Gwamnan Kano ya kafa sabbin hukumomi 4
Published: 25th, April 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki guda huɗu da suka kafa muhimman hukumomi domin ƙarfafa tsarin gudanarwa na jihar da kuma haɓaka ci gaba mai ɗorewa.
Waɗannan dokokin za su samar da Hukumar Kare Hakkokin Jama’a ta Jihar Kano (KASPA), Hukumar Kula da Tallace-tallace da Rubuce-rubuce ta Jihar Kano (KASIAA), Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Zamani ta Jihar Kano (KASITDA), da kuma Hukumar Bunƙasa Ƙananan Kasuwanci da Matsakaita ta Jihar Kano (KASMEDA).
Gwamna Abba, ta bakin mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana muhimmancin waɗannan dokokin wajen ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire, tallafa wa ƙananan kasuwanci, tsara tallace-tallace, da inganta kare hakkin jama’a da samar da ayyuka.
Ya jaddada cewa waɗannan hukumomi za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi, jawo jari, da kuma aiwatar da tsare-tsaren gwamnati yadda ya kamata, wanda ya nuna hangen nesansa na sanar da Kano ta zamani da bunƙasa tattalin arziki.
Ƙarin ’yan Najeriya za su shiga talauci nan da 2027 — Bankin Duniya ’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a NasarawaGwamnan ya yi gargaɗi game da keta waɗannan sabbin dokokin, yana mai cewa za a hukunta duk wanda ya karya su da tsauraran matakai domin tabbatar da bin doka da oda.
Kafa waɗannan hukumomi ya nuna ƙoƙarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da gyara cibiyoyin gwamnati, inganta gudanarwa, da kuma sanya Kano a matsayin cibiyar da ta fi fice a fannin ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci, da ci-gaba mai ɗorewa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tattalin Arziki ta Jihar Kano
এছাড়াও পড়ুন:
NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da sake haka sabbin rijiyoyin man fetur guda hudu yankin Kolmani na jihar Bauchi, kamar yadda Darakta a kamfanin, Yusuf Usman ya tabbatar.
Daraktan ya kuma sake jaddada aniyar kamfanin ta ganin ya fara aikin hako danyen man fetur a Arewacin Najeriya.
Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres Tallafin matar Tinubu na N1bn ga ’yan gudun hijirar Binuwai ya bar baya da kuraYa bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna a rana ta biyu ta taron tattaunawa tsakanin gwamnati da jama’a da Gidauniyar Tunawa da Ahmadu Bello ta shirya.
Daraktan ya ce, “Ya zuwa yanzu, NNPCL ya tono sabbin rijiyoyin danyen man fetur guda hudu a yankin Kolmani na jihar Bauchi, kuma yan kan aikin tantance fasahar da ta fi dacewa a yi aiki da ita a mataki na gaba a aikin.
“A wani yunkurinmu kuma na taimaka wa shirin Shugaban Kas ana komawa amfani da ababen hawa masu amfani da makamashin iskar gas a maimakon man fetur, yanzu haka ana can ana aikin gina tashoshin canza motoci zuwa masu amfani da gas na CNG da LNG,” in ji shi.
Ya ce da zarar an kammala aikinsu, ana sa ran tashoshin za su taimaka wajen bunkasa samuwar gas din kuma cikin sauki a Arewacin Najeriya.
Yusuf ya kuma zayyana wasu muhimman ayyuka da nasarorin da kamfanin ya samu a Arewacin Najeriya da ma sauran sassan kasar a karkashin mulkin Shugaban Kasa Bola Tinubu.