WHO: Masu Ciwon Koda 400 A Gaza Sun Mutu Saboda Rashin Magani
Published: 23rd, April 2025 GMT
Hukumar lafiya ta duniya (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu fama da wannan cutar.
Hukumar lafiyar ta duniya ( w.h.o) ta kuma yi ishara da yadda ‘yan mamaya su ka lalata bangarorin da suke kula da cutuka na musamman a cikin asibitoci.
Ita ma hukumar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa; masu fama da cutar koda a yankin suna fama da matsaloli na rashin Magani, kuma daruruwa daga cikinsu sun mutu saboda hakan.
Haka nan kuma ta yi ishara da yadda mutane 400 daga cikinsu su ka rasu, da hakan yake nufin kaso 40% na adadin masu wannan cutar.
A gefe daya, ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinu ta yi tir da yadda ‘yan mamaya su ka kai wa asibitin “Durrah” na yara hari a gabashin birnin Gaza.
Haka nan kuma hukumar kiwon lafiyar ta Gaza, ta tabbatar da cewa hare-haren da ‘yan mamayar su ka kai wa dakin da yake kula da marasa lafiya na musamman a cikin asibitin kananan yaran, da kuma tashar samar da wutar lantarki a cikin asibitin.
Sanarwar hukumar lafiya ta Gaza ta ce, baya ga hana shigar da abinci da magani da ‘yan mamayar suke yi, suna kuma hana Falasdinawa ci gaba da rayuwa. Ita kuwa hukumar agaji ta “Red-Crecent” ta bayyana cewa; ‘Yan mamaya sun tafka laifukan yaki da su ka hada da kashe masu aikin agaji a cikin watan Maris.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hukumar lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji kuskure ne — Janar Chibuisi
Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa kuskure ne abin da jami’anta ke yi na cin zarafi da cin zalin fararen hula saboda sun sanya kayan sojoji.
Shugaban Sashen Hulɗar Sojoji da Fararen Hula na rundunar, Manjo-Janar Gold Chibuisi, bayyana cewa rundunar tana hukunta duk jami’inta da aka kama da laifin cin zalin farar hula saboda sanya kayan sojoji.
Ya ce duk da haka doka ta haramta wa fararen hula sanya kayan sojoji ba bisa ka’ida ba, kuma laifi ne da zai iya kai su gidan yarin.
Manjo-Janar Gold Chibuisi, ya ci gaba da cewa doka ba ta ba ta ba sojoji ikon hukuntawa balantana cin zalin masu aikata hakan ba. Sai kuma ta ba su ikon kama masu sojan gona da kayansu, kuma an ba sojoji horo a kan kama masu aikata hakam, su miƙa shi ga ’yan sanda domin gurfanarwa a gaban ƙuliya.
Aminu Bayero ya naɗa Sanusi a matsayin Galadiman Kano NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”“Duk waɗannan abubuwan — na cin zalin da cin zarafin da sojoji ke yi wa masa sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba — ba daidai ba ne. Muna kuma wayar da kansu a game da hakan, sa’annan duk sojan muka samu hujja a kansa kuma, muka yi masa hukunci mai tsanani,” in ji shi.
‘Sanya kaya soja haramcin ne ga fararen hula’Sai dai kuma Manjo-Janar Gold Chibuisi ya yi gargadi ’yan Najeriya su guji sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa mutunta kayan sojo wani muhimmin sashi ne na ƙarfafa tsaron ƙasa.
Ya jaddada cewa yin amfani da kayan aikin soja ba bisa ƙa’ida ba ga mutanen da ba su da izini ya saɓa wa doka kuma yana taimakawa ayyukan laifi, yana mai cewa bin irin wannan shawarar zai samar da yarda tsakanin sojoji da jama’a.
Ya yi wannan gargaɗin ne a Abuja a ƙarshen mako a wani taron tattaunawa da ’yan jarida, inda ya ce, “Sanya kayan sojoji ga mutumin da ba soja ba ya saɓa wa dokar ƙasa. Idan kai ba soja ba ne ko jami’in tsaro, yin amfani da unifom ɗinsu — ko kana son sa ko ba ka so — laifi ne.”
Chibuisi ya jaddada cewa dole ne a mutunta doka don kiyaye mutunci da tsaron rundunonin soji, yana mai gargadin cewa masu aikata laifin na iya fuskantar ɗauri a kurkuku.
“Idan kuna son aikin soja, ku shiga aikin soja. Kada ku saka kayanmu idan ba a cikinmu kuke ba,” in ji shi.
Game da haɗarin tsaro da ake tattare da sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba, Chibuisi ya bayyana cewa masu aikata laifuka na ƙara amfani da kakin soja don aikata laifuka, wanda ya sa ya zama da wahala ga fararen hula da hukumomin tsaro su gane sojojin gaske da na bogi.
Ya ce, “A halin yanzu, akwai ’yan fashi da yawa da ke amfani da kayan soji don aikata laifuka. Idan mutane suka ci gaba da yin ado da kayan sojoji, ta yaya za ku bambance tsakanin ɗan fashi da sojan gaske?”
Ya yi kira ga iyalai da al’ummomi da su taimaka wajen wayar da kan jama’a daga matakin gida.
“Idan wani da kuka sani ba ne ya fito sanye da ku ce masa, ‘Dakata, yau ka shiga aikin soja, cire wannan abin mana.’ Ka guji a kama ba.”
Janar din ya ci gaba da bayanin cewa an horar da sojoji don kama fararen hula da aka samu sanye da kayan soja kuma a miƙa su ga ’yan sanda don gurfanar da su a gaban kotu.
Ya kuma jaddada mahimmancin hana aikata laifin kafin ya faru: “Wani gefen shi ne sojojinmu su yi abin da ya dace idan sun ga haka, ɗayan gefen kuma shi ne fararen hula kada su yi hakan kwata-kwata.”
Yayin da yake bayyana bambanci tsakanin Najeriya da sauran ƙasashe a kan wanna batu, Manjo-Janar Chibuisi ya ƙara da cewa, “Nan ba Amurka ba ce. Ba za ku ce saboda fararen hula na sanya kayan sojoji a Amurka, a nan ma dole ya kasance haka. Ƙari ga haka, ƙalubalen da muke fuskanta a nan, ba na tunanin suna da su a Amurka.”