Leadership News Hausa:
2025-11-18@13:57:04 GMT

PSG Ta Doke Barcelona Har Gida A Gasar Zakarun Turai

Published: 2nd, October 2025 GMT

PSG Ta Doke Barcelona Har Gida A Gasar Zakarun Turai

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG, ta doke Barcelona a wasan mako na 2 na gasar Zakarun Turai a wasan da suka buga a filin wasa na Luis Companys.

Ferran Torres ne ya fara jefa ƙwallon a ragar PSG a minti na 19 da fara wasan, amma gab da tafiya hutun rabin lokaci Senny Mayulu ya farkewa baƙin ƙwallonsu, yayin da Goncalo Ramos ya ci ƙwallon ƙarshe kuma wacce ta bai wa PSG nasara a mintin ƙarshe na wasan.

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP, Sun Kama Wasu Da Miyagun Ƙwayoyi Li Qiang Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Sabon Firaministan Algeria

Da wannan nasarar da PSG ta samu ya sa ta koma matsayi na 3 a teburin gasar Zakarun Turai yayin da Barcelona ta koma matsayi na 16 bayan ta haɗa maki uku a wasanni 2 da ta buga.

PSG za ta ziyarci Bayern Leverkusen a wasan mako na 3 a ranar 21 ga watan Oktoba, yayin da Barcelona za ta karɓi baƙuncin Olympiacos ta ƙasar Girka a wasanta na gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Barcelona Gasar Zakarun Turai ƙwallo

এছাড়াও পড়ুন:

Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa

An zaɓi tsohon Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati, Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa a yayin babban taron jam’iyyar da aka gudanar a birnin Ibadan na Jihar Oyo a ranar Asabar.

PDP ta ce Barista Kabiru Tanimu Turaki, ya yi nasarar ce akan Sanata Lado Ɗan Marke da ƙuri’u sama da dubu ɗaya da ɗari biyar, da wakilai 3, 131 suka halarta.

PDP za ta sake farɗaɗowa idan shugabanninta suka cire girman kai — Anenih Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP

Hakan dai na zuwa ne yayin da jam’iyyar ta PDP ta dakatar da Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar, yayin da gwamnonin Adamawa da na Fulato suka ƙalubalanci matakin suna masu cewar matakin ka iya ƙara rura wutar rikicin da jam’iyyar ke ciki.

Barista Kabiru Tanimu Turaki, ya samu ƙuri’u 1,516 daga cikin ƙuri’u 1, 834 da aka kaɗa a yayin zaɓen.

A kujeru biyu ne dai aka yi zaɓe a babban taron jam’iyyar na ƙasa, yayin da dama daga sauran kujerun shugabancin jam’iyyar kuma aka yi maslaha a tsakanin ’yan takara wanda daga bisani aka kira wakilai daga jihohi suka kaɗa ƙuri’unsu kamar yadda dokar hukumar zaben Najeriya ta tanada.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana
  • Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas
  • Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya
  • Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari
  • ’Yan ta’adda sun yi garkuwa da dalibai 25 a Kebbi
  • ’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi
  • Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya
  • Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa
  • Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain
  • Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi