Sharhin Bayan Labarai: Amurka Ba Zata Taba Zama Mai Kawo Karshin Yaki A Gaza Ba
Published: 6th, April 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu nay au zai yi magana kan cewa “Amurka ba zata taba zama mai sulhuntawa tsakanin HKI da Falasdinawa ba” wanda ni tahir amin zan karanta.
A dai dai lokacinda rikicin gaza ya zama matsalar ta duniya a halin yanzu, da dama daga cikin masana suna ganin gwamnatin Amurka wacce ta kasance mai goyon bayan HKI na asali ba zata kuma zama mai shiga tsakanin don kawo karshen rikicinta da falasdinawa ba.
Dangane da wannan shafin yanar gizo mai suna “Alkhanadik’ ya rubuta wani sharhi dangane da yakin na gaza a jiya Asabar yana cewa, a dai dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka ta kasance bangare babba a cikin haddasa matsaloli ga al-ummar Falasdinu na lokaci mai tsawo , ba zata kuma, zama a lokaci guda mai shiga tsakani don warware wannan matsalar wacce ta zama rikicin kasa da kasa ba.
Saboda ko way a san cewa wanda ya soma yaki ba zai zama mai kuma shiga tsakanin don samar da zaman lafiya ba.
Hakama kamfanin dillancin labaran ISNA na JMI ya nakalto cewa Donal Trump shugaban kasar Amurka yana son ya zama mai sulhuntawa tsakanin HKI da kuma falasdinawa, a rigimar da aka dauki shekaru fiye da 70 ana yenta, kuma gwamnatocin Amurka da suka shude har zuwa yau suna goyon bayan HKI, idan ba ma gwamnatin Amurka ba, da a halin yanzu babu HKI.
Masana sun kara da cewa gaskiyar al-amarin ita ce, a duk lokacinda Amurka da HKI sun yi maganan sulhuntawa ko kuma magance matsalar falasdinawa to kuwa, sai dai su kara rikita al-amarin Falasdinawa ta wani bangaren ne amma ba zasu taba gyara ba.
Don haka abinda muke gani a halin yanzu, ba bambancin sa da abubuwan da suka faru a baya ba, na tattaunawa a lokacinda ake ruwan wuta a kanku.
HKI tana kisan kiyashi a gaza, tana kuma ci gaba da rusa gidajensu da kuma duk wani gina a gaza, suna kashesu ta hanyar sasu yunwa, duniya tana gani, amma kuma a can washintong wasu suna maganar wai ana kokarin ganin yadda za’a kawo karshen rikicin.
Wannan ba sabon abu bane, an sha yin haka a baya. Na farko a samar da matsaloli sannan a yi amfani da shi, don tursasawa bangaren da ke da rauni don karban sharuddan da suka tsara.
Tun cikin watan Octoban shekara ta 2023 HKI tare da cikekken goyon bayan gwamnatin Amurka ta fara kissan kiyashi a Gaza, inda mafi yawan wadanda ake kashewar mata da yara ne, da kuma sunan kare kanta take wannan kissan. Manufarsu a wannan yakin a fili yake, wanda kuma shi ne share zirin gaza daga Falasdinawa. Don haka labaran da suke fitowa daga washinton a cikin yan kwanakin da suka gabata na cewa tana kokarin ganin an warware matsalar Falasdinawa da HKI, wata dasisa ce ta shirin neman wata kasa ko kuma wurin da zasu kwashi falasdinawa a Gaza, su kaisu can, sannan HKI ta shari zirin na Gaza ta ginawa yahudawan da take kwasowa daga kasashen yamma zuwa yankin gidana zama.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine
Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine
Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne.
Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa na X cewa: “Trump yana wasa, irin wasan gargadi tare da Rasha: Na kayyade mata kwanaki 50 ko 10 … amma ya kamata ya tuna abubuwa biyu: Na daya Rasha ba Isra’ila ba ne ko kuma Iran. Na biyu. duk wani sabon gargadi yana matsayin barazana ne kuma matakin kunna wutar yaki ne. Ba tsakanin Rasha da Ukraine ba, amma tare da kasarsa. Amurka ta nshiga taitayinta!”
Da sanyin safiyar litinin ne shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da rage wa’adin kwanaki 50 da ya sanya a farkon wannan wata na tsagaita bude wuta a Ukraine zuwa tsakanin kwanaki 10 zuwa 12. Ya ce “ba ya ganin wani ci gaba wajen warware rikicin Ukraine” kuma “babu amfanin jira.”