatawa tsakanin sojojin Hai’at Tahrin Assham Masu Iko da kasar Siriya ta wata kungiyar yan tawaye a yammacin kasar. Ciobiyar watsa labarai ta SOHR ta bayyana cewa an fara yakin ne bayan da aka kaiwa sojojin HIS harin ba zata a kan bakin teku a daren Jumma.a. SOHR wacce take sanya ido a kan al-amuran kasar Siriya ta bayyana haka a shafinta na X a safiyar yau Jumma’a. Ta kuma kara da cewa. a bakin ruwan garin Jabbeh kusa da lardin lardin lantaki mutane 48 aka kashe. Labarin ya bayyana cewa wannan shi ne hari mafi muni a kan sabbin masu iko da kasar Sham tun bayan sun kwace iko da kasar a...
    Kwanaki 29 ke nan da wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutane. An yi garkuwa da Tsiga, wanda tsohon Darakta-Janar na Hukumar Yi Wa ƙasa hidima (NYSC) ne tare da wasu mazauna garin su tara, a wata ranar Laraba. An kama ’yan Pakistan biyu da laifin yin garkuwa a Legas Hukumar Zaɓen Neja ta sanar da ranar zaɓen ƙananan hukumomoni Masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan Janar ɗin da aka sace domin neman kuɗin fansa na Naira miliyan 250m. Wata majiya ta kusa da dangin ta shaida wa wakilinmu cewa, har yanzu ana ci gaba da...