Jigawa Za Noma Rabin Shinkafa Da Ake Amfani Da Ita A Nigeria Nan Da 2030
Published: 25th, April 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ce gwamnatinsa na shirin bayar da gudunmawar kashi 50 na shinkafar da Najeriya ke bukata nan da shekara ta 2030.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar tawagar hukumar tattara kudaden shiga da kasafi (RMAFC) karkashin jagorancin shugaban kwamitin inganta kasafin kudi da kasafin kudi, Ambasada Desmond Akawor, yayin ziyarar ban girma da suka kai a gidan gwamnati dake Dutse.
Ya bayyana cewa, suna noman shinkafa sau biyu a shekara, inda ya nuna cewa, a shekarar 2024 kadai, sun noma sama da hekta 200,000 na shinkafa.
Ya yi nuni da cewa, a bana, suna son noma sama da hekta 250,000 wanda a shekarar 2030, burinsu ya kai kadada 500,000.
Malam Umar Namadi ya ce, a irin takun da suke tafiya za su cimma hakan cikin sauki.
“Babban burinmu shi ne mu ba da gudummawar metric ton miliyan 3.6 na shinkafa kowace shekara don noman shinkafar Najeriya – wanda ke wakiltar kusan kashi 50% na abin da al’ummar kasar ke bukata. Muna da kasa, jama’a, da siyasa don ganin hakan ta tabbata.”
Gwamna Namadi ya ce har yanzu noma shi ne jigon tattalin arzikin Jigawa, inda kusan kashi 85% na al’ummarta ke tsunduma a wannan fanni, inda ya ce gwamnatinsa ta samu nasarorin tarihi a harkar noman rani a yankunan da ba su da yawa a jihar.
Dangane da tallafin albarkatun kasa, gwamnan ya bayyana irin ma’adinan da ba a yi amfani da su a Jigawa ba, ciki har da mai, amma ya bayyana yadda gwamnati ke taka-tsantsan wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro.
Tun da farko, shugaban tawagar RMAFC ya shaida wa gwamnan cewa ziyarar na daga cikin ayyukan da kwamitin ya ba su na tantance ayyukan da suka dace a matakin jihohi ta hanyar ware kudaden shiga na musamman na kasa da kashi 1.68 cikin 100 da nufin karkatar da tattalin arzikin Najeriya, tare da mai da hankali kan noma, yawon bude ido, da ma’adanai masu inganci.
Ya ci gaba da cewa kwamitin ya yaba da yadda aka fara gabatar da jawabai da ziyarce-ziyarcen wuraren da aka fara yi, musamman irin abubuwan da suka shafi albarkatun kasa a jihar, kuma za su ci gaba da duba harkokin noma tare da baiwa gwamnan tabbacin tantance gaskiya.
Ya kuma jaddada muhimmancin amfani da albarkatun kasa domin bunkasar tattalin arziki.
KARSHE/USMAN MZ
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno
Wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya kashe aƙalla mutum 26, ciki har da mata da yara a kan hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da motoci suka tayar da bama-baman da aka ɗana a gefen hanyar, da ya rutsa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida.
Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47 An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da PortugalMajiyoyi, ciki har da wani babba soja, sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu da harin na baya bayan da safiyar ranar Talata.
Sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta tafiya Gamboru Ngala ne daga Rann lokacin da suka isa inda ‘yan ta’addan Boko Haram suka ɗana bam ɗin.
Bayanai sun ce baya ga mutum 26 da suka mutu, ƙarin mutum uku sun ji munanan raunuka.
“Mun tura wasu masu ba da agajin gaggawa inda lamarin ya auku domin kwashe mutane tare da tabbatar da tsaron sauran fararen-hula a wurin,” kamar yadda wata majiyar sojin da ba ta yarda a bayyana sunanta ba ta shaida wa Anadolu.
Ali Abass, wani ganau wanda ke tafiya a kan hanyar a lokacin da lamarin ya auku, ya ce sojojin da ‘yan sa-kai sun kai waɗanda suka jikkata wani asibiti. Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ‘yan’uwansa na cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Harin yana zuwa ne yayin da hare-hare ke ƙara ƙaruwa a yankin Tafkin Chadi, inda ‘yan ta’addan Boko Haram ke ƙara ƙaddamar da hare-haren bama-bamai da kwanton-ɓauna kan motocin fararen-hula da na sojoji.
An ba da rahoton hare-hare irin wannan a ranakun 21 ga watan Maris da 12 ga watan Afrilu. Kawo safiyar ranar Talata dai, jami’an tsaro a Borno ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba.