Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa
Published: 6th, December 2025 GMT
Amurka ta faɗaɗa yawan ƙasashen da ta sanyawa haramcin samun bizar shiga ƙasar zuwa 32 ƙarƙashin jagorancin Donald Trump da ke tsaurara matakan shiga wannan ƙasa ta yammacin duniya saboda abin da ya kira barazanar ƙasashen ga tsaron Washington da kuma kange kwararar ƴan cirani.
Sakatariyar tsaron cikin gida ta Amurka Kristi Noem yayin wasu kalamanta a shirin kai tsaye ta gidan talabijin, ta ce dole ne Amurka ta dakatar da bizar ga duk wata ƙasa da ke turo mata baragurbi waɗanda ke wargaza tsaro da zaman lafiyarta.
Duk da cewa Noem bata bayyana sunayen ƙasashen ba, amma wasu bayanai da suka fita daga ma’aikatar sirrin ƙasar sun ce galibinsu ƙasashe ne na Afrika ciki kuwa har da Kenya da Angola da Masar da Habasha da Ivory Coast sai kuma Najeriya a gaba-gaba.
Wasu majiyoyi sun ce, daga cikin dalilan da ya sanya Amurka saka haramcin visa kan ƙasashen har da yadda wasunsu suka ƙi amincewa da karɓar ƴanciranin da Washington ke tisa ƙeyarsu, sai kuma batutuwa masu alaƙa da rashin isassun takardun shaida daga ƴan ƙasashen kana rashin inganci fasfo.
A cewar Noem yanzu haka ana ci gaba da tantance waɗannan ƙasashe don fitar da jerinsu, matakin da ke zuwa bayan tun a ranar 28 ga watan Nuwamban da ya gabata shugaba Trump ya sanya haramci visa kan mutanen da ke shigowa Amurkan daga ƙasashe matalauta ko masu fama da yaƙi.
Matakin na Amurka na zuwa bayan harin ranar 26 ga watan na jiya, da ya kai ga kisan wani Soja guda, harin da ake zargin wani ɗan ƙasar Afghanistan da kaiwa wanda aka ce ya shiga Amurkan don neman mafaka a shekarar 2021.
Ko a watan Yuni Amurka ta sanya haramcin visa kan ƙasashen Chadi da Congo da Equatorial Guinea da kuma Eritrea baya ga Libya da Somalia da kuma Sudan.
A wani mataki na daban kuma gwamnatin ta Amurka ta buƙaci tsauri kan matafiyan da ke shiga ƙasar daga Burundi da Saliyo da kuma Togo.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka za ta hana ’yan Najeriyar da ake zargi da yi wa Kiristoci kisan kiyashi biza
Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda ya ce Amurka na ɗaukar mataki mai ƙarfi kan munanan ayyuka da tashin hankali da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da sauran sassan duniya.
NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya Na gana da Tinubu kan Kanu ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia“Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka (@StateDept) za ta takaita bizar Amurka ga waɗanda suka san da gaske suna jagoranta, ba da izini, ɗaukar nauyi, goyon baya, ko aiwatar da take hakkin ’yancin yin addini. Wadannan manufofin biza sun shafi Najeriya da sauran gwamnatoci ko mutane da ke zaluntar jama’a saboda addininsu,” in ji Rubio.
Maganganun Rubio sun zo ne kwana guda bayan ’yan majalisar Amurka sun gudanar da taron jin ra’ayi a Washington tare da masana kan ’yancin yin addini da dangantakar ƙasashen waje domin tattauna ƙaruwa da tashin hankali a Najeriya da kuma “zaluncin da aka fi karkata ga Kiristoci.”
Taron majalisar ya kasance wani ɓangare na bincike da ake ci gaba da yi kan batun, bisa umarnin Shugaban Ƙasa Donald Trump.