Aminiya:
2025-07-31@02:14:10 GMT

Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro

Published: 23rd, April 2025 GMT

Ƙungiyar shugabannin majalisun jihohin Nijeriya ta yi tur da matsalolin tsaron da suka addabi jihohin Filato, Borno, Binuwai, Neja, da kuma Kwara a baya-bayan nan.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ɗauki matakan gaggawa domin daƙile bala’in da jihohin a kwanan nan suka tsinci kansu a ciki.

 Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Ibadan da ke Oyo mai dauke da sa hannun shugabanta, Adebo Ogundoyin.

Ya bayyana cewa kashe-kashen dubunnan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba ya janyo musu asarar gidajensu, da dukiyoyinsu, yana haifar musu da tashin hankali.

“Mun kaɗu ƙwarai da yadda matsalar tsaro ke ƙara ƙamari a Nijeriya, da kuma rashin tabbas da ke biyo bayan kashe-kashen.

“Lokacin yin Allah-wadai ya wuce, yanzu matakin gaggawa ya dace gwamnatocin dukkanin matakai su ɗauka domin kawo karshen masifar nan.

“Mun san cewa tsaron kasa na hannun gwamnatin Tarayya ne, amma mu sani gwamnatin kowanne mataki na da alhakin tsaro da walwalar jama’arta, musamman gwamnonin jihohi.

“Bai dace aikinku ya tsaya a yin tituna da tarukan bukukuwa ba. Gwamnatin gaskiya ita ce wacce ta kafu akan kare rayukan al’umma, tabbatar da doka da oda, da kuma raba su da wahala.” In ji shi.

Daga nan ya yi kira ga gwamnatocin jihohin da su taimaka wa yunƙurin gwamnatin tarayya a ɓangaren tsaro ta hanyar samarwa da tilasta bin dokoki da sauran tsare-tsare a matakin unguwanni.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Binuwai Kwara matsalar tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo

Shugaba Bola Tinubu ya karrama ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya da lambar yabo ta OON.

Shugaban ya bai kowacce ’yar wasa  a tawagar ta Super Falcons kyautar gida mai ɗakuna 3 a rukunin gidaje na Renewed Hope da kuɗi dala dubu 100.

Haka kuma, shugaban ya kuma bai wa masu horas da tawagar kyautar dala dubu 50.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF
  • Gwamnatin Sakkwato Ta Sayo Manyan Tan-tan 250 Na Sama Da Naira Biliyan 22
  • Gwamnatin Kano Ta Kammala Gyaran Makarantu Sama Da 1,200 A Kananan Hukumomi 44
  • Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine
  • Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati
  • ’Yan sa-kai aƙalla 100 da jami’an tsaro 30 sun mutu a bakin aiki a Katsina —Gwamnati
  • Shugaban Kasar Masar Ya Roki Trump Ya Kawo Karshen Yaki A Gaza
  • Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo
  • Kungiyar Gwamnonin Jihohi Ta Jajintawa Jihar Adamawa Bisa Ambaliyar Ruwa A Yola
  • Matsalar Lantarki: Ga tsada ga rashin wuta