Sudan Ta fitar da Gargadin Ambaliyar Ruwa a Jahohi 5
Published: 30th, September 2025 GMT
Sudan ta fitar da gargaɗin gaggawar samun ambaliyar ruwa a jihohi biyar bayan matakin ruwa a Kogin Nilu ya ƙaru kamar yadda rahoton gidan jaridar gwamnati Suna ya ruwaito.
Rahotanni sun danganta ƙaruwar matakin ruwa da babban dam ɗin Ethiopia da aka buɗe a wannan watan.
Ma’aikatar nomar rani ta Sudan ta sanar da gargadin ne a ranar 28 ga watan Agusta, inda ta ce ya shafi jihohin Khartoum da River Nile da White Nile da Sennar da kuma Blue Nile.
Ma’aikatar ta yi gargaɗin cewa ruwa na iya mamaye gidaje da gonaki, tare da kira ga ɗaukar matakan gaggawa.
Farfesa Abbas Sharaky na jami’ar Cairo, masani a fannin ƙasa da albarkatun ruwa, ya bayyana cewa ƙaruwar matakin ruwa a Nilu sakamakon kuskuren ɗan adam ne da ya shafi babban dam na Ethiopia.
Sharaky ya ce injinan da ke kula da tafiyar da ruwan dam huɗu sun gaza aiki, wanda ya sa Ethiopia ta kasa shawo kan ruwan da kuma tura ruwan da ya wuce gona da iri zuwa Sudan.
Ethiopia a jiya ta ƙaryata zargin, inda ta ce dam ɗin ya taka muhimmiyar rawa wajen rage illar ambaliyar.
A kowacce shekara, matakin ruwa a Kogin Nilu yana ƙaruwa a watan Agusta saboda ruwan sama mai yawa a tsaunukan Ethiopia.
BBC/Hausa
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Baliya matakin ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Afrika ta Kudu Ta yi Gargadi Game Da Duk Wani Yunkuri Na Fitar Da Falasdinawa Daga Yankin Gaza
Ministan harkokin wajen kasar Afrika ta kudu Ronald lamola a jiya a joharnesbourg yayi gargadi game da kwaso falasdinawa da aka yi a baya bayan nan yana nuna irin yunkurin da ake yi na tilasta musu barin yankin gaza, inda ya bayyan shirin a matsayin wani bangare na shirin korar falasdinawa daga gidajensu.
Pretoriya ta fitar da sanarwa na kokarin kwashe falasdinawa daga yankin Gaza zuwa kasar Afrika ta kudu, yayi gargadin cewa wannan matakin yana iya zama wani bangare ne na shirin iyakoki don tarwatsa falasdinawa da karyar canza musu wuri don basu taimakon Agaji
Minsitan harkokin wajen na afrika ta kudu ya bayyanawa manema labarai cewa batun shirin ajandar iyakoki na dauke falasdinawa daga gaza zuwa yankuna daban daban na duniya, yace Afrika ta kudu bata bukatar wani jirgi ya sake sauka a kasarta domin afili yake wani shiri ne na korar falasdinawa daga gaza da gabar yammacin kogin jodan
Yanzu haka dai jirage biyu ne suka sauka a afrika ta kudu dauke da daruruwan falasdinawa
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza November 18, 2025 Mataimakin Shugaban Iran Na Daya Ya Gana Da Prime Ministan Rasha A Birnin Mosko November 18, 2025 Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin November 18, 2025 Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF November 18, 2025 MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza November 18, 2025 Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci