Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren Filato, sun nemi a yi adalci
Published: 6th, April 2025 GMT
Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wasu ƙauyuka na Ƙaramar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato.
Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Ruwi, Manguna, Daffo, Josho da Hurti.
Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniyaShugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana waɗannan hare-hare a matsayin rashin hankali da tausayi.
Ya ce an kashe mutane da dama ciki har da mata da yara, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan hare-hare na barazana ga zaman lafiya da haɗin kan yankin Arewa.
A wata sanarwa da kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a Gombe, Gwamna Yahaya ya bayyana jimaminsa game da wannan mummunan lamari.
Ya jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma gwamnatin Jihar Filato da al’ummarta baki ɗaya.
Gwamnan ya bayyana damuwarsa kan yadda rikici ke ci gaba da addabar yankunan karkara, musamman yadda ake yawan zubar da jinin bayin Allah.
“Rayuwar ɗan Adam abu ce girma da ba za a yi wasa da ita ba. Waɗannan mugayen hare-hare da ake kai wa mutane abin Allah-wadai ne, kuma dole ne a dakatar da su,” in ji Gwamna Yahaya.
Ya yaba da matakin gaggawa da Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya ɗauka bayan faruwar lamarin, da kuma ƙoƙarin jami’an tsaro wajen shawo kan rikicin.
Sai dai ya buƙaci jami’an tsaro da su ƙara himma wajen kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da cewa an hukunta su.
Gwamna Yahaya ya kuma buƙaci a ƙara ƙoƙarin wayar da kan jama’a kan zaman lafiya, haƙuri da fahimtar juna a tsakanin al’umma, musamman tsakanin manoma da makiyaya.
Ya jaddada ƙudirin gwamnonin Arewa na aiki tare wajen kawo ƙarshen rikice-rikice, ta hanyar ƙarfafa tsaro, tattaunawa da aiwatar da manufofin da za su kawo zaman lafiya da haɗin kai.
Ya kuma buƙaci shugabannin al’umma, ƙungiyoyin addinai da na fararen hula da su tallafa wa gwamnati ta hanyar yaɗa sakon zaman lafiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnonin Arewa hare hare Inuwa Yahaya zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Boko Haram Sun Hallaka ‘Yan Zaman Makoki 7, Sun Jikkata Wasu A Borno
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne.
Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin.
A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp