Yau 29 ga wata, an gudanar da bikin karfafa hadin gwiwa tsakanin babban rukunin gidajen rediyo da talibiji na Sin wato CMG, da mabambantan bangarori na yankin Hong Kong. Jagoran yankin musamman na Hong Kong John Lee Ka-chiu ya bayyana cewa, idan aka waiwayi tarihi, gwamnatin Hong Kong da CMG sun kasance suna hadin gwiwa sosai da juna.

Sun yi hadin gwiwa da juna a fannonin ba da rahotannin manyan bukukuwa, da fadakar da al’ummu manufofi masu muhimmanci, da daidaita al’amura na gaggawa. Bikin karfafa hadin gwiwa na yau ya alamanta sabon babin hadin gwiwar CMG da al’ummar Hong Kong. Jerin matakan da aka dauka, ba ma kawai sun dace da manufofin kasa ba, sun kuma amsa bukatun al’ummar Hong Kong, tare da dacewa da burin jama’a na samun kyakkyawar rayuwa.

 

A lokacin da ake bikin cika shekaru 76 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin, a yau 29 ga Satumba, CMG ta kuma kaddamar da nune-nunen ingantattun shirye-shirye a Hong Kong, inda za a nuna shirye-shirye 9 masu kyau. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: hadin gwiwa

এছাড়াও পড়ুন:

Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Amnesty ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga.

CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas

Ƙungiyar ta ce bincikenta ya gano cewar ’yan bindigar sun kai hari ne da misalin ƙarfe 5 na safiya, inda suka tilasta wani ma’aikacin makarantar ya nuna musu ɗakin kwanan daliban mata, sannan suka yi awon gaba da su.

Amnesty ta ce wannan harin ya sake nuna cewa, “gwamnatin Tinubu ba ta da wani ingantaccen tsari na kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga, duk da matakan da ake ce an ɗauka, domin babu wani gagarumin sauyi da aka gani a ƙasa.”

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin ceto ɗaliban cikin aminci, tare da gano musabbabin yawaitar sace-sacen mutane a sassan ƙasar, abin da ta ce yana barazana ga ilimi da zaman lafiyar al’umma.

Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da sace ɗaliban

A nata ɓangaren, gwamnatin Najeriya ta bayyana tsananin damuwa kan harin, inda ta ce ta bai wa jami’an tsaro umarnin gano da ceto ɗaliban cikin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai, Muhammad Idris ya fitar, ya ce gwamnati za ta tabbata an kamo waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukunci.

Ya ƙara da cewa gwamnati na tare da iyaye da ’yan uwan waɗanda abin ya shafa, tare da jaddada cewa za a yi duk wani abu mai yiyuwa domin ganin yaran sun koma gida cikin aminci.

Za mu dawo da duk ɗaliban da aka sace —Jami’an Tsaro

Wata rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da ’yan sanda, na ci gaba da laluben ɗaliban bayan ’yan bindiga sun awon gaba da su.

Da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar ’yan matan, inda bayanai ke nuni da cewa an sace ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin shugaban makarantar da wani maigadi kana suka jikkatar da dama.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 
  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
  • An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing
  • Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO}
  • Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
  • Na’im Dassim: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci
  • ’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II ya ziyarci Faruruwa, ya buƙaci a tsaurara tsaro
  • Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16
  • An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka
  • Yadda Za Ku Gyara Kanku