Dole Jama’a Su Marawa Sojoji Baya Don Samun Nasara A Yaƙi Da Ƴan Ta’adda
Published: 2nd, May 2025 GMT
Wata ƙungiyar matasa mai suna “North-East Coalition Against Terrorism” ta yi maraba da Major General Abdulsalam Abubakar, sabon kwamandan yakin Operation HADIN KAI (OPHK), inda ta bayyana cewa tana fatan zaman lafiya ya dawo yankin.
A cikin wata sanarwa da Ismail Mustapha da Sakatare Danlami Bukar suka rattaba hannu, ƙungiyar ta ce Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin babban Hafsan Soja Janar Chris Musa za su ci gaba da matsa lamba kan mayakan.
Ƙungiyar ta gargadi matasa su ƙi tayin shiga ƙungiyoyin da ba su da kyakkyawar manufa. Ta kuma bayyana cewa naɗin sabon kwamandan wani yunƙuri ne na ƙara sabbin dabarun yaƙi. “Ya daɗe yankin Arewa-Maso Gabas bai sami cikakkiyar zaman lafiya ba. Za mu ci gaba da zama a baya har sai dukkan al’umma sun goyi bayan Sojojin don shawo kan waɗanda suka jawo mana wannan rikicin,” in ji ƙungiyar North-East Coalition Against Terrorism
Ta kara da cewa; “Lokaci ya yi da za mu tattara mu goyi bayan Sojoji a ƙarƙashin Janar Chris Musa da sauran shugabannin Sojoji don dawo da zaman lafiya a yankinmu “
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Boko Haram Operation Haɗin Kai
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA