2025-11-20@04:06:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 430
«Buɗa baki»:
Ana sa ran za a karrama shahararren ɗan damben boksin na Birtaniya, Fabio Wardley, da kambun zakarun ajin masu nauyi na WBO, bayan Oleksandr Usyk ya janye daga kare kambunsa a fafatawar da zai yi da Wardley. Janyewar ta faru ne bayan Usyk, ɗan kasar Ukraine, ya shaida wa Hukumar Damben Boksin ta Duniya (WBO)...
Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.
Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu...
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta...
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane...
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta bayyana matuƙar damuwa kan harin da aka kai Makarantar Sakandiren Mata da ke Maga a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin sace ɗalibai mata da dama tare da kashe jami’an makarantar. Shugaban ƙungiyar, kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici...
Iyayen ɗalibai ’yan mata 25 ’yan bindiga sace ɗakunan kwanansu a Jihar Kebbi sun bayyana irin tashin hankali da suka shiga bayan abin da ya faru. “Ita kaɗai gare ni,” in ji Malam Muhammad Maga, mahaifin Nafisa, wadda ita kadai ya haifa, kuma take cikin ɗaliban da ’yan bindiga suka sace a makarantar. Malam Muhammad...
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar. A wata sanarwa da ta...
An ɗaura auren Sanatan Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, da Aisha Isah, wata jami’ar soji a Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar sali-alin a Rano. Ɗaurin auren wanda jama’a kaɗan ne suka halarta ya gudana ne da safiyar Litinin ɗin nan a fadar Sarkin Rano da ke...
Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum. Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Nsukka ta ce Gwamnatin Tarayya na lalata makomar ƙasar nan saboda rashin cika yarjejeniyar 2009. A taron manema labarai da ta gudanar a Jami’ar Jihar Benuwe da ke Makurdi, Kodinatan yankin, Kwamared Christian Opata, ya ce gwamnati ba ta jajirce wajen magance matsalolin da suka shafi ɓangaren ilimi....
Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar. Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da...
Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar. Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da...
Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar. Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da...
A wani sabon yunƙuri na inganta haƙƙin yara da walwalarsu, Hukumar kula da kananan yara ta MDD wato UNICEF tare da haɗin gwiwar Hukumar Wayarda kan jama’a da ta Ƙasa (NOA) da Hukumar kidayar Jama’a ta kasa (NPC), da Hukumar Kula da katin zama dan Ƙasa (NIMC), sun kaddamar da shirin wayar da kai na...
Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa. Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko...
Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa. Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa...
Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran...
Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran...
Kungiyar Genoa ta naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Italiya, Daniele De Rossi, a matsayin sabon kociyarta, domin maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar ƙungiyar a ƙarshen mako. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Genoa ta bayyana cewa tana “maraba da Daniele De Rossi” wanda ya jagoranci atisaye na farko da yammacin...
Majalisar Tarayya ta amince da hukuncin cin sarƙa ga duk wani malami da aka samu da laifin cin zarafi ko lalata da ɗalibai a makarantu a faɗin ƙasar nan. Hakan ya biyo bayan amincewar majalisar da Dokar Hana Lalata da Dalibai ta 2025 (HB.1597), bayan tsallake karatu na uku a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Wakilai...
Zohran Mamdani ya lashe zaben Magajin Garin birni mafi girma a Amurka wato New York, kuma zai zama Musulmi na farko a tarihi da ya taɓa shugabantar birnin. Mamdani, mai shekara 34 kuma dan jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya samu nasara bayan ya motsa masu ra’ayin sauyi a cikin birnin da ma fadin ƙasar,...
Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka...
Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka...
Tsohon ɗan takarar Shugaban Najeriya a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce barazanar kawo wa Najeriya hari da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi abin damuwa ne da ke da ɗaga hankalin dukkan ’yan ƙasar. Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra, ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa yammacin wannan Litinin a shafinsa...
Himma Radio, wani gidan rediyon al’umma da ke Jihar Kano, ya sanya yara 40 a makarantar firamare a ƙaramar hukumar Madobi. An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a ranar Lahadi a harabar gidan rediyon da ke Madobi, da nufin rage yawan yara da ke gararamba a titunan jihar ba tare da zuwa makaranta...
“Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi. NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025 Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025 Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa...
“A lokacin, mun yi lissafin adadi a Babban Bankin. Na tashi na kafa sharuda bisa ga ka’idodi, inda na ce a cire tallafin yau. Farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa kashi 13, zan rage shi a cikin shekara guda. Ba za mu samu hauhawar farashin kaya na kusan kashi 30 ba,” in ji...
Babbar Kotun Kano mai lamba 7 da ke zama a cikin birni ta bayar da umarnin tsare Aminu Ismail, mazaunin Unguwar Bai a Karamar Hukumar Ajingi ta jihar, bisa zarginsa da kashe mahaifinsa, Malam Dahiru Ahmad, ta hanyar caka masa wuƙa har lahira. Lamarin ya faru ne bayan samun sabani tsakaninsu kan aniyar Aminu ta...
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta naɗa Luciano Spalletti a matsayin sabon kociya bayan sallamar Igor Tudor da ta yi a farkon makon nan. Juventus ta ƙulla yarjejeniya da tsohon kociyan na Inter Milan da Roma da Udinese da Zenit St Petersburg da kuma tawagar ƙasar Italiya, har zuwa ƙarshen wannan kakar, yayin da take...
Wani haziƙin matashin ɗan wasan Cricket mai shekara 17 ɗan asalin ƙasar Australiya ya mutu a yau Alhamis bayan ƙwallo ta buge shi a lokacin wasa. Ƙwallon ta bugi, Ben Austin a wuyansa ne duk da cewa yana sanye da hular kariyar kai (Helmet) a lokacin da yake ƙoƙarin kare ƙwallon da aka bugo. Za...
Wata babbar kotun Jihar Ekiti da ke zamanta a Ado Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataye wani mai suna Stephen Adamu mai shekara 34 bisa laifin kashe ɗan uwansa. An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban mai shari’a Adekunle Adeleye a ranar 31 ga watan Junairu, 2025, kan tuhumar kashe wani David...
“Muna kira ga hukumar da sauran hukumomi su tabbatar da adalci da daidaito a lokacin ɗaukar ma’aikata na gwamnatin tarayya,” in ji shi. Shugaban Majalisar ya yaba wa Dala bisa kishin ƙasa da ya nuna, sannan ya umarci kwamitin majalisar da ya binciki lamarin tare da gabatar da rahoto domin ɗaukar mataki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
Bugu da kari, an shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka dogaro da kai da karfin ci gaban kimiyya da fasaha, da cimma sabbin nasarori a cikin kara zurfafa gyare-gyare a gida gaba daya, da samun...
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin...
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan kasar. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin...
Aƙalla makiyaya goma aka kashe a wani hari da aka kai wa Fulani makiyaya a wata ruga da ke yankin Tilli a ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar Kebbi. Majiyarmu ta ce harin wanda ya yi kama da na ramuwar gayya na zuwa ne bayan kashe wani ɗan sa-kai a yankin. An rufe makarantu saboda ƙarancin...
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin Masarautar Duguri. Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Aminu Hammayo ne, ya bai wa sabon Sarkin takardar naɗin a madadin gwamnan, a wani biki da aka gudanar a fadar sarkin Duguri, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri, a ranar Juma’a....
Ƙungiyar Arewa Unity Women in Media, ta kai tallafi Makarantar Masu Buƙata ta Musamman da ke Gombe, domin taimaka wa gwamnati wajen kula da rayuwar ɗaliban da ke da buƙata ta musamman. Tallafin ya ƙunshi gidajen sauro, bargo da tabarmi, wanda aka raba wa ɗaliban a lokacin bikin miƙa kayan tallafin. ’Yan sanda sun kama...
Rundunar ’yan sanda ta kama wani matashi ɗan shekara 29, mai suna Abubakar Isah Mokwa ɗalibi da yake karatun digiri na biyu a tsangayar Tattalin Arziki na Noma a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai, Jihar Neja. An kama ɗalibin ne bisa zarginsa da sukar Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago. Rahotanni sun ce an an...
Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma,...
Wannan lamari dai ya janyo ce-ce-ku-ce da fushin jama’a a faɗin jihar, inda al’umma da masu fafutuka ke kira da a bincika tare da ɗaukan mataki cikin gaggawa don hana faruwar irin haka nan gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU October...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Danbare a Jihar Kano, ta gurfanar da wani mutum mai suna Malam Shaddadu bisa zargin sayar da gidan ɗansa ba tare da izini ba. Ɗan mutumin wanda ya gabatar da ƙara, Muhammad Shaddadu, ya shaida wa kotu cewa, lamarin ya samo asalin ne tun bayan da...
Morocco ta ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 a karon farko a tarihin gasar, bayan ta doke Argentina da ci 2 da nema, tawagar da ta fi kowace ƙasa a duniya lashewa a tarihi Wannan gagarumar nasara ya sa ta zama ƙasar Afirka ta biyu da ta ɗaga wannan kofi bayan Ghana, wadda ta yi...
’Yan sandan da aka tura domin daƙile zanga-zangar neman a sako Nnamdi Kanu sun kama ɗan’uwansa da lauyansa, Aloy Ejimakor, inji jagoran zanga-zangar, Omoyele Sowore. A wani saƙo da ya sanya a shafin X, Sowore ya zargi ’yan sanda da kama Kanu’s ɗan uwan Kanu, lauyansa, da wasu masu ’yan ba-ruwanmu ba tare da la’akari ba. “Tawagar...
Hukumar Leƙen Asirin Soji ta Najeriya (DIA) tana gudanar da bincike kan wani tsohon gwamna bisa zargin sa da ɗaukar nauyin sojoji da nufin yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki. Majiyoyin Aminiya sun bayyana cewa akwai zargi mai karfi cewa tsohon gwamnan, wanda ɗan asalin yankin Kudu ne kuma tsohon babban jami’in gwamnati...
Wani ɗan fashi da makami ya kai hari wani gidan biredi da ke cikin garin Kafanchan, a Jihar Kaduna, inda ya harbi ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan sannan ya yi yunƙurin tserewa da kuɗi masu yawa. Manajan gidan burodin, Abdullahi Babiyo, ya bayyana cewa suna cikin aiki lokacin da ɗan fashin, ya shiga gidan da...
An saki ɗan jarida, Ibrahim Ɗan’uwa Rano, bayan da ƴansanda suka tsare shi a shalƙwatar Rundunar Ƴansanda ta Zone 1 Kano bisa zargin batanci ga wani mutum. Sakin nasa ya biyo bayan suka da matsin lamba daga ƙungiyoyin fararen hula irinsu Cibiyar Fasahar Bayanai da Ci Gaban Jama’a (CITAD), da Amnesty International, da sauran ƙungiyoyin...