Iran Ta yi Tir Da Sanarwar Da Kungiyar G7 Ta Fitar Kan Maido Mata Da Takunkumi.
Published: 3rd, October 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen ta Iran tayi Allah wadai da da irin bayanan da kungiyar G7 ta yi game da shirin nukiliyarta, kuma ta bayyana shi a matsayin munafunci da kuma canza gaskiya ,
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il baghae ya fadi cewa kungiyar G7 ta amince da matakin da ya sabama doka da rashin Adalaci da Amurka da kasashen turai 3 suka dauka na sake dawo da takunkumi kwamitin tsaro na majaliar dinkin duniya kan kasar iran, matakin da ya sabama dokar kasa da kasa.
Haka zalika ya soki kungiyar ta G7 na yi gum da baki kan shirin nukiliya Isra’ila ,yace kasashen ba su da hurumin da za su iya yin lecture kan dokokin kasa da kasa , zaman lafiya da tsaro idan aka yi la’akari da halin da suke ciki na rashin gaskiya da rikon amana.
Kasashen na G7 sun yi kira ga dukkan mambobin majalisar dinkin duniya da su yi aiki da takumkumi kuma sun yi Alkawarin basu goyon bayan dari bisa dari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Duniya Sun yi Tir Da Matakin Da Isra’la Ta Dauka Kan Tawagar Sumud Flotilla. October 3, 2025 Kasar Rasha Ta Jaddada Aniyar Ganin Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zata Gudana Cikin Sauri October 2, 2025 Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Jaddada Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Makiya October 2, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Jirgin Ruwa Da Ke Hulda Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila October 2, 2025 Hukumar “UNRWA” Ta Ce: Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Kashe Falasdinawa 100 Akalla Kowace Rana October 2, 2025 Masar Ta Ce: Tana Goyon Bayan Kawo Karshen Yakin Sudan Domin Wanzar Da Zaman Lafiya A Kasar October 2, 2025 Duniya na tir da farmakin Isra’ila kan jirgin ruwan ‘yan agaji zuwa Gaza October 2, 2025 Colombia ta kori jami’an diflomasiyyar Isra’ila October 2, 2025 DRC : An yanke wa Joseph Kabila hukuncin kisa kan cin amanar kasa October 2, 2025 Isra’ila ta kashe Falasdinawa 44 a ranar Laraba October 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23
Gwamnatin kasar ta DRC da kuma kungiyar ‘yan tawaye ta M23 sun rattaba hannu akan wasu takardu da su ka kunshi yadda za a kai ga samun zaman lafiya mai dorewa a gabashin kasar.
A jiya Asabar ne dai bangarorin biyu su ka rattaba hannu akan takardun a birnin Doha na kasar Qatar domin kawo karshe fadace-fadacen da ake yi a gabashin kasar da ya ci rayukan dubban mutane da kuma tilastawa wasu yin hijira a cikin shekara daya kacal.
Karamin ministan harkokin wajen kasar Katar Muhammad Bin Abdulaziz Al-Khulaifi ya ce, rattaba hannu da bangarorin biyu su ka yi share fage ne zuwa ga zaman lafiya.
Haka nan kuma ya ce; Shi zaman lafiya ba a iya tilasta shi ta hanyar amfani da karfi,sai dai ta fahimtar juna.”
Sai dai kuma duk da cewa ana tattaunawar zaman lafiya a tsakanin banbarorin biyu a kasar Katar, fadan da ake yi a can gabashin DRC bai tsaya baki daya ba. A ranar juma’ar nan da ta shude ma dai an kashe mutane 28 a wani hari da kungiya mai ikirarin jihadi ta kai a Kivu ta Arewa.
A cikin watan Janairu na wannan shekarar ne dai kungiyar ta M23 ta shimfida ikonta a cikin birnin Goma da shi ne mafi girma a gabashin kasar, daga can kuma ta kame yankunan Kivu ta Arewa da ta kudu.
Gwamnatin Kinshasha dai tana tuhumar makwabciyarta Rwanda da taimakawa kungiyar ta M23 da makamai da kuma mayaka. Sai dai Rwanda ta sha musanta zargin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli November 16, 2025 An Amince Da Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci