Hamas Ta Yi Allawadai Da Gwamnatin Falasdinawa Kan Masu Goyon Bayanta A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
Published: 8th, April 2025 GMT
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yi tir da gwamnatin Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, saboda dirar mikiyan da ta yi kan Falasdinawa a yankin wadanda suke zanga-zangar beman HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da ta yi a gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Litinin ce, Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, suka rufe shagudansu da harkokin kasuwancinsu da kuma ofisoshinsu don neman HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da suke yiwa yan uwansu kuma yan kasarsu a Gaza.
Majiyar kungiyar Hamas ta kara da cewa wannan dabawa kungiyar wuka a baya ne. Ta ce gwamnatin Falasdinawa a Ramallah tana wa yahudawan HKI aiki, tana taimaka mata wajen kissan falasdinawa a Gaza.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Falasdinawa a yankin
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Tabbatar Da Adalci Ga Falasdinawa Wajen Maido Da Hakkinsu Na Kasa
Dangane da halin da ake ciki game da rikicin Falasdinu da Isra’ila, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, karfin soja ba zai iya samar da zaman lafiya ba, kuma tashin hankali ba zai iya samar da tsaro ba. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen ci gaba da jajircewa a kan tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, da kuma matukar nuna goyon baya ga tabbatar da adalci ga al’ummar Falasdinawa wajen maido da hakkinsu na kasa, da kuma kara azamar warware matsalar Falasdinu tun da wuri ta hanyar samar da cikakkiyar mafita, mai adalci da kuma dorewa.
Guo Jiakun ya ce, kawo karshen rikicin cikin hanzari da samar da dawwamammen zaman lafiya, shi ne babban burin al’ummar Falasdinu da Isra’ila da kuma yankin Gabas ta Tsakiya, kuma wannan aiki ne na gaggawa da ke gaban kasashen duniya. Kasar Sin ta yi imanin cewa, a halin da ake ciki yanzu, ya zama tilas a karfafa tsagaita bude wuta a zirin Gaza, tare da daukar matakin gaggawa domin rage radadin bala’in jin kai a yankin.
Ya ci gaba da cewa, ya kamata kasashen da ke da tasiri na musamman a kan Isra’ila su sauke nauyin da ke wuyansu. Dole ne a aiwatar da ka’idar barin “Falasdinawa su mulki Falasdinu” bisa turbar gaskiya, kuma dole ne a kiyaye hakkin kasar Falasdinu kan batutuwan da suka shafi shugabanci bayan yaki da kuma shirye-shiryen sake gina kasar. Kazalika, a cewarsa, dole ne a ci gaba da bibiyar shawarar “kafa kasashe biyu” ba tare da kakkautawa ba, da samar da karin fahimtar juna da cimma matsaya tsakanin kasa da kasa da kuma yin watsi da duk wani mataki na bangare guda da zai iya yin kafar ungulu a kan “kafuwar kasashe biyu”. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp