Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna.

 

Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan cuta, amma asalin kudaden sun zarta haka, musamman idan Maleriyar ta yi kamari, za a iya kashe ninki uku ko sama da haka na wannan kudi.

 

Yayin da duniya ke yin wannan biki na ranar Maleriya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nanata cewa, cutar na ci gaba da zama barazana, musamman a yankuna masu fama da zafi, duk da cewa; cuta ce da ake warkewa, sannan kuma tana da rigakafi.

 

Don haka, masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya, sun yi kira da a kara zuba hannun jari, don cimma burin kawar da cutar ba tare da samun mace-mace ba.

 

Shugaban Kungiyar Likitoci na Nijeriya (NARD), Dakta Osundara Tope Zenith, ya jaddada bukatar karfafa tallafin gwamnati, domin kawar da cutar baki-daya.

 

Ya bayyana cutar a matsayin wani gagarumin kalubale ga lafiyar al’umma da ke da matukar illa, musamman ga yara ‘yan kasa da shekara biyar da kuma mata masu juna biyu.

 

Dakta Zenith, ya jaddada illar cutar da kuma yadda take yin tasiri a kusan dukkanin sassan wannan kasa, inda ya bayyana cewa; cutar na ci gaba da yin illa ga kiwon lafiya, wanda kuma hakan ya zama wani babban kalubale ga gwamnati da kuma ma’aikatar lafiya baki-daya.

 

“Maleriya ta yadu a kasar nan, sannan kudaden da ake kashewa a kanta na da matukar yawa, koda-yake ana samun ci gaba wajen kokarin magance ta, duk da cewa; kawar da ita baki-daya na bukatar makudan kudade,” in ji shi.

 

Ya bayyana abubuwa da dama da ke da tasiri wajen yaduwar cutar, wadanda suka hada da ruwan sama, sauyin yanayi, har ma da boyayyun gurare da sauraye ke buya a tsakanin mutane da dabbobi. A cewarsa, wasu nau’ikan kwayoyin cuta na iya zama a cikin hanta har tsawon wata guda, wanda hakan ke haifar da koma baya ko da an samu nasarar magani.

 

Har ila yau, ya kara da cewa; baya ga taimakon likitoci, rashin tsaftar muhalli a tsakanin al’umma, kamar rashin kwatoci ko hanyoyin wucewar ruwa da ciyayi da yawa, na ci gaba da samar wa sauro mafaka, wanda hakan ke kawo cikas wajen kokarin kawar da su.

 

Shugaban na NARD ya shaida wa LEADERSHIP cewa, kudaden da gwamnati ke zubawa wajen yaki da cutar Maleriya, ba za su wadatar ba, sannan kuma ta dogara ne kwarai da gaske a kan kasashen waje da ke bayar da taimako.

 

“Har yanzu, muna dogara da kudade daga cibiyoyi kamar Bankin Duniya (World Bank), Bankin Raya Afirka (African Debelopment Bank) da kuma Asusun Duniya (Global Fund).

 

Gudunmawar da gwamnati ke bayarwa ta yi matukar kadan, in ji shi.

 

Idan ana so a cimma wannan bukata, wajibi ne a kara yawan kudaden da ake kashewa a cikin gida Nijeriya tare da kara wayar da kan al’umma da bunkasa sabbin magungunan cutar Maleriyar da kuma na kwari. Kazalika, dole ne a mayar da hankali kan tsaftar muhalli.

 

“Kawar da cutar Maleriya abu ne mai yiwuwa, amma muna bukatar jajircewa da kuma hadin kai, domin tabbatar da ganin mafarkinmu ya zama gaskiya”, in ji shi.

 

Ana iya kubuta daga wannan cuta ta Maleriya, ta hanyar amfani da gidan sauro, fesa magani bayan kulle daki da kuma amfani da maganin Maleriyar. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta jaddada cewa; shan magani a kan lokaci na iya dakatar da cutar daga yin muni.

 

“Yin gwaji da shan magani a kan lokaci, su ne hanya mafi sauki wajen ceto rayuka”, in ji Hukumar ta WHO, sannan ta yi kira da a ci gaba da zuba hannun jari a rigakafi, magunguna da kuma wayar da kan mutane.

 

A halin da ake ciki yanzu, wakilinmu ya ziyarci daya daga cikin matsugunan da ke cikin babban birnin tarayya Abuja. Mazaunan da ke garin Jikwoyi, sun bayyana wani mummunan labari, inda daruruwan mutane, musamman yara ke rayuwa cikin wani mawuyacin hali, sakamakon wasu kwatoci da suka cika da shara, ruwa ba ya samun hanyar wucewa.

 

Wakilinmu, ya bayyana al’amarin a matsayin abin takaici, inda yara kanana ke wasa a wurin babu takalmi cikin datti, ba tare da la’akari da illa ga lafiyarsu ba.

 

A gida daya, sai ka samu mutane da dama suna amfani da bandaki daya, wanda mafi akasari kwata ta gifta ta ciki, ruwan datti ke kwararowa, sannan ga fanfo ya lalace, abubuwan babu kyan gani.

 

Daya daga cikin mazauna unguwar, Mama Ozioma ta bayyana yadda ta sha fama. “Ban ji dadin zama a nan ba, amma ba mu da wani zabi. Haya a unguwanni masu kyau ya yi mana tsada ni da maigidana, domin kuwa ba za mu iya biya”, in ji ta.

 

Zama a irin wadannan lalatattun unguwanni, na tasiri kai tsaye da yanayin lafiyarsu, musamman ma yara kanana.

 

“Shi yasa, ba za ka taba raba ire-iren wadannan unguwanni da Maleriya ba”, in ji ta. “’Ya’yana suna yawan fama da rashin lafiya, amma ba na iya kai su asibiti. A da ina iya sayen magunguna a wani shagon sayar da magani da ke kusa da mu, amma yanzu maganin da a da nake saya 500, yanzu ya koma 1,500. Ba zan iya ba, ya fi karfina”.

 

Mama Ozioma, da ire-iren ta da dama sun koma amfani da magungunan gargajiya.

 

“Yanzu mun koma amfani da agbo. Muna tafasa gangen mangwaro da na gwanda mu sha. Har sai idan cutar ta yi tsanani ne, nake sayen magani ko kuma na je wajen ma’aikaciyar lafiya,” ta ce, idan ka je wajen ma’aikaciyar lafiya, sai kashe akalla Naira 10,000 a kan kowane yaro, kama daga kudin gwaje-gwaje zuwa na magani.

 

Da aka tambaye ta game da amfani da gidan sauro ta bayyana cewa, “Gidan sauro guda daya ba zai iya daukar yara biyar ba. Sannan, ko da muna da guda dayan, yara za su yayyaga shi ne a wajen wasa.”

 

Mummunan halin da ake ciki a Jikwoyi, na nuni da irin bakin talaucin da ake fama da shi a birane, musamman ta fuskar karancin samun lafiya da kuma tashin gwauron zabin da magunguna suka yi.

 

Yayin da Nijeriya ke fitar da alluran rigakafin cutar Maleriya zuwa wasu jihohi da aka kebance, mazauna wasu yankuna a babban birnin tarayya Abuja, na ci gaba da dogaro ne a kan magungunan gargajiya, saboda rashin hali.

 

Har ila yau, binciken LEADERSHIP ya nuna cewa; ana biyan kudin ganin likita a kusan galibin manyan asibitocin babban birnin tarayya Abuja a kan Naira 2,200, yayin da ake gwajin Maleriya kuma a kan Naira 2,000.

Wani likita a daya daga cikin manyan asibitocin, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa; a halin yanzu ba a ba da maganin Maleriya kadai, sai an hada allura. Idan aka hada da kudin ganin likita da sauran gwaje-gwaje, jimillar kudaden da ake kashewa wajen maganin Maleriyar, ya doshi Naira 17,000.

A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta ayyana cutar Maleriya ba wai a matsayin matsalar kiwon lafiya kadai ba, har ma da matsalar tattalin arziki da ci gaba tagayyar al’ummar kasar, inda ta bukaci a gaggauta daukar matakan dakile cutar.

Wannan ne yasa, ma’aikatar ta kaddamar da wani kwamitin shawara kan kawar da cutar Maleriyar a Nijeriya (AMEN), a shekarar 2024.

Ministan lafiya, Farfesa Ali Pate ya kaddamar da ‘AMEN’ a matsayin wani gagarumin yunkuri na tunkarar matsalar da ta jima tana cutar da lafiya da kuma tattalin arzikin ‘yan Nijeriya.

“Maleriya na ci gaba da yin illa ga kasarmu, wanda ba za mu lamunci hakan ba. Nijeriya ce ke da kashi 27 cikin 100 na masu fama da ita a duniya da kuma kashi 31 cikin 100 na mace-macen da ake samu. A shekarar 2022 kadai, sama da yara 180,000 ‘yan kasa da shekara biyar suka mutu, sakamakon wannan cuta,” in ji shi.

Farfesa Pate, ya kuma jaddada makudan kudaden da wannan cuta ta Maleriya ke lashewa, inda ya yi kiyasin ana asarar kimanin Dala biliyan 1.1 a duk shekara.

Ya kara da cewa, “Wannan ya wuce batun matsalar lafiya kadai, domin kuwa yana dakile samar da yawan ayyuka, yana kuma kara zurfafa talauci a tsakanin ‘yan kasa,” in ji shi.

 

Ministan lafiyar ya yi kira ga jama’a kan kowa ya sanya hannu a ciki, inda ya bukaci shugabannin gargajiya da na addini su kawo dauki wajen wayar wa da al’umma kai ta hanyar amfani da gidan sauro da magungunan kashe kwari da kuma allurar rigakafi.

 

Nijeriya ta samu alluran rigakafin cutar Maleriya kimanin miliyan daya a shekarar 2024, inda shirin ya fi karkata kan kananan yaran da suka fi saurin kamuwa da cutar. An tura alluran rigakafin jihohin Kebbi da Bayelsa, wadanda aka gano sun fi yawan masu dauke cutar a Nijeriya.

 

Babban Daraktan Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA), Dr Muyi Aina ya ce, a wani mataki na shirin, hukumar ta yi wa yara 101,158 allurar rigakafin cutar a jihohi biyu, inda ya ce an shigar da shirin cikin jadawalin rigakafin da ake da su da kuma shirye-shiryen wayar da kan jama’a, domin fahimtar shirin da kuma sanin ingancinsa.

 

Ya yarda da cewa, akwai kura-kurai da aka samu wajen kawo allurar rigakafin da kuma sabon tsarin da aka gabatar, a nan ma an samu kalubale.

 

Don haka, a cewar tasa, “Muna bukatar koyon izina daga abubuwan da suka gabata, duk da samun karancin kayayyakin da muka gabatar,” in ji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: da cutar Maleriya kawar da cutar da ake kashewa wannan cuta

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Siyasa Na Gwagwarmaya Ne Kadai Wajen Neman Mukami Ba Wai Don Talakawa Ba — Bafarawa

“Siyasar da na sani ba ita ce abin da ke faruwa a yau ba. Siyasar da na sani ita ce gwagwarmayar muradun jama’a don tabbatar da cewa suna da kyakkyawar rayuwa a duk fannoni kamar ilimi, ruwa, kiwon lafiya, da sauransu. “Na kasance a siyasa tsawon shekaru 48 da suka gabata,” in ji shi.

Ya bayyana yanayin siyasa a matsayin wanda ke cike da rudani da son kai, yana mai jaddada cewa ‘yan siyasa da talakawa sun rikice.

“Saboda wannan, akwai rudani ga masu nema da kuma wadanda ake nema. Masu neman suna makancewa, ba su da imani ko tausayi. Manufarsu kawai ita ce tabbatar da matsayi a gare su. A halin yanzu, talakawa sun tsunduma ciki yunwa, talauci, da jahilci, don haka komai yana cikin rudani,” in ji Bafarawa.

Tsohon gwamnan ya kuma nuna matukar damuwa game da karuwar jahilci a tsakanin matasa, musamman a arewacin Nijeriya, yana mai gargadin cewa makomar yankin na cikin hadari.

“Duk lokacin da kuka cusa mutane cikin jahilci ta hanyar hana su ilimi, kun gama da su. A nan arewa, a gaskiya, kusan kashi 70 cikin 100 na matasanmu ba su da ilimi. Ta yaya wata kasa ko yanki za ta ci gaba ba tare da ilimi ba?” ya tambaya.

Bafarawa ya kare talakawa masu jefa kuri’a da ke karbar kudi a lokacin zabe, yana mai cewa mawuyacin halin tattalin arziki da suke fuskanta ya sa ba su da wani zabi.

A cewarsa, taimakon Allah ne kadai zai iya ceto Nijeriya daga kalubalen da take fuskanta a yanzu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Siyasa Na Gwagwarmaya Ne Kadai Wajen Neman Mukami Ba Wai Don Talakawa Ba — Bafarawa
  • Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Sufurin Miliyoyin Fasinjoji A Ranar Farko Ta Hutun ‘Yan Kwadago
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasar Oman Ce Ta Bukaci Dage Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka
  • An dage tattaunawa ta hudu da aka shirya gudanarwa tsakanin Iran da Amurka
  • Gwamnatin Kano Zata Kashe Naira Miliyan Dubu 51 Don Aiwatar Da Ayukka
  • Al’umma Sun Shiga Fargaba Yayin Da Ake Zargin ‘Yan Bindiga Sun Kashe Limamin Da Suka Sace A Zamfara
  • Dakarun IRGC Na JMI Sun Kaddamar Da Sabon Kwale-Kwale Mai Cilla Makamai Masu Linzami
  • Syria: Adadin Wadanda Aka Kashe A Rikicin Bangaranci Sun Kai 70
  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu gobe Alhamis