A Yau Asabar Ne Ake Bude Tattaunawa A Kasar Oman Akan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
Published: 12th, April 2025 GMT
Tun da safiyar yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka.
Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran.
A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi, ministan harkokin wajen Iran ya yaba da matsayar Oman akan batutuwa da dama su ka shafi wannan yankin na yammacin Asiya.
Daga cikin masu yi wa ministan harkokin wajen na Iran rakiya da akwai mataimakinsa a fagen dokokin kasa da kasa Kazim Garib Abadi, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ambata.
Da marecen yau bayan la’asar ne dai za a yi tattaunawar ta Oman.
Iran da Amurka za su yi tattaunawa ne ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman ba ta gaba da gaba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ministan harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka Game Da Batun Haraji
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin cewa, babu wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a baya-baya nan, haka kuma bangarorin biyu ba su cimma wata yarjejeniya ko su tuntubi juna game da batun haraji ba. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp