An Umurci Sojoji Su Kawarda ‘Yan Bindiga Daga Kwara Da Niger A Cikin Wata Daya
Published: 24th, April 2025 GMT
Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda.
A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22 a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba.
A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar.
Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda.
Oluyede ya kara da cewa, rundunar soji ta samar da Uniform guda 100,000 yayin da aka ware naira miliyan dubu domin ciyar da sojojin a kowane wata.
A kwanakin baya ne wata kungiyar da aka fi sani da Mahmuda ta bulla a kananan hukumomin Kaiama da Baruten na jihar Kwara yayin da wasu da ba a tantance ba suka kashe mutane bakwai a Ilesha Baruba da ke karamar hukumar Baruten a jihar Kwara ranar Litinin.
COV/ALI RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu
A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.
Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.
Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp